Bincike Ya Tono Yadda Tsohon Minista Ya Sharara Karya game da Safarar Sassan Dan Adam
- Wani bincike ya nuna yadda Femi Fani-Kayode ya yada labarin bogi da ya rikita kafofin yada labarai daban-daban a Najeriya
- Labarin ya samo asali ne daga shafin barkwanci na karya, wanda Fani Kayode ya wallafa tare da neman a bi kwakkwafi
- Lamarin ya girmama, har ta kai Majalisar Wakilai ta kasa ta tattauna batun bayan ya bazu a kafafen yada labarai
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Wani sabon bincike ya bayyana yadda tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama kuma wanda aka taba tsayar a matsayin jakada, Femi Fani-Kayode, ya yada karya.
Binciken mai taken ya yi duba a kan labarin sayar da al'aurar maza kusan 7,221 daga Najeriya, inda aka yi safararsu zuwa kasar China.

Kara karanta wannan
'Dan Najeriya da sojojin Ukraine suka cafke a yaki da Rasha ya roki Tinubu alfarma

Source: Twitter
Premium Times ta wallafa cewa binciken ya samu jagorancin dan jarida kuma masani, Kemi Busari, inda suka bi diddigin labarin.
Yadda tsohon Minista ya yada karya
Jaridar Dubawa da ke bin diddigin labarai ta wallafa cewa a ranar 13 ga Afrilu, 2021,Fani-Kayode ya wallafa cewa wani jirgin ruwa daga Najeriya ya yi yunkurin safarar dubunnan al'aura zuwa kasar China.
Sai dai binciken ya gano cewa labarin ya samo asali ne daga shafin barkwanci na karya, World News Daily Report (WNDR), wanda ke wallafa kirkirarrun labarai.
Labarin na WNDR da aka wallafa a ranar 19 ga Maris, 2021, ya yi ikirarin cewa an kama kwalaye 36 dauke da al'aura fiye da 7,000, da darajarsu ta haura dala biliyan 1.15 a kasuwar bayan fage.

Source: Facebook
Ko da yake Fani-Kayode bai ambaci tushen bayaninsa ba, kalamansa sun yi daidai da abin da WNDR ta wallafa.
Binciken ya ce akalla kafafen yada labarai 29 a Najeriya sun sake wallafa labarin, suna jingina shi gare shi a matsayin majiya.
Labarin Kayode ya karade ko'ina
Binciken ya ce a lokacin da ya yi wallafar, Fani-Kayode yana da mabiya sama da miliyan daya a shafinsa na X, lamarin da ya taimaka wajen bazuwar labarin a cikin gaggawa.
Lamarin ya yi girman da har Majalisar Wakilai ta kasa ta tattauna batun tare da bai wa kwamitocinta umarnin bincike kan zargin safarar sassan jikin mutane.
Ko da yake masu tantance gaskiya sun karyata labarin, sakon na Fani-Kayode ya ci gaba da kasancewa a shafinsa har zuwa17 ga Fabrairu, 2026.
Binciken ya dora alhakin kan kafafen yada labarai da suka kasa tantance gaskiyar labarin kafin wallafawa.
Tsohon Minista ya soki Trump
A baya, kun ji cewa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi Allah-wadai da barazanar da Donald Trump ya yi na kawo wa Najeriya hari.
Ya zargi shugaban Amurka da ƙoƙarin haifar da rikicin addini a Najeriya, wanda hakan zai rikirkita kasar domin neman samun albarkatun da ke birne a Najeriya.
Femi Fani-Kayode ya yi kira ga ‘yan Najeriya su haɗa kai, su kare ƙasarsu daga azzaluman dake shirin kawo hatsaniyar da sai kowa ya ji a jikinsa.
Asali: Legit.ng

