Gwamatin Tinubu Ta Gargadi Matasa Masu Shiga Soja a Rasha, Ta Gano Yadda Ake Yi

Gwamatin Tinubu Ta Gargadi Matasa Masu Shiga Soja a Rasha, Ta Gano Yadda Ake Yi

  • Gwamnatin Najeriya ta yi gargadi ga ’yan kasa kan fadawa tarkon daukar su yaki a kasashen waje da ake yi yanzu
  • Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce ana yaudarar matasa da alkawarin aiki mai tsoka, karatu da zama yan kasa
  • Gwamnati ta ce duk wanda ya shiga irin wannan lamari yana yin hakan ne ba tare da sanin gwamnati ba kuma akwai hatsari

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gargadi ’yan kasa da su yi hattara da duk wani tayin aiki ko tafiya da zai kai su shiga yaki a kasashen waje.

Wannan gargadi ya biyo bayan rahoton mutuwar ’yan Najeriya biyu a kasar Ukraine yayin da suke yaki a bangaren Rasha.

An kashe wasu matasan Najeriya 2 a Ukraine
'Yan Najeriya da Ukraine ta ce ta kashe bayan shiga sojin Rasha. Hoto: Головне управління розвідки Міністерства оборони України.
Source: Facebook

Rasha: Gargadin gwamnati ga matasan Najeriya

Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin waje ta wallfa a Facebook.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya kadu da tashin mummunar gobara a Kano, ya tura sako ga Abba, Tinubu

Tuggar ya nuna damuwa kan yadda ake yaudarar matasa da alkawarin aiki mai tsoka, guraben karatu da damar samun takardar zama dan kasa.

A cewarsa, rahotanni sun nuna cewa wasu ’yan Najeriya ana jawo su ne da karya, inda ake sanya su rattaba hannu kan kwangilar soja ba tare da cikakken bayani ba.

Rahoton ya ce wasu ma ana kwace musu takardunsu da zarar sun isa kasar, sannan a tura su yankunan yaki.

An kuma bayyana cewa wasu dillalai na taimakawa wajen shirya tafiya da biza ta yawon bude ido ko wata hanya daban, ba tare da an sanar da su hakikanin abin da ke gabansu ba.

Gwamnatin Tinubu ta gargadi matasa kan zuwa Rasha yaki
Ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar. Yusuf Maitama Tuggar.
Source: Twitter

Hannunka mai sanda ga matasan Najeriya

Gwamnatin ta jaddada cewa duk dan Najeriya da ya shiga irin wannan yaki ba tare da sahalewar hukuma ba, yana yin hakan ne da radin kansa.

Ta ce irin wadannan ayyuka na iya saba wa dokokin Najeriya da na kasa da kasa da suka shafi aikin soja da hayar mayaka.

Ministan ya ce hukumomi na aiki tare da abokan hulda na cikin gida da na kasa da kasa domin bincike da dakile wannan matsala.

Kara karanta wannan

Yadda Ukraine ta kashe 'yan Najeriya da suka shiga sojan Rasha a fagen daga

Haka kuma an umurci ofisoshin jakadancin Najeriya a kasashen waje da su kara sa ido tare da ba da shawara ga ’yan kasa.

Gwamnatin ta bukaci iyaye, shugabannin al’umma da makarantu su fadakar da matasa kan hatsarin fadawa irin wannan tarko.

Ta kuma shawarci ’yan kasa su rika tabbatar da duk wata damar aiki ko karatu ta hanyoyin gwamnati kafin daukar mataki.

Najeriya ta tabbatar da kudurinta na kare mutunci da jin dadin ’yan kasarta a gida da waje.

Rasha: Dan Arewa ya bukaci dawo da shi gida

Mun ba ku labarin cewa wani ɗan Najeriya mai suna Abubakar Adamu ya roƙi gwamnatin tarayya ta dawo da shi gida daga kasar Rasha.

Mutumin yana zargin an yaudare shi zuwa Rasha ne bayan ce masa za a ba shi aikin kula da gida a matsayin mai gadi.

Lauyoyinsa sun ce ya je Moscow da bizar yawon buɗe ido amma aka kwace masa takardunsa, aka tilasta masa shiga soja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.