Ramadan: Dabarun da za a Yi a Ga Wata Ido da Ido a Najeriya

Ramadan: Dabarun da za a Yi a Ga Wata Ido da Ido a Najeriya

  • Bisa umarnin Mai alfarma Sarkin Musulmi, a yau Talata, 17 ga Fabrairu ne za a fita duba wata a shirin fara azumin Ramadan na shekarar 1446
  • Idan aka ga wata a yau, al'ummar Musulmi za su tashi da azumin Ramadan gobe, idan kuma ba a gan shi ba, za a jira sai ranar Alhamis, 18 ga wata
  • Wani dan kwamitin ganin wata na fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Simwal Usman ya sanar da hanyoyin da za a bi wajen ganin wata idan ya fito

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A yau Talatar ne ƙasashe da dama a faɗin duniya za su fita domin duba jinjirin watan Ramadan, wanda shi ne zai tabbatar da ranar da Musulmi za su fara azumin watan Mai alfarma a shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Shirin da ya kamata Musulmai su yi kafin 1 ga watan Ramadan

A Najeriya, mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya buƙaci al’ummar Musulmi su fita domin neman jinjirin watan a yammacin ranar Talata, 17 ga watan Fabrairu, 2026.

Simwal Usman Jibril
Simwal Usman Jibril da Sarkin Musulmi. Hoto: Simwal Usman Jibril
Source: Facebook

'Dan kwamitin ganin wata na fadar Sarkin Musulmi, Simwal Usman Jibrin ya yi karin haske kan dabarun ganin wata a wani bidiyo da ya wallafa a X.

Yadda za a ga wata ido da ido

Jami’i a kwamitin ganin wata na fadar Sarkin Musulmi, Simwal Usman Jibrin ya bayyana cewa ana fara neman jinjirin wata ne bayan faɗuwar rana a ranar 29 ga Sha’aban.

BBC Hausa ta rahoto ya ce:

“Ana neman jinjirin wata ne bayan faɗuwar rana saboda a ranar 29, rana da wata kan ɓullo kusan lokaci ɗaya kuma su faɗi kusan lokaci ɗaya. Saboda haka dole ne a jira rana ta faɗi kafin a samu damar hango shi.”

Ya ƙara da cewa ana jira kusan minti 10 bayan faɗuwar rana kafin a fara duban sararin samaniya, domin a lokacin ne hasken rana ke dusashewa yadda zai bai wa idanu damar gano siririn jinjirin watan.

Simwal ya bayyana cewa babu wani ƙayyadadden lokaci da wata ke yi a sararin samaniya a ranar farko bayan faɗuwar rana, sai dai a mafi yawan lokuta ba ya wuce minti 40 a sama kafin ya ɓace.

Kara karanta wannan

Jerin sharudda 15 da Sarkin Musulmi ya gindaya wa malaman da za su yi tafsiri a Ramadan

Bidiyon da Simwal ya yi bayani:

Ranar fara azumi a Najeriya

Idan aka ga jinjirin watan Ramadan a yammacin yau Talata 17 ga watan Fabarairun 2026, to Musulmai a Najeriya za su fara azumi gobe Laraba.

Amma idan ba a samu sahihin rahoton ganin watan ba, za a cika watan Sha’aban zuwa kwana 30, sannan a fara azumi ranar Alhamis, 19 ga watan Fabarairun 2026.

Wata a sararin samaniya
Yadda wata ya fito a sararin samaniya. Hoto: Simwal Usman Jibril
Source: Facebook

Izala ta tura masu tafsirin Ramadan

A wani labarin, kun ji cewa Kungiyar Izala ta tura malamai sama da 2,000 tafsirin Ramadan zuwa jihohi da wasu kasashen duniya.

Shugaban kungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Lau zai jagoranci tafsiri a jihar Adamawa, mataimakinsa, Sheikh Usman Isa Taliyawa zai yi a Gombe.

Sakataren kungiyar Izala na kasa, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe zai yi tafsirin Ramadan a hedkwatar kungiyar da ke Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng