'Dan Najeriya da Sojojin Ukraine Suka Cafke a Yaki da Rasha Ya Roki Tinubu Alfarma
- Wani 'dan Najeriya, Balogun Ridwan, da ake zargin yana taya Rasha yaki a Ukraine ya shiga hannun sojojin Ukraine
- Rahotanni sun ce an yaudare shi da aikin injiniya, amma aka tilasta masa shiga rundunar sojin yakin kasar Rasha
- Ridwan ya roki Shugaba Bola Tinubu su taimaka masa ya dawo gida, yana mai cewa an yaudare shi ne a kasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kyiv, Ukraine - Wani dan Najeriya, Balogun Ridwan, wanda ake zargin ya shiga rundunar sojin Rasha domin yaki a Ukraine, ya fada hannun sojojin Ukraine.
Matashin ya nemi taimakon Shugaba Bola Tinubu bayan yaudarar shi da aka yi da sunan shiga aikin Injiniya a Rasha mai yaki da kasar Ukraine.

Source: Facebook
Yakin Rasha: 'Dan Najeriya ya roki Tinubu
Wata kafar yada labarai ta Ukraine mai suna UnitedMedia24 ta ruwaito cewa an yaudari Ridwan ne da tayin aikin injiniya a Rasha kafin daga bisani aka tilasta masa shiga aikin soja.
Rahoton ya ce an sa shi ya rattaba hannu kan kwangila da aka rubuta da harshen Rashanci, wanda bai fahimta ba.
Ridwan ya bayyana a faifain bidiyo a Youtube cewa:
“Ranar da muka sanya hannu kan kwangilar, ban fahimci yaren ba. Ba su bari mu yi amfani da wayoyinmu domin fassara shi ba, sai muka sanya hannu kawai.”
Ya kara da cewa tun farko ya sanar da su aikin da ya je nema, yana zaton za a ba shi aiki a fannin da ya kware.
A cewar rahoton, an ba shi horo na makonni kadan kafin daga bisani aka tura shi gaban yaki, inda ya bayyana horon a matsayin wanda ya cika da rudani.

Source: Getty Images
Yadda aka kama 'dan Najeriya a Ukraine
An ruwaito cewa Ridwan ya mika wuya ga sojojin Ukraine yayin wani samame da aka kai a watan Janairun 2026, duk da cewa ba a bayyana takamaiman wurin da aka kama shi ba.
A kwanan nan, an lissafta sunansa tare da wasu ‘yan Najeriya da aka ce sun mutu a fagen daga bayan an yaudare su da aikin tsaro.
Rahoton ya ce yanzu Ridwan na rokon gwamnatin Najeriya ta shiga tsakani domin a ba shi damar dawowa gida.
Ya ce:
“Na tafi Rasha da bizar yawon bude ido domin neman aiki. Gwamnatin Rasha ta yaudare ni ta mayar da ni soja, ta kuma tura ni yaki a Ukraine.”
Ya yi kira ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya gafarta masa tare da taimaka masa ya koma gida inda ya ce ya zo Rasha ne domin ciyar da iyalansa.
Lamarin na kara fito da yadda ake zargin ana yaudarar ‘yan kasashen waje da alkawuran aiki, amma daga bisani a tura su filin daga.
A baya-bayan nan ma, Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya nuna damuwa kan yadda ake daukar ‘yan Najeriya ba bisa ka’ida ba domin shiga rikice-rikicen kasashen waje.
'Dan Arewa ya makale a yakin Ukraine-Rasha
Mun ba ku labarin cewa wani ɗan Najeriya mai suna Abubakar Adamu ya roƙi Gwamnatin tarayya ta dawo da shi gida daga kasar Rasha.
Mutumin yana zargin an yaudare shi zuwa Rasha ne bayan ce masa za a ba shi aikin kula da gida a matsayin mai gadi.
Lauyoyinsa sun ce ya je Moscow da bizar yawon buɗe ido amma aka kwace masa takardunsa, aka tilasta masa shiga soja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


