Ramadan 2026: Lokutan Sahur da Buda Baki a Kano da Wasu Jihohin Najeriya

Ramadan 2026: Lokutan Sahur da Buda Baki a Kano da Wasu Jihohin Najeriya

  • A ranar 18 ga watan Fabrairu, 2026 ne al'ummar Musulmi a Najeriya da ma sassan duniya suka tashi da azumin farko na watan Ramadan
  • Kiyaye lokutan sahur da buda baki yana da matukar muhimmanci ga ingancin azumi kamar yadda Allah ya yi umarni a cikin Alkur'ani
  • A wannan rahoto, Legit Hausa ta kawo jadawalin sahur da buda baki na wasu manyan biranen Najeriya da shawarwari ga masu azumi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Watan Ramadan lokaci ne na musamman ga Musulmi a duk faɗin duniya don ƙarfafa alaƙarsu da Allah ta hanyar yin azumi da kuma kyawawan ayyuka.

A ranar 17 ga Fabrairu, 2026 Legit Hausa ta rahoto cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya ya sanar da ganin wata, kuma Musulmi za su tashi da azumi a washe gari.

Kara karanta wannan

Ramadan: Dakarun Hisbah sun cafke gandaye da rana gotai gotai a Kano

Jadawalin lokutan sahur da buda baki a wasu manyan biranen Najeriya a Ramadan 2026
Wasu 'yan Sudan sun hadu suna buda baki a ranar farko ta azumin Ramadan, a garin Al-Hattana da ke Omdurman, a ranar 18 ga Fabrairu, 2026. Hoto: EBRAHIM HAMID via Getty Images
Source: Getty Images

Sahur da buda baki a lokacin Ramadan

Abin lura ne cewa a Musulunci, akwai dokoki da ka'idoji na gudanar da azumi a watan Ramadan, daga cikinsu akwai kiyaye lokutan sahur da buda baki, in ji rahoton Tribune.

A cikin Suratul Baqarah aya ta 187, Allah Madaukakin Sarki ya bukaci Musulmi su ci, su sha, har zuwa lokacin da alfijir zai keto, sannan su cika azumi har zuwa dare (faduwar rana).

Kamar yadda wannan aya ta nuna, yana da muhimmanci Musulmi ya kiyaye lokacin sahur da na buda baki don kaucewa lalata azuminsa.

Saboda bambancin gari, kasa ko yanayi, lokacin yin sahur da buda baki yana bambanta ne daga wuri zuwa wuri.

A cikin wannan rahoto, Legit Hausa ta kawo maku takaitaccen bayani game da kalandar Ramadan ta 2026 da ta nuna lokutan sahur da buda baki a wasu manyan biranen Najeriya.

Daga cikin wannan kalandar, an zakulo lokutan sahur da buda baki a manyan biranen da suka hada da Legas, Abuja, Kano da Ibadan, kamar yadda shafin Hamari Web ya nuna.

Kara karanta wannan

Jihohin da suka rage lokacin tashi daga ofis alfarmar watan Ramadan a Najeriya

Lokutan sahur da buda baki (19 Fabrairu, 2026)

Birni

Sahur

Buda baki

Lagos

5:45 AM

7:00 PM

Kano

5:28 AM

6:34 PM

Ibadan

5:43 AM

6:57 PM

Abuja

5:30 AM

6:41 PM

Kaduna

5:31 AM

6:40 PM

Maiduguri

5:09 AM

6:16 PM

Jalingo

5: 14 AM

6: 26 PM

Gombe

5: 16 AM

6: 25 PM

Muhimmancin sahur da buda baki

A cikin wani Hadisin Anas bin Malik, wanda Bukhari (1923) da Muslim (1095) suka rauwaito, Manzon Allah (SAW) ya ce:

"Ku yi sahur, domin kuwa a cikin sahur akwai albarka."

Sahur ba kawai cin abinci ba ne, aiki ne na ibada wanda ke ba wa jiki karfin gudanar da ayyukan yau da kullum, amma ba dole bane, kamar yadda aka rahoto a shafin Sunnah.

Haka kuma, Musulunci ya kwadaitar da gaggauta buda baki da zarar lokaci ya yi domin bin sunnar Manzon Allah (SAW) da samun rahama.

Masu azumi su sani cewa sahur da buda baki lokuta ne na karbar addu'a, don haka ya kamata a yi amfani da su wajen mika bukatu ga Allah (SWA).

Kara karanta wannan

Kasashen da za su yi azumi mai tsawo da mafi karanci a duniya a Ramadan

An shawarci Musulmi su rika cin abinci mai gina jiki kamar tsirrai da kayan lambu, su kuma yawaita shan ruwa a lokacin azumin Ramadan.
Musulmi na gudanar da Sahur a masallacin Muhammad Al-Amin da ke Mosul, kasar Iraq a ranar 29 ga Maris, 2025. Hoto: Ismael Adnan Yaqoob/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images

Shawarwari don inganta lafiya a Ramadan

Likitoci suna ba da shawarar cin abinci mai gina jiki a lokacin sahur, kamar su hatsi da kayan lambu wadanda ke dade wa a ciki, musamman ma dabino, in ji rahoton BBC Hausa.

Haka kuma, shan ruwa isasshe tsakanin buda baki da sahur yana taimakawa wajen kare jiki daga bushewa da kasala yayin gudanar da azumi.

Yana da kyau a dinga duba jadawalin a kowace rana domin lokutan suna sauyawa da mintuna kadan, ya danganta da sauyin a kowane birni.

Mutane 7 da za su iya shan azumi

A wani labari, mun ruwaito cewa, akwai mutanen da shari'a ta dauke masu azumi a watan Ramadan, duk da kasancewarsa wajibi, kuma ɗaya daga cikin shika-shikan Musulunci.

Musulmin da ke fama da matsananciyar rashin lafiya wadda ba a sa ran samun waraka, kamar shanyewar ɓangaren jiki ko masu wankin koda ko jini, an ba su damar shan azumi.

Baya ga marasa lafiya, akwai wasu rukunan mutane da su ma aka dauke wa azumin, kamar mata masu haila ko jinin biki, amma za su rama adadin da suka sha bayan Ramadan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com