An Saka Sunan Mahaifiyar Tinubu da Fasto Ya Gina Makeken Masallaci, Ya Sha Yabo
- Fasto Elijah Ayodele, ya kaddamar da sabon masallaci da ya gina a matsayinsa na Kirista a Lagos da ke Kudancin Najeriya
- Ayodele ya bayyana dalilin gina masallacin inda ya ce ba shi da nufin komawa Musulunci saboda niyyar da ya yi na shekaru
- Malamin ya raba motoci, adaidaita sahu, fom din WAEC da kayan tallafi, yayin da limamai da sarakuna suka yaba masa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya kaddamar da masallacin da ya gina.
Ayodele ya sanya masa sunan mahaifiyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Hajiya Abibatu Mogaji.

Source: Facebook
Fasto ya kaddamar da masallaci a Lagos
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a lokacin bikin godiya na shekara-shekara da aka yi ranar Asabar, 14 ga Fabrairu, 2026 a Jihar Legas, cewar The Nation.
Taron ya samu halartar manyan baki daga bangarorin addini, gargajiya, siyasa da nishadi, ciki har da wakilai daga sassa daban-daban na kasar nan.
Daga cikin mahalarta akwai Iyaloja-Janar ta kasa, Folashade Tinubu-Ojo, wacce ta aike da wakilai saboda rashin samun damar halarta da kanta.
Haka kuma akwai wakilin gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, wakilan Etsu Nupe, da dan majalisar wakilai mai wakiltar Oshodi/Isolo.
Da yake jawabi, Primate Ayodele ya bayyana cewa gina masallacin umarni ne daga Allah, kuma ba zai iya sabawa wannan umarni ba.
Ya ce masallacin gidan ibada ne kamar yadda ake da coci-coci, yana mai cewa ba shi da tsoron sukar da wasu za su yi.
Game da sanya sunan masallacin da sunan mahaifiyar Tinubu, ya ce Allah ne ya ba shi wannan umarni duk da yana da wani suna daban a farko.
Ya kara da cewa bai yi hakan don neman wata mukami ko alfarma daga gwamnati ba, sai don biyayya ga umarnin Allah.

Source: Twitter
Malaman Musulunci sun yabawa Fasto Ayodele
Wani malamin Musulmi da aka gayyata ya yaba masa, yana cewa wannan alama ce ta hadin kai tsakanin addinai biyu a kasar nan.

Kara karanta wannan
Lamari ya girma, bayan ganawa da Tinubu, Gwamna ya kori duka 'yan majalisar zartarwa
Babban Limamin Ikorodu ya bukaci jama’a su ji tsoron Allah, yana cewa aikin da Ayodele ya yi ya nuna gaskiyar malamtarsa.
Etsu Nupe ma ya yi masa addu’a tare da kira ga sauran malamai su yi koyi da ayyukan alheri da yake yi, cewar TheCable.
Baya ga masallacin, Ayodele ya raba motoci, adaidaita sahu, kananan bas-bas, fom din WAEC da kayan lantarki ga al’umma.
Sarkin Isolo ya yaba masa, yana cewa irin wadannan ayyuka suna tallafa wa gwamnati tare da karfafa hadin kai a kasa.
Shi ma Eze Ndigbo ya yi masa godiya, yana alkawarin ci gaba da mara masa baya tare da taimaka wa wani mara lafiya mai bukatar dashen koda.
Fasto ya sake gargadin Tinubu kan gwamnoni
An ji cewa fitaccen limamin coci a Najeriya, Fasto Elijah Ayodele, ya yi hasashen wahalar da Shugaba Bola Tinubu zai fuskanta a zaben 2027.
Ayodele ya yi ikirarin cewa ya hango wasu gwamnoni takwas a APC da ba za su marawa kudirin tazarcen Shugaba Tinubu baya ba.
Ya kuma bayyana cewa akwai wani babban kusa a siyasar Najeriya da zai sauya sheka zuwa jam'iyyar hadaka, ADC nan ba da jimawa ba.
Asali: Legit.ng
