Mummunar Gobara Ta Sake Tashi Rigi Rigi a Wata Babbar Kasuwa a Kano
- An sake shiga halin jimami a jihar Kano biyo bayan tashin wata mummunar gobara a daya daga cikin fitattun kasuwannin da ake da su
- Mummunar gobarar dai ta tashi ne da sanyin Asuba inda ta lakume shagunan 'yan kasuwa da dama wadanda adadinsu ya wuce 40
- Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa gobarar na ci gaba da ci a kasuwar yayin da ake jiran jami'an hukumar kashe gobara ta Kano su kawo daukin gaggawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - An sake samun tashin mummunar gobara a daya daga cikin kasuwannin jihar Kano.
Wata gobara da ta tashi da sanyin safiya ta lalata shaguna akalla 50 a kasuwar Fatima Simra Multi-Purpose Market da ke yankin Dakata a jihar Kano.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta ce Shugaban kwamitin gobara na kasuwar, Dauda Haruna Chula, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma'a, 20 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan
DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta
Gobara ta tashi da sanyin asuba a Kano
Dauda Haruna Chula ya bayyana cewa wutar ta tashi ne da misalin karfe 5:40 na asuba a ranar Juma’a.
Ya bayyana cewa shagunan da abin ya shafa galibinsu na kananan 'yan kasuwa ne masu harkar samar da mai, da kuma masu sake sarrafa robobi da leda.
A cewarsa, wutar tana ci gaba da ci har zuwa lokacin da yake magana da safiyar yau.
“Bisa abubuwan da muka gani zuwa yanzu, shaguna kusan 50 ne suka riga suka kone kurmus, kuma wutar tana ci gaba da ci. Har yanzu muna jiran isowar jami’an kashe gobara na jihar Kano."
- Dauda Haruna Chula
An nemi daukin gaggawa
Dauda Haruna Chula ya lura cewa an yi ƙoƙarin tuntuɓar hukumar kashe gobara da sauran hukumomin da abin ya shafa, kuma sun tabbatar da cewa suna da masaniyar faruwar lamarin.
“Mun yi iyakacin ƙoƙarinmu wajen kiran su da sanar da su halin da ake ciki. Ina jin sautin motarsu ma a halin yanzu."
- Dauda Haruna Chula

Source: Facebook
Har yanzu dai ba a tabbatar da girman asarar da aka yi ko kuma ko akwai rayukan da aka rasa ba, amma ’yan kasuwar sun nuna damuwarsu kan jinkirin da aka samu daga jami’an bayar da agajin gaggawa.
Wannan gobara ta faru ne kwanaki ƙalilan bayan wata babbar gobara da ta shafi ’yan kasuwa sama da 1,000 a kasuwar Singer, ita ma a cikin birnin Kano.
Gwamna Abba ya dauki mataki kan gobara a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar gani da ido da kuma jajantawa ga 'yan kasuwar da gobara ta ritsa da su a babbar kasuwar nan ta Singer.
Baya ga tallafin kuɗi, gwamnan ya ba da umarnin gaggauta faɗaɗa da gyaran tituna a cikin kasuwar Singer domin sauƙaƙa zirga-zirga da kuma inganta harkokin kasuwanci.
Hakazalika, Gwamna Abba ya kara da alƙawarin samar da hasken wutar lantarki mai amfani da hasken rana a kasuwar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
