Bayan Fara Azumi, Shugaba Tinubu Ya Aika Sako ga Musulmai da Kiristocin Najeriya

Bayan Fara Azumi, Shugaba Tinubu Ya Aika Sako ga Musulmai da Kiristocin Najeriya

  • Al'ummar Musulmai da Kiristoci sun fara gudanar da azumin watan Ramadan da na Lent rana guda a wannan shekarar
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da sako ga al'ummar Musulmai da Kiristoci sako mai muhimmanci yayin da suka fara wadannan ibadun
  • Mai girma Bola Tinubu ya bukaci da su gudanar da wannan ibadu cikin kyakkyawar fahimta tare da yi wa kasa addu'a

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi muhimmin kira ga mabiya addinin Kirista da na Musulmi kan haduwar azumin watan Ramadan da na azumin Lent.

Shugaba Tinubu ya bukaci su yi amfani da damar wannan haɗuwa ta musamman ta azumin, waɗanda duka suka fara a rana guda a wannan shekara, a matsayin dama ta samar da zaman lafiya, haɗin kai, da kwanciyar hankali a kasa.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Tsohon kwamishinan INEC ya ba Tinubu shawara kan dokar zabe

Shugaba Tinubu ya aika da sako ga 'yan Najeriya
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa wadda Bayo Onanuga ya sanya a shafinsa na X a ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairun 2026.

Tinubu ya magana kan azumi

Shugaba Tinubu ya bayyana fara waɗannan lokuta biyu masu tsarki a lokaci guda a matsayin abin da ba a saba gani ba.

Tinubu ya kara da cewa wannan abu ne da ke tunatar da mu cewa ’yan Najeriya na kowane addini suna da abubuwa da dama da suka yi tarayya a kai, kuma al’umma ɗaya ne a wajen Allah.

“A wannan shekarar, azumin Lent da na Ramadan sun fara ne a rana guda."
“Wannan ba abu ne da aka saba gani ba, kuma yana tunatar da mu cewa a matsayinmu na mutane masu addini, muna da abubuwa da dama da muka yi tarayya a kai, kuma mu al’umma ɗaya ce a wajen Allah."

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamna Zulum ya ware Musulmi da Kiristoci 300,000, ya raba tallafin azumi

- Shugaba Bola Tinubu

Ma'anar waɗannan lokutan biyu

Ga Musulmai Ramadan wata guda ne na azumi, addu’a, da zurfafa tunani a kan sha'anin addini, wanda yake ɗaya daga cikin rukunai biyar na Musulunci, kuma alama ce ta mika wuya ga Allah.

Ga Kiristoci lokacin Lent kwanaki 40 ne na azumi, kame kai, da tuba, don bin misalin lokacin da Yesu Kristi ya yi a cikin daji kafin a giciye shi.

Shugaba Tinubu ya mika sako ga 'yan Najeriya
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tinubu ya mika bukatarsa ga 'yan Najeriya

Shugaban Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya da za su gudanar da waɗannan ibadu da su tabbatar da kyakkyawar fahimta da makwabtansu, bunkasa zaman lafiya, da yin addu’ar neman ci gaba da tsaron ƙasa.

“Mu yi rayuwa bisa kyawawan koyarwar addinanmu kuma mu kasance masu daraja a cikin ayyukanmu ga Allah da kuma sauran mutane."

- Shugaba Bola Tinubu

Daga karshe, Tinubu ya yi addu’ar cewa darussa da farin cikin da ke tattare da waɗannan lokuta masu tsarki su kasance tare da ’yan Najeriya a kowane lokaci.

Kara karanta wannan

'Mulki mafi muni,' Hakeem Baba Ahmed ya yi gargadi kan tazarcen Tinubu a 2027

Shugaba Tinubu tambayoyi

A wani labarin kuma, kun ji cewa ana ci gaba da tafka muhawara kan sojojin da kasar Amurka ta turo zuwa Najeriya.

Audu Bulama Bukarti ya jefo tambayoyi ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan shigowar sojojin na Amurka zuwa Najeriya.

Lauyan ya ce ya kamata a sanar da ’yan Najeriya dalla-dalla kan ainihin iyaka, tsawon lokaci da kuma sharuddan turo sojoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng