Gwamnati Ta Gyara Halin Tubabbun 'Yan Ta'adda sama da 100, Za Su Dawo cikin Mutane

Gwamnati Ta Gyara Halin Tubabbun 'Yan Ta'adda sama da 100, Za Su Dawo cikin Mutane

  • Tubabbun 'yan ta'adda 117 da suka zubar da makamai suka rungumi zaman lafiya sun kammala shirin sauya hali na gwamnati
  • An fadada shirin zuwa yankin Arewa maso Yamma, bayan kyankyashe mutanen da suka zubar da makamansu a Borno
  • Yanzu haka ana shirin bude sababbin sansanoni a shiyyar, yayin da Binuwai ta nemi a bude sansanin a yankin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Akalla mutane 117 da aka bayyana a matsayin ‘yan ta’adda da suka yi nadama daga jihar Borno sun kammala shirin gyaran hali da gwamnati ke yi.

An yaye su ne a lokacin da gwamnati ke ci gaba da fadada wannan tsari na sauya tunanin tubabbun 'yan ta'addan zuwa yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

An kammala gyara tunanin tubabbun yan ta'adda 117
Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum yayin jawabi a wani taro Hoto: The Borno State Governor
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa hakan na zuwa ne a lokacin da gwamnatin jihar Binuwai ta bukaci a kafa sansanin DRR a yankin Arewa ta Tsakiya domin taimaka wa kokarin dawo da zaman lafiya.

An yaye tubabbun 'yan ta'adda daga shirin gwamnati

Jaridar Punch ta wallafa cewa daraktan yada labaran tsaro, Manjo Janar Samaila Uba ne ya tabbatar da kammala shirin a wani taron masu ruwa da tsaki.

Hedikwatar tsaro ce ta shirya taron a wani bangare na kammala shirye-shiryen mika wadanda aka gyara wa tunani ga hukumomin kasa da jihohi don su mayar da su cikin mutane,

Tubabbun yan ta'addan da aka yaye sun fito daga Borno
Taswirar jihar Borno da ke fama da matsalar rashin tsaro Hoto: Borno map
Source: Original

Mai kula da shirin 'operation safe corridor', Birgediya Janar Y. Ali, ya ce mutane 117 da aka yaye sun kammala dukkannn matakan gyara tunani a sansanin Mallam Sidi da ke jihar Borno.

Ya bayyana wannan cigaba a matsayin shaida ta kyakkyawar hadin kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi wajen karbar wadanda suka tuba, sa ido a kansu.

Kara karanta wannan

Katuwar bishiya ta kifo kan fasinjoji a mota, ta danne su sun mutu

Sanarwar ta ce:

“Mutane 117 daga jihar Borno sun samu nasarar kammala shirin a sansanin Mallam Sidi, lamarin da ke nuna karfafa hadin gwiwa tsakanin tarayya da jihohi wajen tarba, kulawa da sake shigar da su cikin al’umma.”

An fadada gyara halin tubabbun 'yan ta'adda

Birgediya Janar Ali ya kuma bayyana cewa an fadada shirin zuwa yankin Arewa maso Yamma, inda aka kafa wani sansanin shirin a watan Fabrairun 2025.

Ya bayyana kokarin da ake yi na fadada shirin a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da zaman lafiya.

Ya ce ana tattaunawa da gwamnatin jihar Zamfara domin inganta tsarin samar sansanin ta yadda zai hada da kula da lafiyar kwakwalwa da sulhu tsakanin al’umma.

Haka kuma za a yi kokarin tabbatar da an bayar da tallafin sana’o’i da kuma gindaya tsauraran matakan sa ido a kansu.

A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, Birgediya Janar Ali ya ce gwamnatin jihar Binuwai ta gabatar da bukatar kafa sansanin gyara halin a jiharta.

Kara karanta wannan

An yi zanga zangar korar 'yan Arewa a Rivers, an fasa shaguna da lalata dukiya

Ya kara da cewa Hedikwatar tsaro ta duba wuraren da aka gabatar, tare da ba da shawarar su dace da ka’idojin kasa na tsaro, gine-gine da dorewa kafin amincewa.

'Yan ta'adda sun kai hari Kebbi

A wani labarin, mun wallafa cewa mayakan kungiyar ‘yan ta’addan Lakurawa sun kai munanan hare-hare a wasu kauyukan jihar Kebbi, inda suka kashe mutane da dama.

Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan sun kai harin ne a ranar Laraba da 1:15 na rana a kauyukan da ke karkashin gundumar Bui a yankin Arewacin jihar Kebbi.

Rahotanni sun bayyana cewa rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, 19 ga watan Fabrairun 2026, inda aka lalata dukiyoyi da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng