Majalisar Shari'ar Najeriya Ta Shiga wa Kwankwaso Fada da Amurka
- Majalisar Kolin Shari'a ta Najeriya ta ba Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kariya kan zargin da wani dan majalisar Amurka ya masa
- Majalisar ta ce babu gaskiya a ikirarin Amurka a kan Kwankwaso, tana cewa akwai alamar an dagora da bayanai marasa inganci
- Wani dan majalisar Amurka ya nemi a hana Rabiu Kwankwaso biza da nufin hana shi shiga kasar kan zargin tauye hakkin addini
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Majalisar Shari’a a Najeriya (SCSN) ta yi watsi da zargin da aka ce yana cikin wani kudiri a majalisar dokokin Amurka, wanda ke zargin ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya, inda ta ce labarin ƙarya ne mai haɗari.
A cikin wata sanarwa da Sakatare Janar na majalisar, Nafiu Baba Ahmad ya sanya wa hannu, majalisar ta kuma yi Allah-wadai da abin da ta kira nufin bata suna ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso dangane da zarge-zargen.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa majalisar ta ce duk da cewa Najeriya na fuskantar manyan ƙalubalen tsaro da suka haɗa da ta’addanci, fashi da makami, babu wani shirin shafe Kiristoci daga doron ƙasa.
Zargin Amurka da aiki da bayanan bogi
SCSN ta nuna damuwa cewa wasu matakan doka da manufofi a ƙasashen waje na iya dogaro da bayanai masu tayar da hankali da marasa inganci.
Ta yi zargin cewa ana amfani da rahotannin kafafen yaɗa labarai, waɗanda ta ce ba su da cikakken fahimta kan yadda rikice-rikicen Najeriya suke.
Majalisar ta soki abin da ta kira dogaro da sharhi da labaran da ba a tantance su ba, tana mai cewa ya kamata manyan matakan da za a dauka a matakin ƙasa da ƙasa su dogara da bincike mai inganci.
Kwamitin Shari'a ya kare Kwankwaso
Game da ambaton Kwankwaso a majalisar dokokin Amurka, majalisar Shari'a ta bayyana hakan a matsayin rashin adalci da kuma son rai.
Ta kara da cewa ware mutum ɗaya daga cikin ’yan siyasar Najeriya alhali ana maganar matsalar ƙasa baki ɗaya alama ce ta nuna wariya maimakon adalci.

Source: Facebook
Majalisar ta ce babbar matsalar Najeriya ta fi karkata ne kan tsadar rayuwa da shugabanci mai rauni, waɗanda suka haifar da talauci da rashin tsaro.
Rahoton Trust Radio ya nuna cewa ta buƙaci masu sa ido su mai da hankali kan matsalolin tsarin mulki da tattalin arziki maimakon ɗaura laifi kan mutum ɗaya kawai a Najeriya.
Haka kuma, majalisar ta ce yiwuwar adawar Kwankwaso ga ayyana Najeriya a matsayin kasa mai matuƙar damuwa (CPC) bisa zargin tauye ’yancin addini na iya kasancewa daga cikin dalilan masa zarge-zarge.
Buba Galadima ya kare Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya fito ya yi magana kan zargin da Amurka ta yi wa Kwankwaso.
Buba Galadima ya bayyana cewa akwai alamar da siyasa a neman kakabawa Kwankwaso takunkumi game da zargin tauye hakkin addini a Najeriya.
Ya bayyana cewa komai da komai game da mulkin da Kwankwaso ya yi a fili ya ke, saboda haka babu wani dalilin neman kakaba masa takunkumi.
Asali: Legit.ng

