Babbar Magana: Ganduje Ya Yi Magana kan Batan Dadiyata, Ya Maida Martani ga El Rufai

Babbar Magana: Ganduje Ya Yi Magana kan Batan Dadiyata, Ya Maida Martani ga El Rufai

  • Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya tanka wa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai kan batun bacewar Abubakar Idris, watau Dadiyata a 2019
  • Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa ya bayyana zargin da Malam El-Rufai ya jingina masa a matsayin mara tushe ballantana makama
  • Ganduje ya nuna tausayawa ga iyalan Abubakar Idris 'Dadiyata', yana mai cewa abin da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne gano gaskiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira da a binciki tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, bayan da ya danganta shi da ɓacewar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.

Ganduje, tsohon gwamna a jihar Kano, ya bayyana zargin da Malam El-Rufai ya jingina masa a matsayin “marar tushe, rashin hankali, da kuma yunƙurin kauce wa alhakin abin da ya faru a Kaduna.”

Kara karanta wannan

El Rufai ya ci gaba da ragargazar gwamnatin APC, ya fadi bambamcinsa da ita

Abdullahi Umar Ganduje.
Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje CFR
Source: Twitter

Premium Times ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Kano, Muhammad Garba, ya sanya wa hannu.

Zargin da El-Rufai ya jingina wa Ganduje

Tun da farko, El-Rufai ya yi iƙirarin cewa an sace Dadiyata ne daga gidansa da ke Kaduna ta hannun ‘yan sanda da aka turo daga Jihar Kano, a lokacin da Ganduje ke gwamna.

A wata hira da ya yi da Arise TV ranar Juma’a, El-Rufai ya ce Dadiyata ba mai sukar gwamnatinsa ba ne kamar yadda ake zato, sai dai mai caccar gwamnatin Ganduje ne.

Ganduje ya maida martani ga El-Rufai

A nasa ɓangaren, Ganduje ya musanta zargin gaba ɗaya, yana mai cewa Dadiyata yana zaune kuma yana aiki ne a Kaduna, inda aka fi saninsa da sukar gwamnatin jihar a lokacin.

Muhammad Garba ya ce:

“Kowa a Kaduna ya san irin sukar da yake yi da kuma wanda yake nufi da ita.”

Kara karanta wannan

Ganduje ya aika muhimmin sako ga Kwankwaso wajen zaman makoki a Kano

Ya ƙara da cewa alhakin tsaron Dadiyata a lokacin yana hannun gwamnatin Kaduna da hukumomin tsaro na tarayya da ke aiki a jihar.

Nasir El Rufai.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma jagora a jam'iyyar ADC, Malam Nasir El-Rufai Hoto: Nasir El-Rufai
Source: Twitter

Ganduje ya tausaya wa iyalan Dadiyata

Sanarwar ta buƙaci a yi taka-tsantsan da kalaman El-Rufai, tana mai cewa irin waɗannan manyan zarge-zarge dole ne su kasance tare da hujjoji masu ƙarfi, ba kalaman siyasa ba.

Ganduje ya nuna tausayawa ga iyalan Dadiyata, yana mai cewa abin da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne gano gaskiya ta hanyar bin doka da tsari.

“Iyalansa suna buƙatar sanin gaskiya. Ba su cancanci a mayar da wannan lamari mai raɗaɗi ya zama abin jayayyar siyasa ba,” in ji Garba.

A ƙarshe, ya buƙaci duk wanda ke da sahihin bayani kan lamarin ya miƙa shi ga hukumomin da suka dace, yana jaddada cewa dole ne a gina irin wannan zargi bisa hujjoji da bin doka, ba zato ba.

El-Rufai ya gano wanda ya sa a kama shi

A wani labarin, kun ji cewa tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi ikirarin cewa sun saurari wayar mai ba shugaban kasa shawara kan taaro, Nuhu Ribadu.

Kara karanta wannan

Bayan EFCC, wata hukumar binciken rashawa ta gayyaci El Rufai, zai sha tambayoyi

Malam El-Rufai ya kuma zargi Nuhu Ribadu da hannu a yunƙurin kama shi a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Alhamis.

Sai dai bai gabatar da wata hujja da ke tabbatar da zargin ba, kuma har zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga Nuhu Ribadu kan zargin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262