Fusatattun 'yan achaba sun kone ofishin hukumar FRSC

Fusatattun 'yan achaba sun kone ofishin hukumar FRSC

Masu babur din haya a ranar Juma'a sun bankawa ofishin jami'an kiyaye hadurra kan titi (FRSC) wuta a garin Bida na jihar Neja. Hakan ya biyo bayan zargin hukumar da suka yi da alhakin halaka dan uwansu.

Sun zargesu da zama musabbabin mutuwar abokin aikinsu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

An gano cewa dan achaban wanda ya mutu, ya bi hannun da ba nashi bane sakamakon kokarin kama shi da jami'an suka yi. Hakan yasa jami'an suka bude kofa daya ta motarsu don kare shi daga gudun da yayi niyya. Amma hakan bai samu ba don sai ya buga kanshi wanda hakan yayi sanadiyyar fashewar kanshi.

Babu kakkautawa aka mika shi asibiti amma sai yace ga garinku daga bisani.

Amma kuma, jami'in hulda da jama'a na hukunar, Olugbemiga Bello ya kwatanta lamarin da abin bakin ciki amma ya musanta hannun jami'ansu a mutuwar.

Hakazalika, shugaban kungiyar 'yan achaba na yankin, Umar Amah, ya musanta hannun 'yan achaban a kone ofishin hukumar FRSC.

Fusatattun 'yan achaba sun kone ofishin hukumar FRSC

Fusatattun 'yan achaba sun kone ofishin hukumar FRSC
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Mijina ya sakeni saboda kawai na tambaye shi ya bani izinin kwanciya da abokinsa

A wani labari na daban, wata mata 'yar Najeriya mai suna Linda ta fada cikin tashin hankali bayan ta bukaci kwanciya da abokin mijinta don samun juna biyu. Linda tayi hakan ne kuwa don ta samu rabo bayan aurenta na shekaru takwas ya kasa samar da haihuwa.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, lamarin ya faru ne a Agodo Egbe da ke yankin Ikotun ta jihar Leagsa inda suke zama. Wannan bukatar kuwa ta jefa Linda cikin mummunan tashin hankalin da ya kai ga mutuwar aurenta, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

Kamar yadda Linda ta bayyana: "A halin yanzu ina zaune da 'yan uwana ne a Ikorodu ta jihar Legas. Ina ta aikawa mijina ban hakuri da neman yafiya a kan bukatar da na mika gabansa.

"Mijina Okey dan kasuwa ne babba don har kasashen duniya yake fita, yana shigo da kaya kala-kala. Yana da kadarori masu yawa a Legas da kuma Kudu maso gabas din Najeriya. Babban kalubalensa kuwa shine rashin haihuwa.

"Mun yi aure ne shekaru takwas da suka gabata amma har yanzu babu haihuwa. Mun je asibiti sannan fastoci da dama sunyi mana addu'ar samun rabo."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel