Zargin Kutsen Waya: Lauya Ya Jero Kuskuren da ke Tattare da Tuhumar El Rufa'i
- Gwamnatin tarayya ta shigar da ƙara tana tuhumar Mallam Nasir El-Rufai da laifin ta’addancin yanar gizo kan zargin sauraron wayar NSA
- Wannan ya biyo bayan kalaman da Nasir El-Rufa'i ya yi na cewa sun samu wasu muhimman bayanai a kan tsare shi ta ɓarauniyar hanya
- Sai dai wani lauya mai fafutukar kare hakkin dan adam, Inibehe Effiong ya ce tuhumar na da matsaloli akalla uku ta fuskar dokar Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Fitaccen lauya kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Inibehe Effiong, ya soki tuhumar da ake yi wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan zargin aikata laifin yanar gizo.
Gwamnatin tarayya na zargin El-Rufai da cewa ya yi ikirarin an saurari wayar Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu bayan an yi masa kutse.

Kara karanta wannan
Bayan taawon kwanaki, an ji dalilin kwace fasfon Malam El Rufai a filin jirgin Sama

Source: Twitter
A sakon da ya wallafa a shafin sa na X, Barista Effiong ya ce idan aka duba tuhumar da kyau, akwai tambayoyi masu yawa da ke bukatar amsa.
Lauya ya ga kuskure a tuhumar Nasir El-Rufa'i
Da farko, Barista Effiong ya ce babu wata hukuma da doka ta sani da suna Department of State Services (DSS) kamar yadda aka ambata a takardar tuhumar.
A cewarsa:
“Dokar hukumomin tsaro na kasa ta amince ne kawai da State Security Service (SSS), ba DSS ba.”
Ya kara da cewa dokar ba ta kuma bai wa hukumar tsaro ta farin kaya, SSS hurumin gurfanar da mutane a gaban kotu ba.
Haka kuma, lauyan ya yi tambaya kan ko furucin da El-Rufai ya yi zai iya zama hujjar da za a kira “extrajudicial statement” a karkashin doka. A cewarsa:
“Don a dauki magana a matsayin furuci da ya kunshi amsa laifi, dole ne a yi ta ne karkashin gargadi.”
Sai dai tun a nan-take,w asu lauyoyi suka ankarar da shi cewa kotu ta saba yi wa hukumar DSS hukunci guda da SSS, sabanin sunan bai canza komai wajen alkalai.
Lauya ya kare El-Rufa'i
Barista Inibehe Effiong ya kara cewa El-Rufai bai ce shi ne ya saurari wayar NSA ba, sai dai ya ce wani ne ya yi hakan kuma ya sanar da shi.
“Bai ce shi ne ya yi kutsen ba. Ya ce wani ne ya yi kuma ya ba shi labari."
Lauyan ya kuma tunatar da cewa kundin tsarin mulki ya bai wa duk wani dan kasa kariya daga tilasta masa bayar da shaida a kansa.
“Babu wata kotu da za ta tilasta masa bayar da shaida da za ta cutar da kansa."

Source: Facebook
Duk da cewa ya ce ba ya cikin masoyan El-Rufai, Effiong ya jaddada cewa tuhumar da aka shigar na da matsala a fuskar doka.
“Ni ba masoyin El-Rufai ba ne, amma wannan tuhuma tana da matsala a bangaren doka."
Bulama Bukarti wanda shi ma lauya ne kuma har ya yi digirin PhD a ilmin shari'a ya ce idan aka ji hirar da aka yi da El-Rufai, za a fahimci yana cikin matsala.
A shafin X, Dr. Bulama Bukarti ya ce tsohon gwamnan ya furta cewa suna sauraron wayarsu, wanda hakan yake nuna kai-tsaye da hannunsa a laifin kutsen wayar Nuhu Ribadu.
Gwamnati ta kai El-Rufa'i kotu
A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin tarayyar Najeriya ta shigar da kara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Ana tuhumar El-Rufai da satar bayanan sadarwar wayar Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu bayan Kalamansa a wata hira da ya yi.
Rahotanni sun nuna cewa matakin shari’ar ya biyo bayan zargin da ake yi cewa tsohon gwamnan na da masaniya ko kuma hannu a lamarin da ya shafi satar bayanan sadarwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

