Gwamna Ya Dauko Fitacciyar Jarumar Fina Finai, Ya ba Ta Shirgegen Mukami

Gwamna Ya Dauko Fitacciyar Jarumar Fina Finai, Ya ba Ta Shirgegen Mukami

  • Gwamna Monday Okpebholo ya nada fitacciyar jarumar Nollywood Mercy Johnson-Okojie a matsayin mai bashi shawara ta musamman
  • Gwamnatin Edo ta bayyana cewa kwarewar Mercy Johnson a fannin huldar jama'a zai taimaka kwarai wajen wayar da kan mutanen jihar
  • Kungiyar jarumai ta AGN ta jinjina wa gwamna Okpebholo bisa karrama masana'antarsu ta hanyar ba mambarta babban mukami

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Edo - Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya ba shahararriyar jarumar fina-finan Nollywood, Mercy Johnson-Okojie, babban matsayi a gwamnatinsa.

Okpebholo ya nada Mercy Johnson a matsayin mai bashi shawara ta musamman kan harkokin hulɗa da jama’a da fafutuka.

Gwamnan Edo ya nada jarumar Nollywood mai taimaka masa ta musamman
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo (hagu) da jarumar Nollywood, Mercy Johnson (dama). Hoto: @m_akpakomiza, @realmercyj
Source: Twitter

Gwamna ya ba jarumar fim mukami

Sakataren gwamnatin jiha, Musa Ikhilor, ne ya sanar da wannan naɗin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a madadin gwamna, in ji rahoton Arise News.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba Aminu Ado Bayero jagorancin ciyar da talakawa a Ramadan

A cewar sanarwar, gwamnan ya amince da naɗin jaruma Mercy ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa yadda jama'a ke fahimtar manufofi da shirye-shiryen gwamnati.

Gwamnati ta bayyana cewa Mercy Johnson fitacciyar jaruma ce, mai shirya fina-finai, kuma ƴar kasuwa wadda ta shafe kusan shekaru 20 tana jan akalar wasan kwaikwayo.

Sanarwar ta ƙara da cewa jarumar ta fito a fina-finai sama da 200 kuma tana da gidauniyar da ke taimaka wa mata, yara, da ɓangaren ilimi da lafiya.

Wasu ayyukan jaruma Mercy a jihar Edo

Musa Ikhilor ya bayyana:

"Baya ga nasarorin da ta samu a harkar nishadi. Mrs. Johnson-Okojie ta kasance mai gudanar da ayyukan jin kai da wayar da kan jama'a.
"A karkashin gidauniyarta ta Mercy Johnson-Okojie, 'yar wasan ta ba mata, kananan yara tallafi ta fuskar jin kai, ilimi da kiwon lafiya."
"Ana sa ran Johnson-Okojie za ta yi amfani da tasirinta da kusancinta da talakawa domin inganta sadarwa tsakanin gwamnati da ƴan ƙasa."
Jarumar dai matar Prince Odianosen Okojie ce, wanda shi ne mamba mai wakiltar mazaɓar Esan ta Arewa maso Gabas da Kudu maso Gabas a Majalisar Wakilai ta Tarayya.

Kara karanta wannan

Jihohin da suka rage lokacin tashi daga ofis alfarmar watan Ramadan a Najeriya

Gwamnatin Edo ta ce jarumar Nollywood Mercy Johnson za ta taimaka wajen wayar da kan jama'a kan ayyukan Gwamna
Jarumar Nollywood, Mercy Johnson da ta samu mukami a gwamnatin Edo. Hoto: @realmercyj
Source: Twitter

Martanin kungiyar AGN kan wannan nadi

Shugaban ƙungiyar jarumai ta ƙasa (AGN), Alhaji Abubakar Yakubu, ya jinjina wa Gwamna Okpebholo bisa wannan mataki na karrama ɓangaren fina-finai na ƙasar nan, in ji rahoton The Nation.

Yakubu ya bayyana cewa wannan naɗin ya nuna yadda tasirin Nollywood yake ƙaruwa a ɓangaren shugabanci da kuma ci gaban ƙasa baki ɗaya a halin yanzu.

"Naɗa ɗaya daga cikin fitattun mambobinmu a matsayin mai ba da shawara abin alfahari ne ga ƙungiyarmu da dukkan fannin ƙirƙira yanzu."

- Abubakar Yakubu.

Gwamna Abba ya sauya mukamin 'yar fim

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Abba Yusuf ya nada Abubakar Matawalle a matsayin sabon shugaban hukumar jin dadin alhazai ta Kano.

Fitacciyar jarumar Kannywood Aina’u Ade ta samu karin girma zuwa babbar mataimakiyar gwamna kan harkokin fina-finai.

Gwamnan ya bukaci dukkan sababbin jami’an da su yi aiki tukuru domin ciyar da jihar Kano gaba da cimma muradun gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com