Ana Batun Sojojin Amurka, An Kashe Kasurgumin 'Dan Bindiga da Ya Addabi Jihohi 7 a Najeriya

Ana Batun Sojojin Amurka, An Kashe Kasurgumin 'Dan Bindiga da Ya Addabi Jihohi 7 a Najeriya

  • Jami'an tsaro sun kai samamen hadin gwiwa kan sansanin wani jagoran dabar yan bindiga, Kachalla Kabiru a jihar Kogi
  • Rahotanni sun nuna cewa luguden wutar da dakaru suka yi ta sama da kasa, ta halaka Kabiru da wasu manyan mataimakansa
  • Majiyoyi sun ce kafin kashe Kachalla Kabiru, shi ke jagorantar ayyukan garkuwa da mutane da ta'addanci a jihohi har bakwai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi, Nigeria - Jami'an tsaron Najeriya sun yi nasarar kawar da wani kasurgumin dan bindiga, Kachalla Kabiru, wanda ya jima yana addabar mutane a jihohi akalla bakwai.

Wannan nasara na zuwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan sojojin da kasar Amurka ta turo, wadanda suka zo da nufin tallafawa dakarun Najeriya da horo da fasaha.

Jihar Kogi.
Taswirar jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kashe Kachalla Kabiru a jihar Kogi

Kara karanta wannan

Kano: Manyan mutane da suka ziyarci kasuwar Singer bayan mummunar gobara

Leadership ta rahoto cewa dakarun tsaron sun kashe Kachalla Kabiru, tare da wasu manyan mataimakansa a wani samame na haɗin gwiwa da suka kai a Jihar Kogi.

Jami'an da suka hadu suka kai wannan samame sun hada da jami'an ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, sojoji da dakarun hukumar DSS.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an gudanar da wannan farmaki ne a ranar 13 ga Fabrairu, 2026, bayan makonni na tattara bayanan sirri da sa ido, wanda ya tabbatar da inda Kachalla Kabiru ke ɓoye.

Jami'an tsaro sun farmaki 'yan bindiga

Rahoton The Nation ya nuna cewa harin ya haɗa da luguden wuta ta sama da jiragen yaƙi na rundunar sojojin saman Najeriya suka kai, tare da haɗin gwiwar dakarun ƙasa.

Wata majiya ta ce:

“An kashe Kachalla Kabiru da wasu daga cikin manyan mataimakansa a wani farmaki na haɗin gwiwa ta sama da ƙasa. Harin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da kasancewarsa a wurin."

Majiyar ta ƙara da cewa Kabiru yana taka muhimmiyar rawa wajen ɗaukar sababbin mayaƙa, tsara hare-hare da kuma jagorantar ’yan bindiga a jihohin yankin Arewa ta Tsakiya da maƙwabtansu.

Kara karanta wannan

Aminu Vs Sanusi II: Gwamna Abba ya sake tabo batun rikicin sarautar Kano a gaban Sanata Barau

Jihohin da Kachalla Kabiru ya addaba a Najeriya

An ce Kabiru ya yi ƙaura ne daga Arewa maso Yamma zuwa Kogi fiye da shekaru 10 da suka gabata, inda ya kafa sansani a dazuka da ƙauyukan kan iyaka.

Daga nan ne ake zargin yana jagorantar ayyukan garkuwa da mutane da ta’addanci a jihohin Kogi, Kwara, Benue, Enugu, Edo, Ekiti da Ondo, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Dakarun sojoji.
Jami'an rundunar sojojin Najeriya a cikin daji Hoto: Nigerian Army
Source: Twitter

Majiyar ta bayyana cewa:

“Kashe Kabiru babbar nasara ce a yaƙi da kungiyoyin ’yan bindiga a yankin Arewa ta Tsakiya, kuma ana sa ran hakan zai kawo cikas ga haɗin kai da shirye-shiryen miyagun laifuffuka a jihohi da dama.”

Sojoji sun kashe kwamandan Boko Haram

A wani rahoton, kun ji cewa Dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), sun samu nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun hallaka wani babban kwamandan Boko Haram mai suna Abou Aisha, wanda ya samu raunin harbin bindiga a wuyansa daga bisani ya mutu.

Sojojin sun kwace kudi kimanin Naira miliyan 37 tare da wasu wayoyin salula da ake zargin suna da alaka da ayyukan ta’addanci a jihar Borno.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262