Sabuwar Dokar Tinubu Ta Zo da Alheri, Kasafin Gwamnatoci zai Karu da Tiriliyoyin Naira

Sabuwar Dokar Tinubu Ta Zo da Alheri, Kasafin Gwamnatoci zai Karu da Tiriliyoyin Naira

  • Ana sa ran cewa sabon umarnin Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai kara wa asusun rarraba kudi na kasa karfi
  • Shugaban ya sanya hannu a kan wata doka da ta tilasta wa kamfanin mai na kasa da wasu hukumomin mai mika kudi kai tsaye ga gwamnati
  • Ana ganin wannan zai habaka kudin da ake raba wa tsakanin gwamnatin tarayaa da jihohin kasar da kusan N14.57tn

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi na iya samun karin kaso daga asusun tarayya bayan sabuwar doka da Shugaba Bola Tinubu ya sanyawa hannu.

Za a samu karin da kusan Naira tiriliyan 14.57 bayan sabon umarnin zartarwa da Shugaba Bola Tinubu ya rattaba wa hannu.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta sake sake tashi rigi rigi a wata babbar kasuwa a Kano

Shugaban kasa Bola Tinubu ya sa hannu a kan sabuwa doka
Shugaba Bola Ahmed tare da shugabanni da wasu jagororin majalisa yayin rattaba hannu a kan wata doka Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta wallaa cewa a sabuwar dokar da Tinubu ya sanya wa hannu, ta yi tanadin cewa dole ne a mayar da dukkanin riba da harajin mai fetur kai tsaye ga asusun gwamnatin tarayya.

Kudin gwamnatocin Najeriya zai karu

Hasashen ya nuna cewa kamfanin mai na kasa zai ta rasa kusan Naira biliyan 906.91 daga kudin gudanarwarsa da kuma asusun binciken sababbin yankuna masu albarkatun mai.

Punch ta wallafa cewa bincike kan kudin shiga na shekarar 2025 da aka mika wa kwamitin rarraba kudin tarayya (FAAC) ya nuna cewa wannan sauyi zai shafi manyan hanyoyin kudin shiga a bangaren mai da gas.

Haka kuma, kudin shiga na 'royalty' na mai da gas da suka kai N7.55tn, da tarar kone iskar gas ta N611.42bn da hukumar NUPRC ke tara wa, su ma za su wuce kai tsaye cikin asusun gwamnatn tarayya.

Sabon umarnin Tinubu zai shafi bangaren man fetur da kudin shigarsu
Shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari Hoto: NNPC Limited
Source: UGC

Hukumar tattara kudin haraji ta kasa ma za ta daina karbar haraji a kan man fetur, wadanda suka samar na N4.905tn a 2025.

Kara karanta wannan

Ramadan: Dakarun Hisbah sun cafke gandaye da rana gotai gotai a Kano

An kuma soke 30% na kudin binciken wurare masu albarkatun man fetur, tare da dakatar da 30% na kudin kula da NNPC ke rikewa daga ribar da aka samo.

Umarnin ya fara aiki daga 13 ga Fabrairu, 2026, bisa tanadin Sashe na 5 da kuma Sashe na 44(3) na kundin tsarin mulki.

Yadda sabuwar doka za ta shafi bangaren mai

Tun bayan fara aiwatar da PIA a 2021, asusun tarayya na karbar 40% ne kacal daga kwangilolin da aka bayar, yayin da NNPC ke rike da 60%.

Yanzu kamfanin ba zai sake sarrafa wannan kaso ba, sai dai a tura shi kai tsaye zuwa cikin asusun gwamnatin tarayya.

Shi kuma asusun 'Frontier' an kirkiro shi ne domin binciken mai a yankunan da ba a saba hakowa ba kamar Tafkin Chadi, Sokoto, Bida, Benue da Dahomey.

Ana amfani da shi wajen binciken kasa, hakar gwaji da nazarin bayanai domin samun bayanan man da ake zaton akwai wa wuraren.

Bincike ya nuna cewa N906.91bn da NNPC za ta rasa ya kasu gida biyu: N453.455bn na kudin gwajin wurare masu albarkatun mai da kuma N453.455bn na kudin gudanarwa.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Shugaba Tinubu ya fadi dalilin sanya hannu a dokar zabe duk da korafe korafe

Ana sa ran tasirin wannan sauyi zai bayyana a taron FAAC na mako mai zuwa, yayin da gwamnati ke jaddada manufar 'Najeriya a kan gaba' wajen kare kudin kasa.

Tinubu ya sa hannu kan dokar zabe

A baya, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya kare matakinsa na sanya wa dokar gyaran zaɓe ta shekarar 2026 hannu, duk da korafin da aka rika yi kan tura sakamako kai tsaye.

Ya bayyana cewa gudanar da sahihin zabe ya fi komai muhimmanci, ko da kokarin aika sakamakon kai tsaye ne kamar yadda yan adawa ke fafutukar a rika yi.

Tinubu ya yi wannan jawabi ne jim kaɗan bayan rattaba hannu kan dokar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng