Abin da ake Zaton Ya Jawo Gobarar da Ta Laƙume Miliyoyin Naira a Kasuwar Singer
- Shugaban gamayyar kungiyoyin kasuwar Singer, Barista Junaidu Muhammadu Zakari ya bayyana gobarar a matsayin babbar jarrabawa
- Gobarar da ta tashi da kusan 4.30 na yammacin Asabar, 14 ga watan Fabrairu ta shafe kusan kwana daya tana ci kafin a samu shawo kanta
- Wani ɗan kasuwa Nazifi ya shaida wa majiyar Legit cewa shi da mahaifinsa sun yi asarar da ta haura Naira miliyan 30 a gobarar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Shugaban gamayyar kungiyoyin ƴan kasuwar Singer, Barista Junaidu Muhammadu Zakari, ya bayyana gobarar da ta tashi a kasuwar Singer da ke Kano a matsayin babbar jarrabawa.
Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 15 ga watan Fabrairu 2026, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kashe ragowar wutar da ta laƙume sassa da dama na kasuwar.

Source: Facebook
A wani bidiyo da Iconic Times Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook, Junaidu ya yi bayani kan abin da ake zargin ya haddasa gobarar da ta gigita jama'a.
Dalilin gobarar kasuwar Singer
A cewarsa, kasuwar ta cika maƙil a ranar Asabar da misalin ƙarfe, kasancewar ranakun Asabar kasuwar Singer na yawan samun baƙi, musamman ma da yake ana shirye-shiryen azumin watan Ramadan.
Ya ce:
"Kasuwar ta cika sosai, sai ga wuta ta tashi a gidan Gilas da ke kan kwanar Singer. Wasu na zaton ko dai matsalar 'solar' ce ko kuma wani abu da ya shafi wutar lantarki.”
Ya ƙara da cewa yanayin tashin gobarar ya ba su tsoro matuƙa, inda ya misalta yadda wutar ta kama kamar an jefa wata nakiya. Barista Junaidu ya ce gwamnati ta taɓa yin alkawarin faɗaɗa kasuwar domin rage cunkoso da kuma kare aukuwar irin wannan mummunan haɗari a nan gaba
Babura kusan 200 sun ƙone a Singer
Wani ɗan kasuwa da ya rasa shagonsa da na mahaifinsa, Nazifi Adam Isa, ya shaida cewa an yi asarar dukiya mai tarin yawa sakamakon gobarar.

Source: Original
A cewarsa, babura da suka ƙone a daren ranar Asabar kaɗai sun kai kusan 200, baya ga kekuna sama da 100 da ya tabbatar sun ƙone ƙurmus.
Ya ce:
“Akwai shagona da na mahaifinmu da muka rasa. An yi asara sosai. Akalla babura kusan 200 sun ƙone, kuma kekuna sama da 100 ma sun lalace, ban ma magana kan sauran kayan shago ba.”
Nazifi ya bayyana cewa a gidansu kaɗai sun yi asarar sama da Naira miliyan 30. Ya roƙi shugabannin kasuwa da hukumomi da su ƙara sanya ido tare da ɗaukar matakan kariya, domin riga-kafi don gaba.
Abba ya nemi agaji a kan gobarar Singer
A baya, kun ji cewa Gwamna Abba Yusuf ya bukaci gwamnatin tarayya ta samar da jiragen sama na kashe gobara biyo bayan tashin wuta a kasuwar Singer ta Kano.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Yadda gobara ke cinye Kasuwar Singer, Gwamna Abba Ya Nemi Taimakon Tinubu
Gwamnan na jihar Kano ya jinjina wa kokarin ma'aikatan kashe gobara yayin da ya ziyarci kasuwar da ta babbake a ranar Asabar zuwa wayewar Lahadi tana ci.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga yan kasuwa da su kwantar da hankulansu tare da baiwa jami'an agaji cikakken hadin kai domin shawo kan wutar.
Asali: Legit.ng

