Trump Ya Jero Sunayen 'Yan Najeriya da Ya Kwace Kadarorinsu a Amurka

Trump Ya Jero Sunayen 'Yan Najeriya da Ya Kwace Kadarorinsu a Amurka

  • Gwamnatin Amurka karkashin shugaba Donald Trump ta kakabawa mutane takwas 'yan asalin Najeriya takunkumi da kwace kadarorinsu
  • Kasar Amurka ta wallafa sunayen mutanen da fadin laifuffukan da ta ke zarginsu da aikatawa da ke da alaka da Boko Haram da sauransu
  • Matakin na nuna cewa mutanen ba za su shiga kasar Amurka ba, idan suna da dukiya a can za a rike ta da kuma sauran abubuwa na dabam

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Ƙasar Amurka ta daskarar da kadarori da dukiyoyin ’yan Najeriya takwas da ake zargi da alaƙa da ƙungiyar Boko Haram da ISIL.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai shafuka 3,000 mai kwanan wata 10 ga Fabrairun 2026, wanda ofishin kula da kadarorin kasashen waje (OFAC) na ma’aikatar kuɗi ta Amurka ya fitar.

Kara karanta wannan

Bukarti: Abubuwa 3 da Najeriya za ta kiyaye bayan sojojin Amurka sun sauka Borno

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaban Amurka, Donald Trump a wajen taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Vanguard ta wallafa cewa Amurka ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin ta na hana mallakar dukiya ga waɗanda aka ayyana a matsayin 'yan ta'adda tare da hana mu’amalar kuɗi da su.

Takunkumin Trump ke 'yan Najeriya

Daga cikin waɗanda aka lissafa kan alaka da Boko Haram akwai Salih Yusuf Adamu, wanda aka fi sani da Salihu Yusuf, an haife shi a ranar 23 ga Agusta, 1990, a Naijeriya..

Cikin wadanda aka kakakbawa takunkumi akwai Babestan Oluwole Ademulero da aka haifa a ranar 4 ga Maris, 1953, a Najeriya, an bayyana shi da sunaye daban-daban ciki har da Wole A. Babestan da Olatunde Irewole Shofeso.

Haka kuma an sanya Abu Abdullah ibn Umar Al-Barnawi, wanda aka fi sani da Ba Idrisa, cikin jerin. An ce an haife shi tsakanin 1989 da 1994 a Maiduguri, Jihar Borno.

Amurka ta sanya Abu Musab Al-Barnawi da kuma ake kira Habib Yusuf a matsayin jagoran Boko Haram kuma ta kakaba masa takunkumi bisa dokokin da suka shafi ta’addanci.

Kara karanta wannan

INEC ta fadi dalilan sa zaben 2027 a Ramadan da matakin da za ta dauka

An danganta Khaled (ko Khalid) Al-Barnawi, wanda sunansa ya bayyana sau biyu a cikin takardar da laifin ta'addanci, an haife shi a shekarar 1976 a Maiduguri, Najeriya.

Sauran da aka kabbawa takunkumi

Ibrahim Ali Alhassan da aka haifa a ranar 31 ga Janairu, 1981, a Najeriya da ke zaune a Abu Dhabi, Hadaddiyar Daular Larabawa, an ce yana da alaƙa da Boko Haram.

Sauran sun hada da Abu Bakr ibn Muhammad ibn Ali Al-Mainuki, wanda aka fi sani da Abu-Bilal Al-Minuki da aka haifa a 1982 a Mainok, Jihar Borno. An bayyana cewa yana da alaƙa da ISIL.

Nnamdi Orson Benson da aka haifa a ranar 21 ga Maris, 1987, a Najeriya, Amurka ta sanya shi cikin jerin takunkumin damfara ta yanar gizo.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Katsina
Shugaban Najeriya yayin wata ziyara jihar Katsina a 2025. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Takunkumin na nufin an rike duk kadarori da abubuwan waɗannan mutane da ke ƙarƙashin ikon Amurka, kuma an hana ’yan Amurka yin mu’amala da su.

Dan Najeriya ya mutu a Amurka

A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar sojin Amurka ta sanar da cewa wani dan Najeriya da ke cikin sojojinta ya rasu a bakin aiki.

Kara karanta wannan

Da sake: ADC ta dura a kan Tinubu saboda yunkurin kama El Rufa'i

An bayyana cewa matashi dan asalin Najeriya mai shekara 21 ya rasu ne bayan fadowa daga jirgin ruwan soja ana tafiya a cikin teku.

An sanar da cewa ya rasu ne bayan shafe sa'o'i ana nemansa ba a gan shi ba, Amurka ta mika sakon ta'aziyya ga 'yan uwansa baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng