‘Sai Kun Biya N100m’: ’Yan Bindiga Sun Rubuta Wasika, Za Su Yi Wa’azi a Ramadan
- ’Yan ta’adda sun aika wa al’ummar Utono a Kebbi wasika, suna neman N100m kafin su shiga gari don “wa’azi”
- Sun yi barazanar kai hari idan ba a biya kudin ba, tare da ambaton harin da ya kashe mutane a Woru, Jihar Kwara
- Gwamnatin Kebbi ta tabbatar da wasikar, ta tura jami’an tsaro da sa ido ta jiragen sama domin dakile duk wata barazana
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Utono, Kebbi - Fargaba ta mamaye al’ummar Utono da ke karamar hukumar Ngaski a Jihar Kebbi, bayan barazanar yan ta'adda.
Wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne sun aike da wasika suna neman Naira miliyan 100 kafin su shiga garin domin “wa’azi”.

Source: Facebook
Barazanar da 'yan bindiga suka yi a Kebbi
Rahoton Punch ya ce lamarin ya kara dagula tsaro a wasu sassan Kebbi da jihohin makwabta, inda kungiyoyin masu dauke da makamai ke kai hare-hare, satar mutane da kuma karbar kudin fansa a yankunan karkara.
A cikin wasikar da aka ce an mikawa shugabannin al’umma da safiyar Alhamis, 19 ga watan Fabrairun 2026 maharan sun gargadi mazauna garin da kada su dauki sakon da wasa.
Wasikar ta ce:
“Wannan ba wasa ba ne. Za mu zo wa’azi. Dole ku biya mu Naira miliyan 100.
“Idan ku ka ki, za ku fuskanci hari, kuma babu wanda za ku zarga sai kanku. Ko da kun kira sojoji, ba za su iya hana mu ba.”
Sun kuma yi ishara da harin da aka kai a al’ummar Woru da ke karamar hukumar Kiama a Jihar Kwara, inda aka ruwaito cewa an kashe mutane bayan an yi watsi da irin wannan gargadi.
Wata majiya daga cikin al’ummar, wacce ta nemi a sakaya sunanta saboda dalilan tsaro, ta ce wasikar ta jefa jama’a cikin tsananin firgici.
Majiyar ta ce:
“Mutane sun firgita. Ambaton abin da ya faru a Woro ya kara tsoratar da jama’a. Iyalan da dama sun fara shirye-shiryen kariya idan wani abu ya taso.”

Source: Original
Gwamnatin Kebbi ta tabbatar da samun wasikar
Da yake tabbatar da sahihancin wasikar, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kebbi, Alhaji Ahmed Idris, ya shaida cewa gwamnati ta dauki matakan gaggawa domin dakile duk wani hari.
Idris ya kara da cewa gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ba ta dauki barazanar da wasa ba.
Ya ce:
“Na yi magana da Daraktan Tsaro; ya tabbatar da labarin, kuma an tura jami’an tsaro zuwa yankin, gwamnati tare da hukumomin tsaro sun jibge jami’ai a yankin, har da sa ido ta sama.
“Kun san gwamnatin jiha ba ta wasa da tsaron al’umma. Mai girma gwamna ya dade yana daukar matakai kan tsaro, kuma wannan ba zai zama na daban ba.”
Hukumomi sun ce ana ci gaba da kara zage damtse a fannin tsaro domin hana sake faruwar hare-hare da kuma kwantar da hankalin al’umma.
'Yan ta'adda sun hallaka Musulmi a Kebbi
Mun ba ku labarin cewa an shiga jimami a jihar Kebbi bayan da 'yan ta'addan kungiyar Lakurawa suka kai wani harin ta'addanci a wasu kauyuka.
Tsagerun 'yan ta'addan sun hallaka mutane sama da 30 bayan sun kai hare-hare a kauyukan da ke yankin Arewacin jihar.
Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta hannun mai magana da yawun bakinta, ta yi karin bayani kan munanan hare-haren na 'yan ta'addan Lakurawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

