Wata Sabuwa: Duk da Suna Jam'iyya 1, Tsohon Sanatan APC Ya Kwarewa Tinubu Baya
- Gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta sha nanata cewa manufofinta kan tattalin arziki suna samar da sakamako mai kyau
- Wani tsohon sanatan jam'iyyar APC, Abubakar Yusuf, ya fito ya saba da wannan matsaya da gwamnatin Najeriya ta ke dauka
- Sanata Abubakar Yusuf ya bayyana abubuwan da yake ganin a wajensa kura-kurai ne, wadanda Tinubu ya yi tun bayan hawa kan kujerar mulki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wani Sanata da ya wakilci mazaɓar Taraba ta Tsakiya a majalisar dattawa, Abubakar Yusuf, ya yi magana kan manufofin tattalin arziki na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sanata Abubakar Yusuf ya bayyana cewa manufofin tattalin arziki na Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba su samar da sakamakon da ake tsammani.

Source: Facebook
Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Politics Today' na tashar Channels tv.
Tsohon sanata ya yi kalamai kan Tinubu
Wannan kalamiai nasa na ɗaya daga cikin mafi ƙarfin suka da aka samu daga cikin jam’iyyar APC mai mulki tun bayan hawan gwamnatin.
Kalaman sun nuna irin rashin gamsuwa da ke ƙaruwa a wasu sassa na jam’iyyar game da yadda ake tafiyar da gyare-gyaren tattalin arzikin kasar, musamman a daidai lokacin da tsadar rayuwa da matsin rashin kuɗi ke karuwa a faɗin Najeriya.
Me sanatan ya ce kan gwamnatin Tinubu?
Sanata Abubakar Yusuf ya yi aiki a majalisar dattawa tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023 a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC.
Ya bayyana cewa tsarin manufofin gwamnatin Tinubu kan tattalin arziki ba su dace da Najeriya ba.
“A cikin tsarin manufofin nasu, kwarai, suna iya kokarinsu, amma wannan tsarin bai dace da Najeriya ba a daidai lokacin da Shugaba Asiwaju ya hau kan mulki.”
- Sanata Abubakar Yusuf
Abubakar Yusuf ya soki tsarin Shugaba Tinubu
Sanata Abubakar Yusuf ya soki matakin janye tallafin man fetur nan take a ranar da aka rantsar da shugaban kasa, inda ya bayyana cewa shawarar ba ta samu cikakkiyar tattaunawa da tsare-tsare yadda ya kamata ba.
“Ina ɗaya daga cikin waɗanda ke cewa ya kamata Shugaba Asiwaju ya jira tukunna. Ba wai kawai a ranar da aka rantsar da shi ya ce 'tallafi ya tafi' ba. A kan wane dalili?”
- Sanata Abubakar Yusuf
Ya buƙaci a riƙa yin shawarwari masu zurfi kafin a ɗauki manyan matakan da suka shafi fannin harkokin kuɗaɗen kasa.

Source: Twitter
Tsohon sanatan ya kuma yi watsi da hujjar cewa cire tallafin ya halatta ne kawai don yaƙi da cin hanci da rashawa.
“Ka zauna da majalisar ministocinka, ka zauna da ministocinka, ka zauna da masu ba ka shawara."
- Abubakar Yusuf
Kotu ta amince a binciki Ministan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata Babbar kotun tarayya ta amince da bukatar da aka gabatar mata kan Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo.
Babbar kotun ta amince da bukatar da ke neman izinin bincikar takardun shaidar karatu na Olubunmi Tunji-Ojo wanda a baya ya kasance dan majalisar wakilai.
Bukatar wadda wani 'dan gwagwarmaya, Emorioloye Owolemi, ya shigar, na neman a bincika sahihancin takardar shaidar kammala sakandare (WAEC) da Ministan ya samu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

