'Dan Majalisar Kaduna da Ƴan Ta'adda Suka Sace Ya Shaƙi Iskar Ƴanci

'Dan Majalisar Kaduna da Ƴan Ta'adda Suka Sace Ya Shaƙi Iskar Ƴanci

  • Rahotanni sun bayyana cewa ƴan ta'adda sun saki ɗan majalisar Kaduna, Hon. Usman Garba Zingo bayan rahoton sace shi
  • Bayan labarin cewa an yi garkuwa da Hon. Zingo, Majalisar dokokin Kaduna ta musanta rahoton, inda ta ce ba a sace shi ba
  • Amma a wani bidiyo, an ga jama'a suna taya ɗan majalisar murnar shaƙar iskar ƴanci bayan ya shafe kwanaki a hannun ƴan bindiga

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kadunao– Ɗan majalisar jihar Kaduna, Hon. Usman Garba Zingo, ya samu ‘yancin bayan ƴan ta'adda sun sako shi a yammacin ranar Lahadi, 15 ga watan Fabrairu 2026

Rahotanni sun bayyana cewa mazauna yankin da iyalansa sun samu nutsuwa da farin ciki, yayin da magoya bayansa suka rika tururuwa zuwa gidansa don taya murna.

Kara karanta wannan

Bashir El Rufa'i ya fadi yadda mahaifinsa ya samu bayanan wayar Nuhu Ribadu

An saki dan majalisar Kaduna da ake zargin an sace
Taswirar jihar Kaduna inda ake zargin an sace ɗan majalisa Hoto: Legit.ng
Source: Original

Bakatsine ya wallafa a shafin X cewa an yi zargin an sace Hon. Zingo a yayin da yake kan hanyarsa daga jihar Zamfara zuwa Kaduna.

Sai dai Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta fito fili ta musanta cewa an yi wani garkuwa da ɗan majalisar.

Jama'a sun cika gidan ɗan Majalisar Kaduna

A.cikin bidiyon da Bakatsine da ya wallafa, an ga mutane suna taya ɗan majalisar murna bayan dawowarsa, ana ƙoƙarin miƙa masa hannu tare da taya shi jaje.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a fitar da cikakken bayani kan yadda aka samu nasarar sakinsa ba.

Ba a san ko an cika wasu sharudda ko kuwa an cimma wata yarjejeniya ba, domin jami’an tsaro da iyalansa ba su yi bayani a hukumance ba.

Mutane sun taya ɗan majalisar dokokin jaje

Labarin dawowar Hon. Zingo ya bazu, mazauna yankinsa sun taru domin tarbar sa, inda suka nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa dawowarsa cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 200 sun shiga garuruwa 3 da Asubah, sun kashe mutane sama da 30

Yan sanda ba su fitar da bayani a kan sako dan majalisa ba
Wasu daga cikin ƴan sandan Najeriya Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Su ma masu bibiyar shafin Bakatsine sun bayyana ra'ayoyinsu mabambanta a kan dawowar ɗan majalisar da aka musanta cewa an sace shi.

@ArimSman ya ce:

"Labari mai daɗi. Idan shugabannin siyasa su ne waɗanda wannan matsalar tsaro mai ta shafa, rashin ingantaccen kiwon lafiya da kuma lalacewar tsarin ilimi, za a tilasta masu magance matsalolin.

@milordi ya ce:

"Mutanenku suna cewa a bar ‘yan bindiga haka nan. Duk wanda ya nemi a yi musu ruwan bama-bamai, maƙiyin Arewa ne."

@AliAli33361018 ya ce:

"Dattawan Arewa da malamai su fito su yi zanga-zanga kan matsalar tsaro a Arewa. Ba kullum sai zanga-zangar “a cire Amupitan, Shugaban INEC” ba. Su yi zanga-zanga kan kashe-kashe da garkuwa da mutane a Arewa."

An sako mutane a jihar Kaduna

A baya, kun ji cewa an sako Kiristocin da aka yi garkuwa da su yayin da suke tsakiyar ibada a wani coci da ke Kurmin Wali, yankin Kufana a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

'Baki ke yanka wuya,' Hadimin Tinubu ya bukaci a binciki El Rufai kan zargin kutsen waya

Rahotanni sun tabbatar da cewa mutanen sun kuɓuta daga hannun ’yan bindiga bayan shafe makonni da dama suna tsare, lamarin da ya ba su damar komawa cikin iyalansu lami lafiya

An sace su ne a ranar 18 ga Janairun 2026, a lokacin da suke gudanar da ibadar Lahadi a cikin cocin. Majiyoyi sun ce maharan sun kutsa cikin garin tare da ɗaukar masu ibadar zuwa wani wuri.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng