Bayan Girke Sojojin Amurka, Turkiyya Ta Jaddada Aniyar Taya Najeriya Yakar 'Yan Ta'adda
- Jakadan Turkiyya, Mehmet Poroy, ya ce Najeriya da ƙasarsa na fuskantar barazanar ta’addanci masu kama da juna
- Ya bayyana cewa Türkiye ta shirya bayar da kayan aiki da haɗin gwiwar soji ga Najeriya domin a fatattaki yan ta'addan da suka damu kasar
- Mehmet Poroy, ya bayar da wannan tabbaci ne a lokacin da manyan kasar nan ke kuka da shigo da sojojin Amurka su taya yakar yan ta'adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Jakadan ƙasar Turkiyya a Najeriya, Mehmet Poroy, ya bayyana cewa ƙasarsa da Najeriya suna fuskantar irin kalubalen da suka shafi ta’addanci.
Ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairu, inda ya ce ƙasashen biyu na da sha’awar samar da tsare-tsaren yaƙi da ta’addanci masu inganci.

Kara karanta wannan
"Ana buƙatar taimako": Shehu Sani ya yi maraba da girke sojojin Amurka a Najeriya

Source: Twitter
Jaridar The Sun ta wallafa cewa jakadan ya bayyana cewa Turkiyya ta samu ƙwarewa sosai a tsawon shekaru wajen yaƙar kungiyoyin ta’addanci daban-daban.
Turkiyya na son taimakon Najeriya kan tsaro
Jaridar Punch ta ruwaito Mehmet Poroy na cewa yanzu ƙasar ta shirya ba wa Najeriya kayan aiki da gogewarta domin taimakawa wajen shawo kan matsalar tsaro.
Poroy ya jaddada cewa nasarar Najeriya wajen murkushe ta’addanci zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a Afrika baki ɗaya, musamman ta Yamma.
Ya kuma ce Turkiyya ta bunƙasa ɓangaren tsaronta domin magance tushen rashin tsaro a cikin ƙasar da ma yankunan da ke kewaye da ita.

Source: Facebook
Wannan, a cewarsa, ya taimaka wa rundunar sojin Turkiyya wajen murkushe barazanar ‘yan ta’adda, kuma Najeriya ma za ta iya amfana.
A kalaman Mehmet Poroy:
“Muna aiki tare da takwarorinmu na Najeriya domin zurfafa haɗin gwiwar soji a wannan fanni, kamar yadda shugabanmu ya bayyana cewa muna tare da Najeriya a yaƙinta da ta’addanci."
Yadda Turkiyya za ta taimaka wa Najeriya
Ya ƙara da cewa ba wai samar da kayan aikin soji kadai kamfanonin Turkiyya ke yi ba, har da aiki tare da hukumomin Najeriya domin samar da wasu kayayyaki a cikin kasar nan.
Jakadan ya ce matsayin Najeriya a matsayin ƙasa mafi girman tattalin arziki a Afrika ta Yamma kuma ta huɗu a Afrika baki ɗaya, ya sa Turkiyya ke kallonta da muhimmanci.
A cewarsa, yawan jama’an Najeriya da ya haura miliyan 230, ƙarfin tattalin arzikinta da kuma buƙatar zurfafa alaƙar kasuwanci, na sanya ƙasar ta zama mai muhimmanci ga Turkiyya.
Ya ce:
“Türkiye na kallon Najeriya a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗa a nahiyar Afirka."
Poroy ya tuna cewa dangantakar ƙasashen biyu ta samo asali tun ƙarni na 16 lokacin hulɗar daular Ottoman da Daular Kanem-Bornu.
Najeriya: An damu kan shigowar sojojin Amurka
A baya, mun wallafa cewa wasu fitattun ’yan Najeriya sun yi Allah-wadai yadda Najeriya ta bude kofa ake jibge sojojin Amurka a wasu daga cikin sassan kasar nan.

Kara karanta wannan
Ministan Tinubu ya jero yankunan da aka ba sojojin Amurka izinin shiga a Arewacin Najeriya
Mutane irinsu Dr Abubakar Siddique Mohammed, Dr Dauda Garuba, Prof Massaud Omar, Prof Mohammed Kuna, Engr YZ Ya’u, da Dr Usman Bugaje sun yi tir da lamarin.
Sun buƙaci gwamnati ta ƙarfafa sojojin cikin gida maimakon dogaro da ƙasashen waje domin yaki da matsalolin da suka dabaibaye sassa daban-daban na Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
