An Samu Matsaloli 2 a Shari'ar Malamin Musulunci da Ake Zargi da Hannu a Shirin Juyin Mulki

An Samu Matsaloli 2 a Shari'ar Malamin Musulunci da Ake Zargi da Hannu a Shirin Juyin Mulki

  • Hukumar DIA ta saba umarnin kotu, ta gaza gurfanar da Sheikh Sani Abdulkadir Zaria a ranar 18 ga watan Fabrairu, 2026
  • An ce maimakon haka, DIA ta mika malamin addinin musulunci ga DSS domin ci gaba da bincike kan zarginsa da hannu a shirin juyin mulki
  • Tun farko dai babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ya bada umarnin gurfanar da malamin addinin musulunci domin sauraron bukatar belinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar leƙen asirin soji ta Najeriya, (DIA), ta miƙa malamin addinin Musulunci da ake tsare da shi, Sheikh Sani Abdulkadir Zaria, ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).

Idan baku manta ba, jami'an tsaro sun cafke malamin ne bisa zarginsa da hannu a wani shirin juyin mulki kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda bai yi nasara ba.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamna Zulum ya ware Musulmi da Kiristoci 300,000, ya raba tallafin azumi

Babbar kotun tarayya.
Kofar shiga harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An karya umarnin kotu kan zargin malamin

Daily Trust ta tattaro cewa a makon da ya gabata, babbar kotun tarayya mai zama Abuja ta umarci DIA ta gurfanar da Sheikh Sani Zaria a gabanta don fara sauraron korafinsa.

Babbar kotun, a zamanta na ranar Juma'a, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Peter Lifu, ta bayar da umarnin cewa DIA ta gabatar da malamin a gabanta ranar 18 ga Fabrairu, 2026 domin a saurari buƙatar belinsa.

Matsaloli 2 da suka kawo tsaiko a kotu

Sai dai a zaman da aka koma ranar Laraba, lauyan malamin, Mohammed Sheriff, ya sanar da kotu cewa DIA ba ta gabatar da wanda yake karewa ba, tare da bayyana cewa an riga an miƙa shi ga DSS.

A daya bangaren kuma, ma’aikatan kotu sun sanar da cewa alkalin da ke jagorantar shari'ar ya je halartar rantsar da sababbin alkalai 14 na Babbar Kotun Tarayya a Kotun Ƙoli a ranar.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta ji koken musulmai, ta gyara dokar zabe saboda azumin Ramadan

Malamin da ake zargi ya kalubalanci tsare shi

Sheikh Sani Abdulkadir ya shigar da ƙara kan take haƙƙin dan Adam a gaban kotu, inda ya nemi a bada umarnin sakinsa, kamar yadda Guardian ta kawo.

Wadanda ya shigar kara sun hada da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), hukumar DIA, Antoni Janar kuma Ministan Shari'a da kuma bankin Ja'iz.

Sheikh Sani Abdulkhadir Zaria.
Malamin darikar Tijjaniya a Najeriya, Sheikh Sani Khalifa Abdulkhadir Zaria Hoto: Imam Abdullahi Usman Zaria
Source: Facebook

Majiyoyi daga iyalansa sun danganta kama malamin da kyautar Naira miliyan biyu da aka tura asusun bankin wani shugaban ƙungiyar Fityanul Islam Tijanniyya da ake tsare da shi, daga wani mabiyinsa da ake zargi a batun juyin mulkin.

Falana ya kawo rudani kan zargin juyin mulki

A wani rahoton, kun ji cewa Babban lauya a Najeriya, Femi Falana (SAN) ya kawo rudani game da shirin gurfanar da sojojin da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulki.

Falana ya ya bayyana cewa ba za a iya gurfanar da sojojin da ake zargi da shirya juyin mulki a gaban kotun sojoji ba a tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.

Falana ya jaddada cewa dole ne a gurfanar da irin waɗannan mutanen a gaban kotunan farar hula, kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya tanada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262