NOA Ta Gargadi 'Yan Kasuwa, Ta Gano Abubuwa 2 da Za Su Kawo Wahala a Watan Ramadan
- Hukumar NOA ta bayyana cewa boye kayan abinci da kara farashi ba bisa ka'ida ba na iya jefa mutane a wata sabuwar tsadar rayuwa a watan azumi
- Sakamakon haka, NOA ta gargadi yan kasuwa da su gujewa wadannan abubuwa biyu domin kaucewa tashin farashin kayan abinci
- Shugaban NOA na kasa, Lanre Issa-Onilu ya ce ɓoye kaya da gangan na rushe ƙoƙarin da ake yi na daidaita tattalin arziki
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), ta gargaɗi ’yan kasuwa da su guji ɓoye kayan abinci da kuma ƙara farashi ba bisa ƙa’ida ba a lokacin watan Ramadan da kuma azumin Kiristoci na Lent.
Wannan gargadi na kunshe ne a wata sanarwa da Shugaban ahukumar NOA na kasa, Lanre Issa-Onilu, ya fitar a ranar Alhamis, 19 ga watan Fabrairu, 2026.

Source: Getty Images
NOA ta gano makircin yan kasuwa
A rahoton da The Cable ta dauko, ya ce hukumar ta samu rahotanni cewa wasu ’yan kasuwa na ɓoye muhimman kayayyakin abinci da ake yawan amfani da su a lokacin azumi.
Issa-Onilu ya ce a bayanan da suka samu, 'yan kasuwa na boye kayan abincin ne domin su haifar da ƙarancin kaya a kasuwa tare da ƙara farashi.
Ya bayyana wannan dabi’a a matsayin abin da ke kawo tangarda ga tattalin arziki kuma hakan rashin ɗa’a ne musamman a lokacin da ake bukatar tausayi, sadaukarwa da kula da juna.
“Wannan lokaci ne da ake bukatar tausayi, sadaka da jin ƙai ga marasa galihu. Abin takaici ne yadda wasu ke anfani da wannan lokaci na ibada domin neman riba mai yawa a kan talakawa,” in ji shi.
Illar boye kaya ga tattalin arzikin kasa
Shugaban NOA ya ce ɓoye kaya da gangan na rushe ƙoƙarin da ake yi na daidaita tattalin arziki, yana ƙara hauhawar farashi tare da tsananta wahalar da mutane ke fuskanta, cewar Daily Post.
Ya ƙara da cewa gudanar da kasuwanci cikin adalci wajibi ne na ƙasa da kuma na ɗabi’a, yana mai jaddada cewa gaskiya, daidaito da arahar farashi sun dace da ƙimar ƙasa da koyarwar addini.
Issa-Onilu ya buƙaci ƙungiyoyin ’yan kasuwa da na kasuwanni su tabbatar da bin doka da oda a tsakanin mambobinsu, tare da haɗin gwiwa da hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da bin doka.

Source: Twitter
Hukumar NOA ta tashi tsaye
Ya kuma sake jaddada aniyar NOA na ci gaba da shirye-shiryen wayar da kai a jihohi da ƙananan hukumomi domin ƙarfafa ɗabi’a mai kyau, tattalin arziki da haɗin kan ƙasa.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da sa ido kan al’amura tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin kare jin daɗin al’umma da kuma tabbatar da martabar ƙasa.
Wani magidanci, Yahaya Ahmad ya koka kan yadda kayan abinci suka tashi lokaci guda bayan fara azumin watan Ramadan.
Da yake hira da walikin Legit Hausa, Yahaya ya ce irin wannan kari da aka samu ba na Allah da Annabi ba ne, wasu ne kawai suka yi domin kuntatawa al'umma.

Kara karanta wannan
"Ana buƙatar taimako": Shehu Sani ya yi maraba da girke sojojin Amurka a Najeriya
"Wannan tsadar ba daga Allah take ba, domin da yawa daga ciki tsohon kaya ne a hannunsu, amma ganin yadda mutane suke da bukata shiyasa suka kara kudi.
"Muna kira ga gwamnati ta sa ido kan irin wadannan yan kasuwa marasa tausayi, su tausaya mana a wannan wata mai albarka, za su samu lada a wurin Allah," in ji shi.
Hauhawar farashi ya ragu a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar NBS ta tabbatar da raguwar hauhawar farashin kayan abinci da sauran kayayyakin amfani a watan Janairu, 2026.
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa alkaluman hauhawar farashi ya yi ka zuwa kashi 15.10 cikin 100 a watan Janairu da ya gabata.
Manyan sassan da suka fi bada gudummawa ga raguwar hauhawar farashin sun haɗa da abinci da abin sha marasa giya (6.04%), gidajen cin abinci da masauki (1.95%) da sufuri (1.61%).
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

