'Yan Sanda Sun Cafke Tsohon Hadimin Buhari yayin da El Rufa'i ke Tsare

'Yan Sanda Sun Cafke Tsohon Hadimin Buhari yayin da El Rufa'i ke Tsare

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Cross River ta cafke tsohon hadimin marigayi shugaba Muhammadu Buhari kan wasu zage-zarge
  • Rahotanni sun nuna cewa zarge-zargen na da alaka da kungiyar lauyoyi, inda ta yi takaitaccen bayani game da abin da ya faru
  • Okoi Obono-Obla ya yi aiki a karkashin Muhammadu Buhari kafin daga baya ya sallame shi saboda wasu abubuwa da suka taso

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Cross River - Rundunar ’yan sandan Cross River ta tabbatar da kama tsohon hadimin shugaba Muhammadu Buhari, Okoi Obono-Obla a karamar hukumar Yakurr da ke jihar.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Eitiokpa Sunday Akata, ya sanya wa hannu, an ce an kama shi ne bisa tanade-tanaden doka.

Eitiokpa Sunday Akata da Okoi Obono-Obla
Okoi Obono-Obla a hagu, kakakin 'yan sanda, Eitiokpa Sunday Akata a dama. Hoto: @ObonoOblaSenate|@BenHundeyin
Source: Twitter

Dalilin kama tsohon hadimin Muhammadu Buhari

Kara karanta wannan

DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

Daily Trust ta wallafa cewa Akata ya ce an kai Okoi Obono-Obla sashen binciken laifuffuka na jiha (SCID) da ke Calabar, inda ake ci gaba da bincike kan zarge-zargen aikata laifi.

Ya ce:

“An kama Obono-Obla bisa doka a ranar 19 ga Fabrairu, 2026, da misalin ƙarfe 12:00 na rana a kusa da Abuja Park, Ugep, sakamakon wani ƙorafi da aka miƙa wa kwamishinan ’yan sanda,
"Korafin na zarginsa da laifuffuka da suka shafi ƙirƙirar takardun bogi da kuma shiga harkar lauya ta hanyar yaudara.

Dangane da inda ya ke a yanzu, 'yan sanda sun ce:

“An sanar da lauyansa. Iyalansa ma sun san inda yake a halin yanzu.”

Rundunar ta musanta zarge-zargen cewa an sace shi ko kuma wasu jami’an tsaro da ba a san su ba ne suka kama shi, tana mai cewa wannan labari ƙarya ne mara tushe.

Shugaban 'yan sandan Najeriya
Sufeton 'yan sandan Najeriya a ofishinsa. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Bayanin kungiyar lauyoyi

A nasa ɓangaren, shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Calabar, Enome J. Amatey, Esq., ya ce har yanzu ƙungiyar ba ta samu cikakken bayani a hukumance kan wace hukuma ce ta kama shi ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fusata da rigimar APC ta lakume rayukan mutane 2, ya ba da umarni

Ya ce:

“Mun ji labarin kama shi. Ba mu san wace hukuma ce ta kama shi ba. Yanayin lamarin bai fito fili ba.
“Muna fatan za a mutunta haƙƙinsa, a ba shi damar kare kansa yadda ya kamata tare da samun wakilcin lauya.”

Ya jaddada cewa ƙungiyar za ta tabbatar an bi doka yadda ya kamata, kuma ba za a tsare Obono-Obla fiye da wa’adin da kundin tsarin mulki ya tanada ba tare da hujjar doka ba.

This Day ta wallafa cewa a 2016 Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Okoi Obono-Obla a matsayin hadimi na musamman ga shugaban kasa a ma'akatar shari'a kafin ya sallame shi a 2019.

Hukumar ICPC ta tsare Nasir El-Rufa'i

A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta tabbatar da kama tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

An kama tsohon gwamnan ne jim kadan bayan hukumar EFCC ta ba shi beli bayan bincike da ta masa, inda ya shafe kwana biyu a hannunta.

Tun El-Rufa'i yana kasar Masar ya ke cewa ana shirin kama shi a Najeriya, kuma yana sauka filin jirgin sama aka yi yunkurin cafke shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng