Matakan Trump Sun Fara Jefa Dubban Jama'a cikin Hadari a Jihar Yobe

Matakan Trump Sun Fara Jefa Dubban Jama'a cikin Hadari a Jihar Yobe

  • Gwamnatin jihar Yobe ta yi bayani game da yadda janye tallafin Amurka da shugaba Donald Trump ya yi ke shafar dubban al'umma
  • Shugaban hukumar YOSEMA a jihar, Muhammad Goje ya bayyana cewa matakin ya jefa jama'a kimanin 250,000 cikin hadari a sassan Yobe
  • Baya ga wadanda abin ya shafa wajen samun tallafi, rahotanni sun nuna cewa matakin shugaba Trump ya sa dubban jama'a rasa ayyukan yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Yobe - Gwamnatin Jihar Yobe ta bayyana cewa sama da mutum 250,000 ne suka shiga mawuyacin hali sakamakon umarnin dakatar tallafi da shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi a shekarar 2025.

Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Yobe (YOSEMA), Dr Muhammad Goje, ne ya bayyana hakan a wani shirin da ya gabatar.

Kara karanta wannan

Wanda mahaifinsa ya daure tsirara ya zama 'kwarangwal' bayan shekara 17

Buhun tallafin Amurka da Donald Trump
Kayan abinci a buhun tallafin Amurka da shugaba Donald Trump a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tallafin Amurka ga Yobe a baya

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Dr Goje ce tsawon fiye da shekara 10, Amurka ce babbar mai ba da tallafi a jihohin Borno, Adamawa da Yobe

Ya ce tana ɗaukar nauyin tallafin abinci a matakin gaggawa, abinci mai gina jiki, kiwon lafiya, ayyukan kariya da tallafa wa iyalan da suka rasa matsugunansu.

Trump ya dakatar da tallafi a Yobe

A cewar Goje, dakatar da tallafin Amurka ya shafi fiye da mutum 250,000 kai tsaye a Jihar Yobe bayan matakin da Donald Trump ya dauka a 2025.

Ya ƙara da cewa dakatar da tallafin ya tilasta wa ƙungiyoyin jin-ƙai rage ayyukansu, fafutukar neman kudi, ko kuma janye ayyukansu gaba ɗaya.

Dr Goje ya bayyana cewa daga cikin mutum 250,000 da abin ya shafa, kusan 13,000 yara ne da ba sa zuwa makaranta, yayin da sauran suka haɗa da ’yan gudun hijira,

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito kan zargin gwamnati na ba majalisar harkokin Musulunci ta Najeriya makudan kudi

Sauran sun hada da waɗanda ke buƙatar kariya daga cin zarafi, da kuma masu amfana da ayyukan kiwon lafiya, samar da ayyukan yi da sauran fannoni na jin-ƙai.

Ya ce:

“A shekarar 2024, tsarin jin-ƙai na Najeriya (HRP) ya buƙaci Dala miliyan 926.5 domin taimaka wa mutum miliyan 4.4.
"Daga cikin wannan adadi, an samu kusan Dala miliyan 556, inda Amurka ta bayar da kusan Dala miliyan 316, wato kusan kashi 57 cikin 100 na jimillar tallafin,”

Matakin Trump ya kawo matsalar abinci

Game da abinci kuma, Goje ya ce sakamakon umarnin Trump, raba abinci fiye da tan 650 a kowane wata da shirin abinci na duniya (WFP) ke yi zai tsaya daga watan Fabrairu 2026.

Rahoton Trust Radio ya nuna cewa shugaban a ce a halin yanzu, tallafin abincin na taimakawa kusan gidaje 65,000 a kowane wata, inda ya ce gwamnatin jihar ta fara daukar matakai.

Yadda aka raba tallafin Amurka a Najeriya
Tallafin abincin da Amurka ta raba a baya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya kuma bayyana cewa a faɗin yankin Arewa maso Gabas, ma’aikatan jin-ƙai kusan 2,508 ne suka rasa ayyukansu sakamakon dakatar da tallafin.

Dan bindiga ya kai hari Amurka

Kara karanta wannan

Aminu Vs Sanusi II: Gwamna Abba ya sake tabo batun rikicin sarautar Kano a gaban Sanata Barau

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Amurka ta tabbatar da cewa wani dan bindiga dauke da makami ya kai hari wajen da ake wasa.

Shugabar 'yan sanda ta yankin ta bayyana cewa dan bindigan ya harbe mutane 2 har lahira yayin da wasu da suka jikkata ke asibiti.

Bidiyon da aka dauka daga wajen kai harin ya nuna mutane na gudu a lokacin da mutumin ke cigaba da harbi kan me uwa da wabi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng