Gwamna Ya Tausaya wa Ma'aikata, Ya Masu Wata Garaɓasa a Wurin Aiki saboda Ramadan

Gwamna Ya Tausaya wa Ma'aikata, Ya Masu Wata Garaɓasa a Wurin Aiki saboda Ramadan

  • Gwamna Bala Mohammed ya rage awannin aikin ma'aikatan Bauchi inda za su rika tashi da karfe 3:00 na yamma a watan Ramadan
  • A cewar gwamnan, wannan matakin zai ba ma'aikata Musulmi damar yin ibada a cikin nutsuwa da kuma halartar tafsiran Al-Kur'ani
  • A gefe guda, Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya taya Musulmi da Kirista murnar fara azumin Ramadan da na Lent a rana daya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Bauchi - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya tausaya wa ma'aikatan jiharsa yayin da aka fara azumin watan Ramadan na shekarar 2026.

Mai girma Bala Mohammed ya amince da rage lokutan tashi daga aiki ga ma'aikatan gwamnatin jihar a duk tsawon lokacin azumin Ramadan na bana.

Gwamna Bala Mohammed ya rage lokutan da ma'aikata za su rika tashi daga aiki a Ramadan.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da ya rage wa ma'aikata lokutan tashi daga aiki a Ramadan. Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Gwamna ya ji tausayin ma'aikata a Bauchi

Wannan umarni na kunshe a cikin sanarwar da daraktan harkokin ma'aikata a ofishin shugaban ma'aikata, Ismail Ibn L Garam, ya fitar a ranar Talata, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamna Abba ya tuna da ma'aikata, ya yi musu tagomashi saboda azumi

Sanarwar, mai kwanan wata 17 ga Fabrairu, 2026, ta bayyana cewa wannan mataki ne na ba wa ma'aikata Musulmi damar gudanar da ibadu cikin natsuwa.

Hakazalika, gwamnan jihar ya ce ma'aikata Musulmi za su samu isasshen lokacin halartar tafsiran Al-Kur'ani a watan Ramadan.

Sabanin lokutan tashi daga aiki a Bauchi

Sanarwar ta bayyana cewa, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed, ya amince ma'aikata su riƙa tashi daga aiki a lokacin azumin Ramadan na 1447AH/2026 kamar haka:

  • Litinin zuwa Alhamis: Za a riƙa tashi da ƙarfe 3:00 na yamma.
  • Ranar Juma'a: Lokacin tashi yana nan a ƙarfe 1:00 na rana kamar yadda aka saba.

An kuma buƙaci ma'aikata da su yi amfani da wannan lokaci mai tsarki wajen gudanar da addu'o'in neman ci gaba, zaman lafiya, da haɗin kai a jihar Bauchi da kuma Najeriya baki ɗaya.

Sakon Gwamna ga Musulmi da Kirista

A ɓangare guda, Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya taya al'ummar Musulmi da Kirista murnar fara azumin Ramadan da kuma na Lent a yau Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Jihohin da suka rage lokacin tashi daga ofis alfarmar watan Ramadan a Najeriya

Gwamnan Kwara ya taya Musulmi da Kirista murnar fara azumin Ramadan da Lent a ranar guda.
Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq yana sanya hannu kan wasu takardu. Hoto: @RealAARahman
Source: Twitter

Gwamnan ya lura cewa fara azumin addinan biyu a rana ɗaya ya ƙara jaddada buƙatar kowa ya yi aiki tare don samar da zaman lafiya da kuma yaƙi da duk wani mugun nufi da zai dakile ci gaban ƙasa.

Jaridar Tribune ta rahoto Abdulrahman Abdulrazaq ya ce:

"Azumi yana buɗe wa ɗan adam wata kofa ta musamman ta kusanci ga Mahalicci ta hanyar nisantar zunubai, bayar da sadaka, da ayyukan alheri."

Ya kuma buƙaci mabiya addinan biyu da su yi aiki tare da gwamnati wajen inganta jin daɗin rayuwar jama'a tare da addu'ar samun sauƙi a cikin yanayin da ƙasar take ciki.

"Muna godiya ga Kauran Bauchi" - Badakoshi

A zantawar Legit Hausa da Bashir Abdullahi Badakoshi, wani ma'aikaci a gwamnatin jihar Bauchi, ya ce sun ji dadin wannan ragin lokacin aiki da suka samu.

Badakoshi ya ce:

"Wannan ba bakon abu ba ne, dama duk shekara yana rage lokacin zuwa aiki da Ramadan. Amma an ce yaba kyauta tukuici, mu kuma tukuicinmu shi ne godiya, don Allah ma yana son masu gode masa. Da wannan muna cewa Kauran Bauchi mun gode."

Kara karanta wannan

A zo a nema: Gwamnatin tarayya ta bude shafin daukar matasa aiki a Najeriya

Hajiya Balaraba Gwallaga, ta ce ragin lokacin aikin yana da muhimmanci gare su mata, iyaye, wadanda suke bukatar kasancewa a gida don hada kayan buda baki.

"Ai watakan mu ne da godiya. Dama muna ta zulumin yadda za mu rika yini a wajen aiki, sannan mu tashi mu koma gida mu fara shirin buda baki.
"Yanzu kuwa ka ga za mu je gida da wuri, mu hada komai da wuri, har mu saurari tafsirin Alkur'ani, kafin lokacin shan ruwa. Mun gode da wannan mataki da gwamna ya dauka."

- Hajiya Balaraba Gwallaga.

Ramadan: Gwamna zai kashe N1bn a ciyarwa

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnatin Sokoto ta ware Naira biliyan daya domin ciyar da masu azumi a Ramadan na shekarar 2026 da muke ciki.

Gwamna Ahmed Aliyu ya kaddamar da shirin a Hukumar Tarihi ta jihar, yana cewa an kara cibiyoyin ciyarwa daga 155 zuwa 170.

Shirin, wanda aka fara tun zamanin tsohon gwamna Aliyu Wamakko, na ci gaba da tallafa wa dubban mabukata domin rage radadin talauci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com