Bayan Tsawon Kwanaki, An Ji Dalilin Kwace Fasfo na Malam El Rufai a Filin Jirgin Sama

Bayan Tsawon Kwanaki, An Ji Dalilin Kwace Fasfo na Malam El Rufai a Filin Jirgin Sama

  • Hukumar DSS ta yi karin haske jan dalilan da suka jawo ta kwace fasfo na tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai
  • Ana zargin cewa jami'an DSS sun yi yunkurin kama El-Rufai a lokacin da ya sauka daga jirgi a Abuja bayan ya dawo daga kasar Masar
  • Wata majiya ta ce DSS ta samu labarin tsohon gwamnan zai koma Masar da zaran ya kammala amsa tambayoyi a hukumar EFCC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), ta bayyana dalilin da ya sa ta kwace fasfo din tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a filin jirgin sama a Abuja.

Hukumar DSS ta kuma tabbatar da cewa ta fara binciken El-Rufai da ɗansa kan zargin hannu a ɓacewar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, a shekarar 2019.

Kara karanta wannan

Yadda ta kaya tsakanin El Rufai da jami'an hukumar EFCC bayan ya amsa gayyata

Tsohon gwamna.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma jagora a jam'iyyar ADC, Malam Nasir El-Rufai Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

Dalilin karbe fasfon Nasir El-Rufai

Wata majiya mai ƙarfi ta shaidawa Vanguard cewa an kwace fasfo din ne a ranar Alhamis a filin jirgin Abuja Abuja domin hana shi komawa Masar bayan ya shigo Najeriya.

Majiyar ta ce El-Rufai yana da masaniyar cewa hukumar DSS na bincikensa kan lamarin Dadiyata, kuma ya shirya amsa gayyatar hukumar EFCC da ICPC masu yaki da rashawa.

A cewar majiyar, bayanai sun nuna cewa tsohon gwamnan ya shirya komawa birnin Alkahira na ƙasar Masar bayan kammala amsa tambayoyi.

DSS ta fara bincike kan sace Dadiyata

Ta ƙara da cewa an sake buɗe batun sace Dadiyata bayan watanni ana bincike mai zurfi, wanda ya nuna cewa El-Rufai, wanda shi ne gwamnan Kaduna a lokacin, yana da masaniya kan abin da ya faru.

An sace Dadiyata, malami a Sashen Turanci da Ilimin Harsuna na Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-Ma, Jihar Katsina, a ranar 1 ga Agusta, 2019, daga gidansa da ke Kaduna, kuma har yanzu ba a san inda yake ba.

Kara karanta wannan

Yadda jama'a suka fito zanga zanga da El Rufa'i ya ziyarci EFCC

Lamarin ya jawo hankalin ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa, ciki har da Amnesty International, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Bayanan da aka samu daga El-Rufai

A wata hira da ya yi a tashar Arise TV, El-Rufai ya ce ya samu labarin wani ɗan sanda da ya tuba wanda ya amsa cewa yana cikin tawagar da aka turo daga Kano domin sace Dadiyata.

Sai dai ya musanta cewa Dadiyata mai sukar gwamnatinsa ne, yana mai cewa bai ma san shi ba, kuma ya danganta lamarin da gwamnatin Kano ta wancan lokaci ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje.

Dakarun DSS.
Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a bakin aiki Hoto: @OfficialDSSNg
Source: Twitter

Sai dai majiyar tsaron ta ce kalamansa cewa wani ɗan sanda ya amsa da hannunsa aka sace Dadiyata, kuma aka ɓoye bayanin tsawon lokaci, abin mamaki ne.

Ta ce tun farko, kamata ya yi a mika wannan bayani ga hukumomin bincike, musamman ganin yadda lamarin ya jawo hankalin duniya.

Majiyar ta kuma ce binciken sirri ya nuna cewa El-Rufai na amfani da sunan Ganduje da kuma zargin wani ɗan sanda a matsayin kariya.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito kan zargin gwamnati na ba majalisar harkokin Musulunci ta Najeriya makudan kudi

Gwamnatin Tinubu ta fara shari'a da El-Rufai

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu.

Gwamnatin ta maka El-Rufai a kotu ne saboda zargin yi wa wayar mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu kutse, wanda ya saba wa doka.

Haka kuma gwamnati ta yi zargin cewa El-Rufa'i ya aikata laifi da suka hada da sanin wasu da suka aikata hakan ba tare da kai rahoto ga hukumomin tsaro ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262