ICPC ta sake gayyatar tsohon hadimin Buhari, Obono-Obla, bisa takardun makaranta na bogi

ICPC ta sake gayyatar tsohon hadimin Buhari, Obono-Obla, bisa takardun makaranta na bogi

  • Hukumar bincike akan rashawa da sauran laifuka mai zaman kanta ta ICPC, ta kara karar tsohon hadimin Buhari, Okoi Obono-Obla
  • Hakan ya faru ne a ranar Litinin bisa zargin sa da amfani da takardun makaranta na bogi, a babbar kotun jihar Filato
  • Ana zargin sa da amfani da sakamakon jarbawar bogi wurin neman gurbin karatu akan shari’a a jami’ar jihar Jos (UNIJOS)

Filato - Hukumar bincike akan rashawa da sauran laifuka mai zaman kan ta, ICPC, ta gayyaci tsohon hadimin shugaban kasa, Okoi Obono-Obla, bisa laifin amfani da takardun makaranta na bogi.

Hukumar ta maka karar Obono-Obla a ranar Litinin, a babbar kotun jihar Filato da ke Jos kamar yadda NewsWireNGR ta ruwaito.

Read also

An dakatar shugaban wata makarantar Larabci da aka ci zarafin wata daliba

ICPC ta sake gayyatar tsohon hadimin Buhari, Obono-Obla, bisa takardun makaranta na bogi
Obono-Obla. Hoto: NewsWireNGR
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An zarge shi da amfani da takardun makaranta na bogi don neman gurbin karatu a fannin shari’a a jami’ar jihar Jos (UNIJOS).

Takardar bogi da ya yi amfani da ita tana daya daga cikin laifuka 10 da ake zargin sa dasu ciki har da zargin sa da rashawa, dama tun ranar 1 ga watan Yulin 2020 ICPC ta maka shi babbar kotun Abuja.

Saidai daga baya hukumar ta janye karar bisa ruwayar NewsWireNGR.

Har ila yau hukumar ta kara maka shi a kotu

A ranar 8 ga watan Yulin 2020 hukumar ta kara maka shi a babbar kotun FCT, tare da Mr Obono-Obla, tsohon hadimin shugaban kasa na musamman har da Aliyu Ibrahim da darektan ABR Global Petroleum Resources Ltd, Daniel Omughele Efe.

Sannan a ranar 4 ga watan Maris din 2021, hukumar ta kara sabunta karar, yayin da ta cire korafin amfani da takardar bogi da sauran korafi 3 na zargin sa da rashawa.

Read also

2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya koma APC a hukumance, ya gana da shugaban jam'iyyar a Abuja

Ranar 17 ga watan Maris, Obono-Obla ya bayyana gaban kotu saboda laifuka 5, wadanda duk ya musanta aikatawa.

A ranar Litinin, Obono-Obla ya kara musanta aikata duk laifukan.

Daga baya kotu ta bayar da belin sa da N1,000,000 tare da gabatar da wani tsayayye.

Abin da yasa Legas ta zama matattaran mashaya, muggan ƙwayoyi, Kakakin Majalisa Obasa

A wani labarin, Kakakin majalisar jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya yi alkawarin cewa majalisar jihar za ta cigaba da goyon bayan yakin da ake yi da shan miyagun kwayoyi a jihar da illar da hakan ke yi wa matasa da mazauna jihar.

A ruwayar The Punch, Obasa ya yi wannan alkawarin ne yayin da ya karbi bakuncin jami'an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, da kwamandan jihar, Ralph Igwenagu ya yi wa jagoranci.

Kakakin majalisar ya ce yana fatan idan aka hada hannu wurin yaki da matsalar hakan zai taimaka wurin inganta lafiyar mutanen Legas.

Read also

Sarkin Musulmi Da Shugaban CAN Sun Buƙaci a Kama Musulmin Da Suka Kashe Fasto a Kano

Source: Legit.ng

Online view pixel