Fusatattun Mutane Sun Farmaki Ofishin FRSC, An Samu Asarar Rayuka a Babbar Hanya

Fusatattun Mutane Sun Farmaki Ofishin FRSC, An Samu Asarar Rayuka a Babbar Hanya

  • Shugaban hukumar FRSC Shehu Mohammed ya yi Allah-wadai da harin da wasu fusatattun mutane suka kai wa ofishinsu
  • Wani jami'in kiyaye hadurra da direban tirela sun rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota da kuma harin fusatattun mutane
  • Hukumar FRSC ta ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan abin da ya haddasa hatsarin da kuma harin da aka kai ofishinsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Benin - Shugaban FRSC, Shehu Mohammed, ya yi Allah wadai da harin da fusatattun mutane suka kai wa jami'an hukumar da kuma kayan aikinsu bayan wani hatsari a Benin.

Ya tabbatar da cewa dukkan waɗanda aka samu da laifi za su fuskanci fushin doka kamar yadda tsarin shari'ar ƙasarmu ta tanadar.

Hukumar FRSC ta yi magana da wasu fusattu suka farmaki ofishinta da ke Benin.
Jami'an hukumar FRSC a bakin aiki. Hoto: @FRSCNigeria
Source: Twitter

Shugaban ya fitar da wannan gargaɗin ne a cikin wata sanarwa da jami'in yaɗa labaran hukumar, Olusegun Ogungbemide, ya fitar a ranar Juma'a, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Katuwar bishiya ta kifo kan fasinjoji a mota, ta danne su sun mutu

Haɗarin mota da kisan jami'in FRSC

Rahoto ya nuna cewa wani direban tirela ya riga mu gidan gaskiya sakamakon haɗarin motoci biyu a babban hanyar Benin zuwa Legas.

Jami'an hukumar FRSC sun sami munanan raunuka yayin ƙoƙarin ceto mutane, inda ɗaya daga cikin jami'an ya rasu daga baya sakamakon raunukan da ya ji.

Bayan faruwar hatsarin, wasu fusatattun mutane sun mamaye ofishin hukumar da ke kusa da babbar mashigar Benin (Toll Gate) inda suka lalata kayayyaki.

Sai dai saurin shiga tsakani da jami'an tsaro suka yi ya taimaka kwarai wajen dawo da doka da oda da kuma hana ƙara lalata abubuwa.

Shehu Mohammed ya ce:

"Bayan afkuwar hatsarin, wasu fusatattun mutane sun farmaki tare da lalata ofishinmu, amma jami'an tsaro sun taimaka wajen dawo da zaman lafiya."

Jami'an tsaro sun kai wa FRSC dauki

Shugaban hukumar ya bayyana faruwar lamarin a matsayin abin takaici wanda ba za a lamunta ba, inda ya ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Jami'an DSS sun cafke El Rufai a harabar ofishin EFCC

Ya gode wa rundunar sojin ƙasa da na ƴan sanda saboda yadda suka kawo dauki cikin gaggawa domin dakile harin da aka kai wa jami'ansa, in ji rahoton The Nation.

Yayin da yake yin Allah wadai da harin, shugaban ya nanata cewa jami'ansa suna gudanar da aikinsu ne na ceton rayuka lokacin da wannan mummunan hatsari ya faru.

Ya jajantawa iyalan direban da kuma jami'in da ya rasu, sannan ya ba da umarnin bincikar dalilan da suka sa mutane suka fusata haka har suka kai harin.

Shugaban hukumar FRSC ya ce za a gudanar da cikakken bincike kan harin da aka kai wa jami'ansa
Shugaban hukumar FRSC, S. Mohammed (hagu) ya jagoranci rangadi a lokacin bukukuwan karshen shekara. Hoto: @FRSCNigeria
Source: Twitter

FRSC ta yi kira ga 'yan Najeriya

Shehu Mohammed ya nemi hadin kan jama'a wajen mara wa hukumar baya domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata ba tare da fuskantar barazana ko hari ba.

A ƙarshe, ya buƙaci mutane da su kasance masu bin doka da oda, inda ya ce tashin hankali ba zai taɓa zama mafita ga matsalolinmu ba.

Rundunar FRSC za ta ci gaba da sanya ido a kan hanyoyinmu domin tabbatar da cewa ana bin ƙa'idodin tuki domin kiyaye rayukan dukkan jama'a.

An karrama wasu jami'an FRSC

A wani labari, mun ruwaito cewa, jami’an hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) huɗu sun samu takardun yabo bisa halin kirki da gaskiya da suka nuna.

Kara karanta wannan

Ramadan 2026: Tsofaffi da wasu mutane 7 da shari'a ta ba su damar shan azumi

Hukumar FRSC ta ba jami'an nata lambar yabo ne bisa dawo da Naira miliyan 870 waɗanda suka samu a wajen wani hatsarin mota da ya auku.

Wasu ƴan Najeriya sun ce kamata ya yi hukumar ta FRSC ta yi wa jami’an ƙarin girma a maimakon ba su takardun yabo kawai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com