El Rufai na Hannun EFCC, Atiku Ya Aika Sakon Taya Murna ga Tsohon Gwamnan Kaduna
- Atiku Abubakar ya taya Nasir El-Rufai murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya kira shi da jarumi kuma mutum mai basira
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ayyukan El-Rufai suna nan a bayyane duk da tsangamar siyasa da yake fuskanta
- A halin yanzu, El-Rufai ya na hannun hukumar EFCC, tun bayan da ya mika kansa ofishinsu na Abuja a safiyar ranar Litinin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya taya tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Atiku ya bayyana El-Rufai a matsayin mutum mai "ilimi, jarumta, da kuma basira ta musamman" a cikin wasiƙar taya murnar da ya fitar a yau Litinin.

Source: Twitter
Atiku ya karfafi gwiwar El-Rufai
Tsohon mataimakin shugaban kasa ya aika wa Malam Nasir El-Rufai wannan sakon ne a shafinsa na X.
A cewar Atiku, nasarorin El-Rufai da kuma kyakkyawar manufarsa a bayyane suke ga kowa, duk da irin ƙalubalen siyasa da yake fuskanta a halin yanzu.
Atiku Abubakar ya ce:
"Ina taya Malam Nasir El-Rufai murnar zagayowar ranar haihuwa. Mutum ne mai ilimi, jarunta, da kuma basira ta musamman a rayuwa.
"Duk da tsangwamar siyasa da yake fuskanta a yanzu, ba za a taba yin adawa da kyawawan ayyukansa da manufofinsa a fannin shugabanci ba."
Atiku ya ci gaba da yi wa El-Rufai fatan alheri, inda ya roƙi Allah ya ba shi ƙarfi da kuma shiriya a cikin shekarunsa na gaba.
Rigingimun da suka kewaye El-Rufai
Wannan saƙon ya zo ne a lokacin da labarai da suka shafi El-Rufai suke ci gaba da zama a shafukan farko na jaridu, tun bayan yunƙurin kama shi da aka yi a filin jirgin saman Abuja.
Haka zalika, hukumomin EFCC da ICPC sun aika masa da takardun gayyata domin amsa wasu tambayoyi game da ayyukansa bayan dawowarsa daga ƙasar Masar.
A ranar Lahadi, El-Rufai ya aika wa Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, takarda yana neman ƙarin bayani kan wani sinadarin guba da ake zargin an shigo da shi kasar, kamar yadda muka ruwaito.

Source: Twitter
Martanin ofishin Ribadu ga El-Rufai
Rahoto ya nuna cewa ofishin Nuhu Ribadu ya umarci El-Rufai da ya miƙa dukkan hujjojin da yake da su ga hukumar DSS domin gudanar da bincike.
Wannan takun-saka dai yana ƙara ruruta wutar siyasa tsakanin ɓangaren tsohon gwamnan da kuma mambobin gwamnatin tarayya dake ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Masu lura da lamura na ganin cewa saƙon Atiku zuwa ga El-Rufai wani babban mataki ne na siyasa duba da irin halin da tsohon gwamnan yake ciki.
El-Rufai zai kai kansa ofishin EFCC
A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i zai gurfana a gaban EFCC a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairu, 2026.
Ya bayyana haka ne bayan yunkurin da wasu jami'an tsaron Najeriya suka yi yunkurin cafke shi a filin jirgin Abuja a makon da wuce.
Da ba su samu damar tafiya da shi ba, jami'an DSS sun kwace fasfon tsohon gwamnan, yayin da ya ke zargin ana masa bita da kulli.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

