El Rufa'i Ya Amsa Gayyata, Zai Kai Kansa Ofishin EFCC a Yau

El Rufa'i Ya Amsa Gayyata, Zai Kai Kansa Ofishin EFCC a Yau

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i zai gurfana a gaban EFCC a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairu, 2026
  • Ya bayyana haka ne bayan yunkurin da wasu jami'an tsaron Najeriya suka yi yunkurin cafke shi a filin jirgin Abuja a makon da wuce
  • Da ba su samu damar tafiya da shi ba, jami'an DSS sun kwace fasfon tsohon gwamnan, yayin da ya ke zargin ana masa bita da kulli

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - A yau Litinin, 16 ga watanFabrairu, 2026 ne tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, zai bayyana a gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC.

El-Rufai ya tabbatar da hakan ne bayan wata takaddama da ta barke tsakaninsa da jami’an Hukumar Tsaro ta DSS a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Kara karanta wannan

"Ƙila don ya ƙi APC ne": El Rufa'i ya yi tir da kai sunan Kwankwaso majalisar Amurka

Tsohon gwamnan Kaduna zai je ofishin EFCC
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa a wasu jami'ai sun yi yunkurin kama El-Rufa'i ne bayan dawowarsa daga Cairo.

El-Rufa'i zai gurfana a gaban EFCC

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa tsohon gwamnan ya ce tun yana kasar waje EFCC ta aiko masa da takardar gayyata zuwa gidansa.

Sai dai lauyoyinsa suka sanar da hukumar cewa ya saba yin wata tafiya a karshen kowace shekara, kuma zai amsa gayyatar da zarar ya dawo gida.

Ya kara da cewa tun kafin ya iso Najeriya ya shaida wa EFCC cewa zai je ofishinta a ranar Litinin 16 ga watan Fabrairu domin amsa tambayoyin.

EFCC ta gayyaci El-Rufa'i tun yana kasar waje
Shugaban EFCC na kasa, Olu Olakayode Hoto: Economic and Finacial Crimes Commission
Source: Facebook

Ranar ta zo daidai da ranar haihuwarsa. Har zuwa yanzu, ba a fito karara a bayyana takamaiman dalilin da ya sa ake son yi masa tambayoyi ba.

Haka kuma babu cikakken bayani daga hukumomin da lamarin ya shafa a kan zarge-zargen da ake yi wa babban 'dan adawan.

Kara karanta wannan

Bayan sha da kyar, El Rufai ya fadi adadin jami'an tsaron da suka so cafke shi

Yadda jami'ai suka so damke El-Rufa'i

A ranar Alhamis 12 ga watan Fabrairu, 2026, jami’an DSS sun rike fasfon El-Rufai a filin jirgin Abuja jim kadan bayan ya sauka a jihar.

An kuma ce sun yi kokarin tafiya da shi, amma ya bukaci su gabatar da takardar kotu da ta ba su ikon yin hakan.

Rahotanni sun nuna cewa wasu jama’a da ke wurin sun nuna rashin amincewarsu da matakin jami’an, lamarin da ya sa ba a samu tafiya da shi ba.

Daga baya, El-Rufai ya zargi Hukumar ICPC da amfani da jami’an DSS domin kama shi ba bisa ka’ida ba.

Ya kuma danganta lamarin da Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan Sha’anin Tsaro, inda ya ce ana amfani da hukumomi wajen takura masa saboda sabanin siyasa.

Bashir El-Rufa'i ya kare mahaifinsa

A baya, mun wallafa cewa dan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Bashir El-Rufai, ya yi karin haske kan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan kalaman mahaifinsa, Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan

Bayan EFCC, wata hukumar binciken rashawa ta gayyaci El Rufai, zai sha tambayoyi

Bashir ya bayyana cewa mahaifinsa bai taba cewa shi ne ya aikata laifin kutsen waya ko satar sauraren wayar wani ba, kamar yadda ake kokarin manna masa.

Ya ce ana kuskuren fahimtar abin da ya fada ne, inda wasu ke kokarin alakanta shi da aikata laifi kai tsaye. Sai dai ya ce wani ne ya saurari hirar kuma ya bayar don radin kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng