Ministan Tinubu Ya Jero Yankunan da Aka ba Sojojin Amurka Izinin Shiga a Arewacin Najeriya
- Ministan tsaron Najeriya, Janar Chirstopher Musa ya tabbatar da isowar sojojin Amurka Najeriya don taimakawa wajen yaki da ta'addanci
- Janar Musa mai ritaya ya ce a halin yanzu gwamnatin tarayya ta ba sojojin Amurka izinin shiga wasu yankuna a jihar Bauchi
- Ya jaddada cewa zuwan sojojin na daga cikin yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma wa, kuma ba zai taba 'yancin Najeriya ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da isowar sojojin kasar Amurka domin taimakawa dakaru sojin kasar nan ta fannin fasaha da leken asiri.
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya bayyana cewa shigowar sojojin Amurka cikin Najeriya na da nasaba da batun horaswa da kuma tallafin fasaha.

Source: Twitter
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da jaridar The Nation a Ma’aikatar Tsaro da ke Abuja, wadda aka fi sani da “Ship House”.

Kara karanta wannan
Kurunkus: Sojojin Amurka 100 sun shigo Najeriya, hedkwatar tsaro ta fadi Abin da ya kawo su
Sojojin Amurka sun samu izinin shiga Bauchi
A cewar ministan, sojojin Najeriya da na Amurka za su yi aiki tare a wasu yankuna na Jihar Bauchi, inda Gwamnatin Tarayya ta ba su izinin shiga domin ba da horo da tallafi a yaƙin da ake yi da ’yan ta’adda.
“Eh, wasu daga cikinsu (sojojin Amurka) sun zo, mu na aiki tare. Ban san batun zuwansu Borno ba, amma na san sun samu izinin shiga wasu yankuna a Bauchi domin taimaka mana da horo saboda yaƙin da muke yi.
"Za su taimaka mana da fasaha. Amurka na da ingantacciyar fasaha ta zamani kamar jirage marasa matuƙi da tauraron ɗan adam, waɗanda suke da matuƙar muhimmanci a gare mu,” in ji shi.
Najeriya ta taba tura dakaru wasu kasashe
Ya ƙara da cewa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe abu ne da aka saba yi, yana mai cewa Najeriya ma ta taɓa tura dakarunta zuwa ƙasashe kamar Laberiya, Saliyo, Tanzaniya da Burma domin taimako.
Ministan ya ce matsalar tsaro ta ƙara tsananta ne bayan rikicin Libya, wanda ya haddasa yawaitar makamai da masu laifi a yankin Sahel, lamarin da ya shafi Najeriya.
“’Yan ta’adda suna ko’ina, musamman bayan yankin Sahel ya rikice. Abin ya fara ne bayan faduwar Libya. Makamai da masu laifi sun kara yawaita, suka shigo yankinmu. Don haka muna buƙatar tallafin ƙasashe domin fuskantar matsalar,” in ji shi.

Source: Getty Images
Tabbacin mutunta ikon Najeriya
Ministan ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa wannan haɗin gwiwar Najeriya da Amurka na ɗan lokaci ne kuma yana ƙarƙashin yarjejeniya, cewar rahoton The Cable.
“Duk abin da muke yi bisa yarjejeniya ne, suna mutunta ikonmu da yancin kasarmu. Mun gaya musu cewa wannan aiki na ɗan lokaci ne. Da zarar an cimma burin da ake so, za su tafi,” in ji shi.
Yadda Najeriya ta nemi tallafin Amurka
A wani labarin, kun ji cewa hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta tabbatar da isowar dakarun sojojin Amurka 100 a wani bangaren yarjejeniyar da aka cimma.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun DHQ na kasa, Manjo Janar Sama'ila Uba ya rattaba wa hannu.
A cewarsa, gwamnatin Najeriya ce ta nemi Amurka ta turo dakarun sojoji masu kwarewa da za su taimaka wajen yaki da ta'addanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
