Gwamnati Ta Gurfanar da El Rufa'i a gaban Kotu kan Zargin Kutsen Waya
- Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a gaban kotu bayan wasu kalamai da ya yi
- A makon da ya gabata ne El-Rfai ya ce sun samu wasu bayanai a kan shirin kama shi bayan an yi kutse a wayar Nuhu Ribadu
- Gwamnatin tarayya ta yi martani, inda ta dauki matakin shari'a tare da mika batun gaban Babbar kotun tarayya da ke Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta shigar da kara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a kan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
Ta dauki matakin shari'a a kan tsohon gwamnan bisa zargin satar bayanan sadarwar wayar Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.

Source: Twitter
Jaridar Zagazola Makama ta wallafa cewa takardun kotu sun nuna cewa El-Rufai mai shekaru 65 ya bayyana a matsayarsa a ranar 13 ga Fabrairu, 2026.
Gwamnati ta kai El-Rufa'i kotu
A cewar masu gabatar da kara, a yayin hirar da El-Rufa'i ya yi a makon da ya wuce, tsohon Gwamnan ya amince da cewa yana da masaniya ko kuma hannu a lamarin da ake zargi.
Haka kuma gwamnati ta yi zargin cewa El-Rufa'i ya aikata laifi da suka hada da sanin wasu da suka aikata hakan ba tare da kai rahoto ga hukumomin tsaro ba.

Source: Twitter
An shigar da karar ne karkashin lamba TABU DET CR/99/2026. A tuhuma ta farko, ana zargin ya amince a bainar jama’a cewa shi da wasu abokan hulda sun shiga katsalandan a sadarwar wayar NSA.
Gwamnatin ta bayyana cewa wannan al'amari ya sabawa sashe na 12(1) na dokar hana laifuffukan yanar gizo ta shekarar 2024.
Tuhumar da ake yi wa El- Rufa'i
Tuhuma ta biyu na cewa ya bayyana sanin wasu da suka aikata wannan laifi amma bai kai rahoto ba, wanda ake ganin ya ci karo da sashe na 27(b) na dokar da aka ambata.
Sai kuma tuhuma ta uku wadda ke zargin amfani da wasu na’urorin fasaha wajen jefa al’umma cikin fargaba tare da barazana ga tsaron kasa, da ya saba da sashe na 131(2) na dokar sadarwa ta 2003.
Lauyoyin Gwamnatin Tarayya da suka hada da M.E. Ernest, O.M. Owan, U.M. Bulla, C.S. Eze da V.E.G. Orubor ne suka shigar da karar.
Sun bayyana cewa lamarin na karkashin ikon sashen shari’a na Abuja na Babbar Kotun Tarayya, inda ake sa ran wanda ake kara zai gurfana domin amsa tuhume-tuhumen.
Hukumomi sun ce za a ci gaba da bincike da kuma zaman shari’a kamar yadda doka ta tanada domin a tabbatar da adalci.
El-Rufa'i ya amsa gayyatar EFCC

Kara karanta wannan
Babbar magana: Ganduje ya yi magana kan batan Dadiyata, ya maida martani ga El Rufai
A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i zai gurfana a gaban EFCC a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairu, 2026 domin amsa dukkanin tambayoyin hukumar.
Ya bayyana haka ne bayan yunkurin da wasu jami'an tsaron Najeriya suka yi yunkurin cafke shi a filin jirgin Abuja a makon da wuce inda masoyansa suka shiga tsakaninsa da jami'an.
Da ba su samu damar tafiya da shi ba, jami'an DSS sun kwace fasfon tsohon gwamnan, yayin da ya ke zargin ana masa bita da kulli saboda rawar da zai taka wajen adawa da gwamnati.
Asali: Legit.ng

