"Ana Buƙatar Taimako": Shehu Sani Ya Yi Maraba da Girke Sojojin Amurka a Najeriya

"Ana Buƙatar Taimako": Shehu Sani Ya Yi Maraba da Girke Sojojin Amurka a Najeriya

  • Sanata Shehu Sani ya goyi bayan haɗin gwiwar tsaron Najeriya da ƙasar Amurka don yaƙi da ƴan ta'adda
  • Da farko, hukumar tsaron Najeriya ta tabbatar da zuwan sojojin Amurka 100 da kayan aikinsu kasar nan
  • Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan batun ikon ƙasa da tsaro yayin da wasu ke ganin shigo da sojojin barazana ce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana goyon bayansa ga haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.

Tsohon Sanatan ya bayyana cewa matakin ya dace a wannan lokaci da ƙasar ke fuskantar ƙalubalen tsaro da yaki da ta'addanci.

Shehu Sani ya yi lale da sojojin Amurka
Sanata Shehu Sani, Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: @ShehuSani/Donald J Trump
Source: Facebook

Shehu Sani a yi wannan bayani ne a wata hira da ya yi a shirin The Morning Brief na Channels Television a ranar Laraba, bayan zuwan wasu dakarun Amurka Najeriya.

Kara karanta wannan

Manya sun fara nuna damuwa da jibge sojojin Amurka da aka soma a Najeriya

Matsayar Shehu Sani kan shigowar sojojin Amurka

Jarida Punch ta wallafa cewa Sanata Shehu Sani bai dace Najeriya ta ci gaba a tafarkin da ake kai inda yan ta'adda ke kashe bayin Allah ba.

Ya ce:

“Ba za mu iya ci gaba da zura ido ba yayin da ‘yan ta’adda ke kashe-kashe da sace mutanenmu, sannan mu rufe ƙofofinmu ga taimakon wasu ƙasashe."

Ya ƙara da cewa, duk da cewa yaƙin na Najeriya ne, akwai buƙatar samun goyon baya daga ƙasashen da za su iya bayar da tallafi na fasaha da horo.

Hedikwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ) ta sanar da zuwan sojojin Amurka 100 tare da wasu kayan aiki, bayan wata yarjejeniya ta tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

Yadda sojojin Amurka suka shigo Najeriya

Mai magana da yawun rundunar tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya ce haɗin gwiwar zai bai wa Najeriya damar samun ƙwarewar fasaha ta musamman domin ƙarfafa yaƙi da ta’addanci.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya jero yankunan da aka ba sojojin Amurka izinin shiga a Arewacin Najeriya

Shehu Sani ya ce ana buƙatar taimako a Najeriya
Tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani Hoto: Shehu Sani
Source: Twitter

Sai dai matakin ya jawo muhawara daga wasu ‘yan siyasa da masu sharhi, inda wasu ke nuna damuwa kan batun ikon ƙasa da kasancewar sojojin ƙasashen waje a cikin Najeriya. Shehu Sani ya amince cewa lallai akwai dalilin a shiga, amma ya ce dole a fuskanci gaskiya tsantsa a kan matsalar tsaron Najeriya.

Sai dai ya ce ikon ƙasa ya riga ya fuskanci barazana daga kasancewar ‘yan ta’adda da suka shigo daga ƙasashen waje.

Ya kuma bayyana cewa babu wata rundunar soja a duniya da ba ta yin haɗin gwiwa da sauran ƙasashe domin cimma manufofinta.

Martanin Shehu Sani ga taimakon Amurka

A baya, mun wallafa cewa Najeriya ta samu tallafin kayan aiki na sojoji a yakin da take yi da 'yan ta'adda da 'yan bindiga daga rundunar tsaron Amurka.

Kayan aikin sun iso ne yayin da Najeriya ke kara karfafa hadin gwiwar da take yi da Amurka domin tunkarar matsalar ta'addanci da ya ke son mamaye kasar.

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yabawa Amurka tare da mika kokon bararsa ga sauran kasashen duniya masu ikirirarin suna kaunar Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng