Ramadan: Sanata Ya Jika Takakawa da Abin Alheri a Yobe, an Raba Buhuna 17,000

Ramadan: Sanata Ya Jika Takakawa da Abin Alheri a Yobe, an Raba Buhuna 17,000

  • Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya yi rabon abinci ga talakawa a Yobe saboda azumin Ramadan
  • Ahmed Lawan ya raba buhuna 17,000 na shinkafa, gero da sukari ga al’ummar Yobe domin tallafa musu a Ramadan
  • An gudanar da rabon ne a karamar hukumar Nguru ta hannun gidauniyar Sanata Ahmed Ibrahim Lawan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Nguru, Yobe - Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya tausayawa yan mazabarsa ana shirin azumi.

Ahmed Lawan ya raba buhuna 17,000 na shinkafa, gero da sukari ga al’ummar Jihar Yobe domin tallafa wa Musulmai a watan Ramadan.

Ahmed Lawan ya yi rabon Ramadan
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan. Hoto: Abdullahi Muhammad Nasir.
Source: Facebook

An gudanar da bikin rabon kayan ne ranar Lahadi a karamar hukumar Nguru ta jihar, karkashin kulawar gidauniyar Senator Ahmed Ibrahim Lawan, cewar Punch.

Ramadan: Yadda yan siyasa ke rabon abinci

Kara karanta wannan

Gwamna ya ware Naira biliyan 1, zai ciyar da talakawa abinci a watan Ramadan

Mafi yawan yan siyasa na amfani da lokacin azumin watan Ramadan domin tunawa da yan mazabarsu wadanda wani lokaci ake daukar lokaci ba a hadu ba.

A yanzu, wasu yan siyasa sun fara rabon wanda ya haɗa da na Sanata Ahmed Lawan da kuma gwamnatin jihar Sokoto da ya umarci biyan albashi saboda Ramadan karkashin jagorancin Ahmed Aliyu.

A shekarar bara, yan siyasa da dama sun yi ta gasar rabon kudi da kayan abinci saboda al'ummarsu ta samu sauki.

Sanata ya raba kayan abinci a Yobe saboda Ramadan
Bikin raba kayan abincin Ramadan da aka yi a Yobe. Hoto: SAIL Media Team.
Source: Facebook

Sanata Ahmed Lawan ya raba kayan azumi

Da yake jawabi a wajen taron, Lawan wanda Bashir Nguru ya wakilta, ya ce an shirya tallafin ne domin taimaka wa al’ummar Musulmi su gudanar da watan Ramadan cikin sauki.

Ya kara da cewa za a raba buhunan 17,000 din daidai a kananan hukumomi 17 na jihar, inda kowace za ta samu buhu 1,000 na shinkafa, sukari da gero.

Ya bayyana cewa za a raba kayan ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, magoya baya da kuma marasa galihu a fadin jihar.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta fadi tanadin da ta yi wa al'ummar Musulmi

“Wannan karamci yana nuna kudirina na tsayawa tare da al’ummata a lokutan farin ciki da kuma kalubale."

Ya ce wannan mataki zai taimaka wa mabukata su mai da hankali kan ibadunsu a wannan wata mai alfarma, cewar Vanguard.

Har ila yau, ya ce tallafin ya dace da kokarin Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Yobe na rage wahalhalun rayuwa da jama’a ke fuskanta.

Da yake magana a madadin Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Yobe, Alhaji Auwalu Dan-Kwayo ya yaba da wannan shiri.

Ya ce tallafin zai taimaka matuka wajen saukaka matsin tattalin arziki da talakawa ke fuskanta, musamman a wannan watan na Ramadan.

Ramadan: Gwamnan Sokoto ya raba kayan abinci

Mun ba ku labarin cewa gwamnatin Jihar Sokoto ta ware Naira biliyan daya domin ciyar da masu azumi a Ramadan na shekarar 2026 da muke ciki.

Gwamna Ahmed Aliyu ya kaddamar da shirin a Hukumar Tarihi ta jihar, yana cewa an kara cibiyoyin ciyarwa daga 155 zuwa 170.

Shirin, wanda aka fara tun zamanin tsohon gwamna Aliyu Wamakko, na ci gaba da tallafa wa dubban mabukata domin rage radadin talauci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com