Yadda Wata Kotu a Najeriya ta Kashe N16m a Feshin Maganin Kwari
- Majalisar Dattawa ta nuna damuwa kan kashe N16m wajen feshin maganin kwari a kotun IST, alhalin wasu fannoni na fuskantar ƙarancin kuɗi
- Akwai saɓani tsakanin bukatar kotun na kashe miliyoyin kuɗi kan takardu da kuma kiran da majalisa ke yi na komawa tsarin aiki na zamani
- Kotun ta bayyana kashe makudan kuɗi kan wutar lantarki da intanet a matsayin ɓangare na abubuwan da suka cinye kasafin kuɗinta na 2025
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Talata ne mambobin Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kasuwar Hannun Jari suka tuhumi hukumar Kotun sauraron ƙararrakin Kasuwanci da Hannun Jari (IST).
Majalisar ta tuhumi kotun ne kan kashe kimanin Naira miliyan 16 wajen ayyukan shara da feshin maganin kwari a shekarar 2025.

Source: Getty Images
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa IST wata kwararriyar kotu ce da aka kafa a ƙarƙashin Dokar Zuba Jari da Hannun Jari ta 2007 (wacce aka yi wa gyaran fuska a 2025).
Kotun IST ta kashe N16m a feshin kwari
An samar don kotun ne don sasanta saɓanin dake tasowa a kasuwar hannun jari tare da yin shari’a tsakanin masu zuba jari da masu gudanar da kasuwanci, kuma ana iya daukaka ƙarar hukuncinta.
Shugaban kotun, Aminu Junaidu, ya bayyana cewa sun kashe N16m a shara da feshin maganin kwari e lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar dattawan a ranar Talata.
Rahoto ya nuna cewa Sanata Osita Izunaso ke jagorantar kwamitin, inda Aminu Junaidu ya ce IST ta kashe N16m din ne daga cikin N30m da aka ware wa wannan fanni a kasafin 2025.
Junaidu ya bayyana cewa kotun tana yin feshin ne duk bayan wata uku don hana ɓera lalata takardu masu muhimmanci.
Ya ƙara da cewa an ba da kwangilar ayyukan shara ne ga kamfanoni masu zaman kansu a fadin ofisoshinsu na shiyya-shiyya.
Kotun ta gabatar da takardun kasafin
Takardun ayyukan kotun sun nuna cewa ta kashe Naira miliyan 6.13 wajen sayen kayan rubutu na ofis da na’urorin kwamfuta.

Kara karanta wannan
Ramadan na karatowa, za a yi gyaran iskar gas da zai rage wutar lantarki a Najeriya
Junaidu ya ce kayan rubutun suna da muhimmanci wajen rubuta hukunci da fitar da kofofin shari’a (CTC) ga masu bukata, in ji rahoton Daily Trust.
Ya lura cewa ko da yake masu neman takardun suna biyan kuɗi, amma ya ce ana tura kuɗaɗen ne kai tsaye zuwa asusun gwamnati na bai-ɗaya (TSA).
“Wannan kotu ce. Dole ne mu rubuta hukuncinmu. Muna yin kwafi mu ba masu ƙara da duk wanda ya nema, shi ya sa muke amfani da kayan rubutu fiye da intanet,” in ji Junaidu.
Ya bayyana wasu kudade da kotun ta kashe a 2025 da suka haɗa da: tafiye-tafiye da bada horo (N29m), kuɗin wutar lantarki (N981m), kuɗin waya (N990m), kuɗin intanet (N702m), gyaran motoci (N3.4m), man janareta (N39m), da bada horo a cikin gida (N9.5m).

Source: Facebook
Sukar da Majalisar dattawa tayi
Wani mamba na kwamitin, Sanata Ogoshi Onawo, ya soki ci gaba da kashe kuɗi kan kayan rubutu a lokacin da ya kamata a ce ana amfani da fasahar zamani.
Shugaban kwamitin, Sanata Osita Izunaso, ya bukaci ƙarin bayani kan yadda aka kashe makudan kuɗi kan shara yayin da ba a ba fannin wayar da kan jama'a muhimmanci ba.
An yi rigima da Natasha a majalisa
A wani labari, mun ruwaito cewa, an samu takaddama a majalisar dattawa tsakanin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ma'aikatan ofishin Sanata Titus Zam.
Rikicin ya fara ne lokacin da Natasha ta je taron kwamitin majalisa kan hukumar raya Arewa ta Tsakiya, amma ta tarar an gama taron.
Sanata Natasha ta garzaya ofishin Zam, wanda shi ne shugaban kwamitin don jin dalilin cire ta daga taron, lamarin da ya jawo rikici.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

