An ‘Bankado’ Alakar Epstein, Tsohon Firayin Ministan Isra’ila da Boko Haram

An ‘Bankado’ Alakar Epstein, Tsohon Firayin Ministan Isra’ila da Boko Haram

  • Wani sabon bincike ya danganta marigayi Jeffrey Epstein da tsohon Firaministan Isra’ila, Ehud Barak da Boko Haram
  • Rahoton ya ce an yi amfani da tattaunawar tashoshin jiragen ruwa a Lagos da Badagry, da kuma fasahar tsaro, domin samun moriyar kasuwanci
  • Binciken ya yi zargin cewa hanyoyin tsaro da jarin da aka zuba sun bai wa bangarorin damar cin gajiyar rashin zaman lafiyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

U.S - Wani sabon rahoto ya yi zargin alakar marigayi attajirin Amurka, Jeffrey Epstein, da tsohon Firaministan Isra’ila, Ehud Barak da ta'addanci.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa ana zargin sun yi amfani da rikicin Boko Haram a Najeriya domin samun riba da muradun dabarun siyasa.

Zargin alakar Epstein da Boko Haram ta sake tayar da jijiyoyin wuya
Marigayi attajirin dan kasuwa a Amurka, Jeffrey Epstein. Hoto: T@nicksortor.
Source: Twitter

An sake bankado bayanai game da Jeffrey Epstein

Rahoton The Sun ya ce wasu sakonnin imel da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta fitar a 2018 sun nuna Epstein na saukaka tattaunawa tsakanin Jide Zeitlin, shugaban Asusun Zuba Jari na Najeriya a wancan lokaci, da Sultan Ahmed bin Sulayem, tsohon shugaban DP World na Hadaddiyar Daular Larabawa.

Kara karanta wannan

DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

An ce tattaunawar ta mayar da hankali kan neman cikakken iko da tashoshin jiragen ruwa a Lagos da Badagry, bayan tattaunawa da shugabannin Najeriya tun 2005 ba ta haifar da sakamako ba.

Rahoton ya bayyana cewa DP World ba ta son zuba jari a wani yankin masana’antu a Najeriya ba tare da cikakken iko da tashar jirgin ruwan da ke makwabtaka da shi ba.

Masu binciken sun kuma bayyana cewa kusan Epstein na tattauna wa da Barak, wanda ake zargin ya nemi kara karfafa hadin gwiwar tsaro tsakanin Isra’ila da Najeriya bayan barin mukaminsa.

Bayan sauka daga mukamin Ministan Tsaro a 2013, an ce Barak ya yi anfani da alakar tsaro a Najeriya wajen bude kofar zuba jari a harkokin makamashi da kasuwanci masu alaka da Isra’ila.

Bincike ya danganta Epstein da cin gajiyar rikicin Boko Haram
'Dan kasuwa a Amurka da ya mutu a gidan yari, Jeffrey Epstein. Hoto:@gaming_leaker.
Source: UGC

Yadda aka tallata wa Najeriya dabarun yaki da ta'addanci

A 2015, Barak da abokinsa sun zuba dala miliyan 15 a kamfanin FST Biometrics, wanda tsohon shugaban leken asirin Isra’ila, Aharon Ze’evi Farkash, ya kafa.

Tsarin na’urar tantance halittu na Basel, wanda aka fara amfani da shi a kan iyakar Isra’ila da Gaza, an tallata shi a Najeriya a matsayin mafita kan ta’addanci, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Duniya labari: Sanata a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya, ana ta rasa 'yan majalisa

An ce an gabatar da fasahar ga Jami’ar Babcock a matsayin kariya daga hare-haren Boko Haram, tare da kuma tallata ta ga gwamnatocin Afirka domin sarrafa bayanan jama’a.

Rahoton ya kuma ambaci wata hadin gwiwa ta 2020 da Bankin Duniya ya tallafa, wacce ta hada Hukumar Tsaro ta Yanar Gizo ta Isra’ila da kamfanin Toka Group, wanda Barak ya kafa tare da wasu, domin tallafa wa tsarin tsaron yanar gizon Najeriya.

A karshe, binciken ya ce wannan jerin tsare-tsaren tsaro da dabarun zuba jari sun bai wa Epstein da Barak damar cin gajiyar rashin zaman lafiyar da rikicin Boko Haram ya haifar, tare da bunkasa muradun kamfanonin Isra’ila a Najeriya.

Yadda Epstein ya so kasuwancin mai a Najeriya

An ji cewa sababbin takardun hukumar FBI sun nuna Jeffrey Epstein ya taba shirin cinikayyar danyen mai da Najeriya.

Sakon Imel ya bayyana yadda aka yi masa alkawarin ribar dala miliyan shida daga sayar da man Najeriya zuwa China.

Takardun sun kuma fallasa hulɗar Epstein da manyan mutane a duniya, ciki har da shugabannin siyasa, da manya a cikin gwamnatin Amurka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.