Basarake Ya Shiga har Aso Villa Ya Nemi Tinubu Ya Saki Nnamdi Kanu
- Sarkin gargajiya daga Kudu maso Gabashin Najeriya, Dr Lawrence Agubuzu ya roki Shugaba Bola Tinubu da ya saki Nnamdi Kanu da aka garkame
- Lawrence Agubuzu ya yi kira da Bola Tinubu a wani taron sarakunan gargajiya da aka yi a Fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja
- Ya bayyana cewa sakin Kanu na da muhimmanci wajen shawo kan matasan yankinsu, idan kuma ba a saki Kanu ba, ya nemi a maida shi kasar Kenya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wani sarkin gargajiya daga yankin Kudu maso Gabas ya roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya saki jagoran 'yan ta'addan IPOB, Nnamdi Kanu.
Ya ce ko a sake shi ko kuma a mayar da shi Kenya inda Gwamnatin Muhammadu Buhari ta kamo shi, yana mai gargaɗin cewa ci gaba da tsare shi na ƙara tayar da hankalin matasa a yankin.

Source: Facebook
Basarake ya roki Tinubu a saki Kanu
Vanguard ta wallafa cewa Sarkin, Dr Lawrence Agubuzu, ya yi roƙo kai tsaye ga shugaban kasa a yayin taron 2026 na shugabannin gargajiya a Abuja game da Nnamdi Kanu.
“Ku fito da wannan mutumin (Kanu). Idan ba ma son ganinsa a Najeriya, ku mayar da shi Kenya ko London, inda aka ɗauko shi.
“Don Allah ku yi wani abu a kan shi. Ba za mu iya samun ci gaba a wannan ƙasa ba idan ba mu faɗa wa kanmu gaskiya ba,”
Agubuzu ga Tinubu.
Kwatanta Kanu da Sunday Igboho
Taron ya ɗauki wani sabon salo a lokacin da ake gabatar da saƙonnin fatan alheri, inda Agubuzu ya yi amfani da damar wajen matsa wa shugaban kasa lamba kan makomar Kanu.
Agubuzu ya ce Ooni na Ife ya yi kira kan hadin kai, ida ya nuna shakku kan saƙon, yana zargin cewa Ooni ɗin na shirin ba Sunday Igboho wata babbar sarauta ta girmamawa, wanda ya ce aikinsa iri daya ne da Kanu da ke rufe.

Source: Twitter
“Mai martaba yana shirin ba Sunday Igboho babbar lambar yabo ta sarauta, wanda a yankinmu na Kudu maso Gabas muke kallon sa a matsayin takwaran Nnamdi Kanu,”
Inji Agubuzu
Barazanar da sarakunan Ibo ke fuskanta
Sarkin ya kuma shaida wa Tinubu cewa akwai ƙarin fargaba tsakanin matasan Kudu maso Gabas, yana mai gargaɗin cewa sarakunan yankin na rasa amincewar jama’arsu sakamakon rashin warware batun Kanu.
Leadership ta rahoto ya ce:
“Wasu daga cikinmu ana ce mana mu je mu yi aiki, amma matasan Kudu maso Gabas sun harzuka, za su iya dukanmu."
Kungiyar IPOB ta yi martani ga Amurka
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar 'yan ta'addan IPOB ta yi martani ga wani dan majalisar Amurka kan batun raba Najeriya.
'Dan majalisar mai suna Riley Moore ya soki masu neman a raba Najeriya saboda a cewarsa Kiristoci za su sha wahala sosai.
'Yan IPOB da Nnamdi ke jagoranta sun bayyana cewa hada kasar bai jawo kare Kiristoci ba, inda suka ce raba ta ne mafita.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

