Sheikh Bashir Aliyu Ya Yi wa Tinubu Raddi kan Rokon 'Yan Najeriya Su Yafe Masa
- Malamin Musuluncin nan, Dr Bashir Aliyu Umar ya yi wa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu martani game da rokon da ya yi a yafe masa
- Malamin ya bayyana cewa babban abin da ya kamata Shugaban kasa ya mayar da hankali a kansa shi ne sauke nauyin da ke kansa
- A wajen bude tafsirin Ramadan 2026 a fadar shugaban kasa ne Bola Ahmed Tinubu ya roki 'yan Najeriya su yafe masa idan ya masu laifi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Sheikh Bashir Aliyu Umar ya yi martani game da kalaman Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da yake rokon a yafe masa.
Malamin Musuluncin ya yi tsokaci kan yadda shugabanni ke rokon jama'a su taya su da addu'a wajen samun damar aiki yadda ya kamata.

Kara karanta wannan
An ji abin da ya roka da Tinubu ya yi waya da Shugaban gwamnatin kasar Jamus a tarho

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Sheikh Bashir Aliyu Umar ya yi ne a wani sako da shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ya wallafa a Facebook.
Kiran Sheikh Bashir Aliyu ga Bola Tinubu
A matanin da Sheikh Bashir Aliyu Umar ya yi, ya bayyana cewa a halin yanzu, kamata ya yi shugaban kasa ya mayar da hankali wajen sauke nauyin da ya ke kansa.
Malamin ya ce:
"An ce shugaban kasa ya ce 'yan Najeriya su yafe masa. Ai ba zancen a yafe mar ba, zancen ka ba mai hakki hakkinsa. Ofis da Allah ya baka, da Allah ya ce ka yi rahama, ka yi rahama."
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa shugaba Bola Tinubu ya roki 'yan Najeriya su yafe masa ne yayin tafsirin Ramadan da aka kaddamar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Source: Facebook
Maganar yi wa shugabanni addu'a
Sheikh Bashir Aliyu Umar ya yi tsokaci kan kiran da ake yi na cewa a rika yi wa shugabanni addu'a domin samun nasara wajen tafiyar da mulki.
Ya bayyana cewa Annabi SAW ya riga ya gama yi wa shugabanni addu'a, ya ce aikin malamai kawai dauraya ne a kan abin da ya riga ya gabata.
Sheikh Bashir Aliyu Umar ya yi ishara da Hadisin da Annabi SAW da ya yi nuni da cewa:
"Dun wanda ya jibanci al'amarin al'umma ta ya tausasa musu, ka tausasa masa. wanda duk ya jibanci al'amarin al'umma ta ya tsananta, ka tsananta masa."
Malamin ya kara da cewa addu'ar da ke cikin hadisin ta shafi kowa da kowa, mutum a cikin gidansa da sauransu ba shugabanni kawai ba.
An yi gargagi kan tazarcen Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon hadimi a fadar shugaban kasa, Hakeem Baba Ahmed ya yi hasashen cewa babu alamar za a samu sauki idan shugaba Bola Tinubu ya zarce.
Dr Hakeem Baba Ahmed wanda ya yi aiki da Kashim Shettima ya ce idan shugaban kasar ya zarce lamura za su iya lalacewar da ba a taba gani ba a tarihin Najeriya.
Ya ce tun bayan murabus da ya yi a shekarar 2025, babu wani sauyi da ya gani sai karuwar matsalolin tsaro, musamman a wasu yankunan Arewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
