'Yan Bindiga Sun Rubuto Wasika, Sun Lissafa Garuruwa 3 da Za Su Farmaka a Arewa

'Yan Bindiga Sun Rubuto Wasika, Sun Lissafa Garuruwa 3 da Za Su Farmaka a Arewa

  • Iba Gani Adams ya yi Allah-wadai da wasikar barazanar ta'addanci da aka tsinta a kasuwar Ira dake nuna shirin kai hari a jihar Kwara
  • A cikin wasikar, 'yan ta'adda sun yi barazanar kai hare-haren bai daya a wasu garuruwa uku na karamar hukumar Oyun da ke jihar
  • Aare Ona Kakanfo na kasar Yarbawa, Gani Adams ya kuma fadi bayanan sirri da ya samu kan shirin 'yan ta'adda a Kwara da Kogi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kwara - Aare Ona Kakanfo na ƙasar Yarbawa, Iba Gani Adams, ya yi Allah-wadai da shirin da ake zargin wasu ƴan ta’adda na yi na kai hare-hare a garuruwan Kwara.

Gani Adams ya bayyana cewa 'yan ta'adda sun shirya kai hare hare a garuruwan Ira, Inaja, Aho da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Oyun a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

A zo a nema: Gwamnatin tarayya ta bude shafin daukar matasa aiki a Najeriya

Ana fargabar cewa 'yan bindiga za su kai hare-hare a wasu garuruwan Kwara
Mazauna kauyen Tantatu na zaune a wajen gidajensu a gundumar Kajuru, ranar 19 ga Maris 2024. Hoto: Emmanuel Buba / AFP via Getty Images.
Source: Getty Images

'Yan bindiga sun yi barazanar kai hare-hare

Jaridar Tribune ta rahoto cewa, Iba Gani Adams ya bayyana hakan ne bayan an tsinci wata wasikar barazanar kai hare-hare da 'yan bindiga suka ajiye a kasuwar garin Ira.

A cikin wasikar, 'yan ta'adda sun gargaɗi mazauna yankin game da hare-haren da suke shirin kai wa kansu nan ba da daɗewa ba.

Gani Adams ya yi nuni da cewa wannan barazana ta jefa fargaba mai tsanani a zukatan mazauna waɗannan garuruwa na jihar Kwara, wanda hakan ke shafar harkokinsu na yau da kullum.

Gani Adams ya bayyana cewa:

"Ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta jiha da su ƙarfafa matakan tsaro, su inganta raba bayanan sirri, da kuma tura isassun jami'ai domin dakile waɗannan hare-hare."

Fargabar kai hari a shiyyar Kudu maso Yamma

Aare Ona Kakanfo ya kuma yi kira ga dukkan hukumomin tsaro, ciki har da ƴan sanda, DSS, sojoji, da dakarun sa-kai da su ƙarfafa sintiri a Ira da sauran garuruwan da ke maƙwabtaka da yankunan

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga ya ritsa da shugaban karamar hukuma a Kaduna, an kashe mutane

A cewarsa, bayanan sirri da ofishinsa ya samu sun nuna cewa wasu ƙungiyoyin ta’adda na shirin kai hare-hare na bai-ɗaya da nufin kashe mutane, yaɗa tsoro, da kuma dagula zaman lafiyan sassan Kudu maso Yamma.

Jaridar Vanguard ta rahoto Gani Adams ya ƙara da cewa:

"Yana da matuƙar muhimmanci mu hada hannu da hukumomin tsaro domin tantancewa da kuma kai rahoton duk wani motsi na ban-zara cikin gaggawa."
Gani Adam ya roki gwamnatocin jiha da tarayya su kai dauki a garuruwan da ake shirin farmaka.
Taswirar jihar Kwara, inda ake fargabar 'yan bindiga za su kai hari. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Bukatar kare Yarbawa a Kwara da Kogi

Ya jaddada cewa tsaro da lafiyar al’ummar da ke jin yaren Yarbanci a jihohin Kwara da Kogi abu ne mai mahimmanci, kuma dole ne a haɗa kai domin tabbatar da cewa zaman lafiya ya yi tasiri a yankunan.

"Yana da muhimmanci a samar da tsaro ga garuruwan Yarbawa da ke Kwara da Kogi. Dole mu hade kanmu mu yaki wannan matsala ta 'yan ta'adda."

- Aare Ona Kakanfo na ƙasar Yarbawa, Iba Gani Adams.

Wannan gargaɗi na zuwa ne a daidai lokacin da ake kira ga gwamnati da ta sake duba tsarin tsaro a yankunan karkara domin kare rayuka da dukiyoyin talakawa.

Bidiyon mutanen da aka sace a Kwara

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya amsa gayyata, zai kai kansa ofishin EFCC a yau

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan ta'adda sun saki bidiyon mutane 176 da suka sace a garin Woro dake jihar Kwara kuma suke ci gaba da tsare su.

A cikin bidiyon, an jiyo mutanen da aka sacen, wadanda mafi yawansu mata da kananan yara ne, suna neman daukin gaggawa daga al'umma da gwamnati.

Al'ummar garin Woro, sun ce 'yan bindigar sun dade suna masu barazana, a karshe suka kai masu hari mafi muni a tarihin garin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com