Bulama Bukarti: Zaɓi 2 da Suka Rage wa El Rufa'i kan Zargin Kutsen Wayar NSA
- Wani lauya kuma masani kan harkokin tsaro, Bulama Bukarti, ya bayyana cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya sa kansa a matsala
- Bulama Bukarti ya ce tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya furta kalaman da ke nuna ya saurari kiran wayar Malam Nuhu Ribadu ba bisa ka'ida ba
- Ya ce ko da an ce kuskure ne, zabi biyu ya rage wa El-Rufa'i a kan wannan matsala a kotu, kuma dukkaninsu ba masu dadi ba ne ga babban 'dan siyasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Lauyan kuma mai sharhi kan harkokin tsaro, Bulama Bukarti, ya soki masu cewa Nasir El-Rufai bai taɓa cewa ya saurarar kiran wayar Nuhu Ribadu.
Lauyan ya bayyana cewa ba shi da alaka ta kusa ko ta nesa da tsohon gwamnan ko Mashawarcin Shugaban kasa a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Source: Twitter
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Bulama Bukarti ya ce ko da an ce El-Rufa'i ya yi subul da baka ne, ya aikata laifi mai girma da ya yi gum da bakinsa.
Bulama Bukarti ya dura a kan Nasir El-Rufa'i
Bulama Bukarti ya bayyana cewa a hirar da kunnensa ya jiye masa, ya ji Nasir El-Rufa'i ya ce suna sauraron wayar da Nuhu Ribadu ke yi.
Ya ce:
“Waɗanda ke cewa El-Rufai bai ce ya saurari kiran wayar NSA ba, ko dai ba su kalli hirar ba ne ko kuma suna yaɗa ƙarya da gangan.”
Ya ƙara da cewa a hirar, El-Rufai ya bayyana cewa:
“Muna sauraron kiran wayoyinsu."
A cewarsa, daga baya El-Rufai ya ce wani ne ya saurarar wayar ya ba shi labari, amma bai taɓa nuna cewa maganar farko kuskure ba ce.
Wani zabin ya rage wa El-Rufa'i?
Bulama Bukarti ya ce ko da za a yi hujjar cewa kalaman farko na El-Rufai kuskure ne, rashin kai rahoton wanda ke saurarar kiran wani da kuma amfana da hakan laifi ne.

Source: Facebook
Ya kuma bayyana cewa ba shi da wata matsala ta kashin kai da El-Rufai ko kuma goyon bayan Nuhu Ribadu. A cewarsa:
“Ban taɓa haɗuwa da ko ɗayansu ba, kuma ban taɓa magana da su ta waya ba. Amma ba zan iya jure wa ɗan siyasa ya fito a talabijin na ƙasa ya amsa cewa ya aikata laifi ba, sannan ya sha saboda yana cikin ɓangaren adawa.”
Ya ƙara da cewa idan har shari’ar ta kai kotu, El-Rufai zai fuskanci zaɓi biyu ne kawai: ko dai ya nace a kotu cewa abin da ya faɗa gaskiya ne, wanda hakan zai zama kamar amsa laifi.
Bulama Bukatar ya kara da cewa zabi na biyu ga tsohon gwamnan shi ne ya amsa cewa shi makaryaci ne, kuma ya shata karya a kafar talabijin.
A kalamansa:
“Ko dai El-Rufai yana ƙarya ne, ko kuma shi mai laifi ne. Ban san wanne ne zai fi masa muni ba."
DSS ta yi maganan kan El-Rufa'i
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ta bayyana dalilin da ya sa ta kwace fasfo din tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a a Abuja.
Hukumar DSS ta kuma tabbatar da cewa ta fara binciken El-Rufai da ɗansa kan zargin hannu a ɓacewar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, a shekarar 2019.
Majiyoyi daga cikin hukumar sun bayyana cewa an kwace fasfo din ne a ranar Alhamis 12 ga watan Fabrairu, 2026 a filin jirgin Abuja Abuja domin hana shi komawa Masar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


