Batanci ga Annabi: An Taso Gwamnati a Gaba bayan Hukuncin Kisa ga Aminu Shariff

Batanci ga Annabi: An Taso Gwamnati a Gaba bayan Hukuncin Kisa ga Aminu Shariff

  • A ranar 10 ga Agusta, 2020, wata kotu a Kano ta yanke wa Aminu Yahaya-Shariff hukuncin kisa kan zargin batanci ga Annabi SAW
  • Amnesty International ta ce lafiyarsa ta tabarbare a gidan yari, yana fama da matsananciyar matsalar cutar asma da ke damunsa
  • Kungiyar Amnesty Int'l ta bukaci hukumomin Najeriya su janye dukkan tuhume-tuhume tare da sake shi ba tare da sharadi ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Kungiyar Amnesty a Najeriya ta sake dawo da maganar Aminu Yahaya Sheriff da aka yanke wa hukuncin kisa.

A ranar 10 ga Agusta, 2020, wata kotu a Jihar Kano ta yanke wa Aminu Yahaya-Shariff hukuncin kisa bisa zargin yin batanci ga Annabi SAW.

An bukaci hukumomi sun sake matashi da ya yi batanci ga Annabi SAW
Gwamna Abba Kabir da matashi, Aminu Yahaya Shariff. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Amnesty International.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da kungiyar Amnesty ta fitar a yau Alhamis 19 ga watan Fabrairun 2026 a shafinta na X game da hukuncin.

Kara karanta wannan

Ana batun dokar zabe, kotu ta ba hukumar INEC sabon umarni

Amnesty ta soki yadda ake tsare da matashin

Ta ce matashin yana da shekaru 22 a lokacin da aka yanke masa hukuncin, a shari’ar da aka ce ba ta cika ka’idojin adalci ba, kuma bisa tuhume-tuhume da ake zargin ba su da tushe.

Bayan ya fitar da wata waka ta WhatsApp a watan Maris na shekarar 2020, wasu fusatattun matasa sun kona gidansu.

Rahotanni sun ce ‘yan uwansa sun tsallake rijiya da baya bayan sun kusa fadawa hannun jama’a masu niyyar cin zarafinsu.

A watan Maris na 2024, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty ta kai ziyara ga Yahaya Sharif a wurin da ake tsare da shi.

Dalilin haka ta gano cewa lafiyarsa na cikin mummunan yanayi, musamman ganin yana fama da matsananciyar cutar asma wadda ke bukatar magunguna akai-akai.

Amnesty ta koka kan ci gaba da tsare matashi da ya yi batanci ga Annabi a Kano
Taswirar jihar Kano inda matashi Aminu Yahaya Shariff ya fito. Hoto: Legit.
Source: Original

Amnesty na fargabar da halin da yake ciki

Haka kuma a watan Nuwamba na 2024, kungiyar ta sake ziyartarsa, inda aka bayyana cewa duk da yana samun sauki sakamakon magungunan da ake ba shi, har yanzu yana bukatar samun magani a kai a kai domin kiyaye lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Katuwar bishiya ta kifo kan fasinjoji a mota, ta danne su sun mutu

Kungiyar ta jaddada cewa dokokin batanci ga addini na tauye ‘yancin fadin albarkacin baki wanda ya zama ruwan dare a yanzu.

Amnesty ta kuma sake yin kira ga hukumomin Najeriya da su janye dukkan tuhume-tuhume da ake yi wa Aminu Yahaya-Shariff tare da tabbatar da sakin sa nan take ba tare da wani sharadi ba.

Batanci: An yanke wa Mubarak Bala hukunci

A baya, kun ji cewa a ranar Talata, 5 ga watan Afrilun 2022, ne kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 24 kan matashi dan jihar Kano wanda bai yarda akwai Allah ba.

Mubarak Bala dai ya amsa tuhumar da ake masa na yin batanci ga Allah da Manzonsa, Annabi Muhammad SAW da ya ba mutanen da suka san shi mamaki matuka.

Kafin ya zama mara addini, matashin ya yi karatun Al-Kur'ani mai zurfi kafin aka sake daga gidan yari a ranar a watan Janairun 2025, bayan shafe kusan shekaru huɗu da rabi a tsare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.