Dubu Ta Cika: Wasu Jagororin 'Yan Bindiga 17 Sun Shiga Hannu, 'Yan Sanda Sun Jero Sunayensu

Dubu Ta Cika: Wasu Jagororin 'Yan Bindiga 17 Sun Shiga Hannu, 'Yan Sanda Sun Jero Sunayensu

  • Dakarun 'yan sandan Najeriya sun wargaza sansanonin 'yan bindiga da dama a kananan hukumomi hudu a jihar Kaduna
  • Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Kaduna, DSP Mansir Hassan ya ce an kama wasu hatsabiban 'yan bindiga 17 a harin
  • Kwamishinan 'yan sandan Kaduna ya tabbatar wa mutane cewa rundunar za ta ci gaba da kai samame don kakkabe masu miyagun laifuffuka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama mutum 17 da ake zargin jagorori ne na dabar ’yan bindiga daban-daban da ke addabar jihar.

Dakarun 'yan sanda sun samu wannan nasara ne a yayin wani samame na musamman da suka kai sansanonin miyagu 'yan bindigar domin murkushe su a Kaduna.

Yan sanda.
Jami'an yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

’Yan sandan sun ce sun tarwstsa sansanonin ’yan bindiga tare da ƙwato bindigogi kirar AK-47 guda uku, bindigogi kirar gida guda bakwai, da adadi mai yawa na miyagun ƙwayoyi, in ji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Wanda mahaifinsa ya daure tsirara ya zama 'kwarangwal' bayan shekara 17

'Yan sanda sun samu galaba kan 'yan bindiga

Mai magana da yawun rundunar a jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Ya ce rundunar yan sandan ta gudanar da samamen ne daga ranar 10 zuwa 13 ga Fabrairu, 2026, a ƙoƙarin ta na yaƙar ’yan bindiga da sauran munanan laifuffuka.

An kai farmakin ne kan sansanonin ’yan bindiga da wuraren ɓoyewarsu a ƙananan hukumomin Kajuru, Tafa, Igabi da kuma Kauru.

An kwato makamai daga hannun miyagu

DSP Hassan ya bayyana cewa an yi musayar wuta mai tsanani da ’yan bindigar, inda aka kashe da dama daga cikinsu, sannan aka rusa sansanoninsu.

Kakakin yan sandan ya ce:

"'Yan sandan sun ƙwato bindigogi AK-47 guda uku, bindigogi bakwai da aka ƙera a gida, karamar bindigar hannu (pistol) guda ɗaya da miyagun kwayoyi."

An kuma kama wasu da ake zargi da bayar da bayanai ga ’yan bindiga da kuma masu safarar miyagun ƙwayoyi da ke da alaƙa da cibiyoyin laifuffuka, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga ya ritsa da shugaban karamar hukuma a Kaduna, an kashe mutane

Sunayen waɗanda aka kama

Rundunar ta bayyana sunayen wasu daga cikin waɗanda aka kama, ciki har da Ahamdu Bala, Abdullahi Alh. Fulani, Ado Bayero Reku, Samaila Bala, Nasiru Rabiu, Ibrahim Bello da Jafar Adamu.

Sauran su ne Nura Abdullahi, Adamu Alh. Raini, Adamu Haruna, Ado Babwuro, Shuaibu Sa’idu, Isiya Bammi, Kabiru Adamu, Habibu Rabiu, Suleiman Adam, da Abubakar Idris.

Yan sanda.
Sufeto Janar na rundunar yan sandan Najeriya, IGP Kayode Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Kwamishinan ’Yan Sandan Kaduna, Rabiu Muhammad, ya bai wa mazauna jihar tabbacin cewa za a ci gaba da kai samamen domin kawar da ’yan bindiga, dakile yaɗuwar makamai ba bisa ƙa’ida ba da sauran laifuffuka.

Miyagu sun kashe mutane a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa wasu mahara da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai harin ta'addanci a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

'Yan bindigan sun kashe mutane biyu tare da kona motar shugaban karamar hukumar Kajuru, yayin wani hari da suka kai a kauyen Ugom.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun mamaye unguwar Ehwakya da ke cikin kauyen, inda suka riƙa harbin kan mai uwa da wabi

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262