Tsohon Yaron Ganduje Ya Fadi Illar da Tikitin Jonathan, Kwankwaso Zai Yi wa Tinubu

Tsohon Yaron Ganduje Ya Fadi Illar da Tikitin Jonathan, Kwankwaso Zai Yi wa Tinubu

  • Salihu Tanko Yakasai ya magantu kan tasirin tikitin hadin gwiwar Goodluck Jonathan da Rabiu Musa Kwankwaso a zaben Najeriya
  • Tsohon hadimin Abdullahi Ganduje ya bayyana sauya sheƙar Abba Kabir Yusuf zuwa APC a matsayin cin amana ga Rabiu Musa Kwankwaso
  • Yakasai ya ce Arewa na jin an ware ta a mulkin Bola Tinubu, yana mai cewa Atiku Abubakar ko Jonathan ne kaɗai za su iya tara kuri’un Arewa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Wani tsohon hadimin yada labarai na tsohon Gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasai, ya magantu kan zaben 2027 a Najeriya.

Yakasai ya ce hadakar tikitin Goodluck Jonathan da Rabiu Musa Kwankwaso za ta girgiza siyasar 2027 tare da tada hankalin Bola Tinubu da APC.

An fadi firgicin da Tinubu zai shiga idan aka hada Kwankwaso da Jonathan a 2027
Sanata Rabiu Kwankwaso da Bola Tinubu. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Yakasai ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar TheCable wanda ta wallafa a YouTube inda ya ce irin wannan hadaka za ta jefa shugaba Bola Ahmed Tinubu cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ganduje ya yi magana kan batan Dadiyata, ya maida martani ga El Rufai

Yakasai ya magantu kan shigar Abba APC

Da yake magana kan sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa APC, Yakasai ya ce yana da 'yancin haka, amma ya bayyana hakan a matsayin cin amana.

Ya ce Abba ya shafe kusan shekaru 40 karkashin kulawar Kwankwaso, yana mai cewa dangantakarsu ta zarce ta siyasa zuwa ta uba da ɗa.

A cewarsa, matakin da gwamnan ya dauka ya raba tafiyar Kwankwasiyya gida biyu, inda wasu ke tare da Kwankwaso, wasu kuma ke goyon bayan Abba.

Yakasai ya ce duk da haka, siyasar Kano ba ta tabbata sai a ƙarshe, domin sauyi guda kaɗai na iya sauya alkibla kafin zaɓen 2027.

Yakasai ya yi hasashe kan zaben 2027
Rabiu Kwankwaso, Bola Tinubu da Goodluck Jonathan. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Goodluck Jonathan.
Source: Facebook

Hasashen Salihu Yakasai kan zaben 2027 a Najeriya

Game da takarar shugaban kasa, ya ce Kwankwaso ba zai samu tikitin takara ba, amma zai fi dacewa da kujerar mataimaki idan dan takarar daga kudu ne.

Ya kara da cewa idan Atiku Abubakar ya zama dan takara, Kwankwaso ba zai iya zama abokin takara ba, domin dole ne kujerar mataimaki ta koma Kudu.

Kara karanta wannan

Ganduje ya aika muhimmin sako ga Kwankwaso wajen zaman makoki a Kano

Yakasai da aka fi sani da Dawisu ya ce Arewa na jin an ware ta a mulkin Tinubu, musamman wajen nade-nade da ayyukan raya kasa da aka fi karkata zuwa kudu.

A cewarsa, wannan haushi na iya sa Arewa ta hade domin kalubalantar APC, musamman idan Atiku ne ya samu tikitin hadakar adawa.

Ya kuma ce idan Jonathan ya fito takara, zai samu karbuwa sosai, domin zai yi wa’adin shekara hudu kacal, abin da zai sa Arewa ta amince da shi.

Yakasai ya ce a halin yanzu APC ba ta cika alkawurran kamfen ba, musamman a bangaren wutar lantarki da tsaro, duk da cewa ana ganin wasu ayyuka suna gudana.

Yakasai ya caccaki gwamnatin Tinubu

Mun ba ku labarin cewa tsohon hadimin Abdullahi Umar Ganduje, Salihu Tanko Yakasai, ya yi magana kan adalci da rabon dukiya a jihohi.

Tsohon 'dan takarar gwamnan ya yi zargin cewa an ware biliyoyin Naira domin ayyuka a jihar Lagos cikin shekaru na mulkin Bola Tinubu.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan zargin nuna bambanci tsakanin yankunan Najeriya wajen yin ayyuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.