Musulunci Ya Yi Rashi a Najeriya, Mataimakin Shugaban JIBWIS Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Musulunci Ya Yi Rashi a Najeriya, Mataimakin Shugaban JIBWIS Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Mataimakin shugaban kungiyar Izala na I a jihar Katsina, Alhaji Sani Abubakar Daura ya riga mu gidan gaskiya ranar Juma'a, 13 ga Fabrairun 2026
  • Shugaban Izala na jihar Katsina kuma Daraktan Da'awah na kasa, Sheikh Yakubu Musa Hassan ya tabbatar da hakan a wata sanarwa
  • Sanarwar ta bayyana cewa za a yi jana'izar marigayin yau Asabar, 14 ga watan Fabrairu, 2026 a gidansa da ke garin Daura

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Kungiyar Jama'atul Izalatil Bid'ah Wa Ikamatus Sunnah (JIBWIS) ta Jihar Katsina ta rasa daya daga cikin shugabanninta.

Kungiyar JIBWIS wacce aka fi sani da Izala ta tabbatar da rasuwar mataimakin shugaban ta na jihar Katsina I, Alhaji Sani Abubakar Daura.

Izala.
Shugaban kungiyar JIBWIS na Katsina, Sheikh Yakubu Musa Hassan da mataimakinsa, Alhaji Sani Abubakar Daura Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

Mataimakin shugaban Izala a Katsina ya rasu

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kungiyar Izala reshen Katsina ta wallafa a shafinta na Facebook a daren jiya Juma'a.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya yi karatun ta natsu, ya ja kunnen APC kan jam'iyyar ADC

Shugaban kungiyar na Jihar Katsina, kuma Daraktan Da'awah na Kasa, Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan (Sautus Sunnah) ya tabbatar da rasuwar mataimakin nasa.

Ya ce marigayin ya rasu ne a ranar Juma'a 25 ga watan Sha'abanz 1447AH, wanda ya yi daidai da 13 ga watan Fabrairun 2026.

An sa lokacin jana'iza a Daura

Sheikh Yakubu Musa ya ce:

"A madadin Kungiyar JIBWIS ta jihar Katsina, ina sanar da rasuwar Mataimakin shugaban kungiyar na jiha na I, Alh. Sani Abubakar Daura, wanda Allah SWT ya yi ma rasuwa a yau (Juma'a) 25 ga Sha'aban, 1447AH, daidai da 13 ga Fabrairu, 2026
"Za'a gabatar da jana'izar shi gobe Asabar 26 ga watan Sha'aban 1447 wanda ya yi daidai da 14 ga watan Fabrairu, 2026 a Garin Daura
"Muna rokon Allah SWT Ya jikanshi, Ya gafarta ma shi, Ya haska ka kabarin shi, ya sanya albarka a cikin zuriyarsa, Allah SWT Ya sanya Aljannar Firdausi ta zama makoma a gare shi

A karshe, Sheikh Yakubu Musa ya roki Allah da Ya ba su hakurin jure wannan Babban rashin, inda ya kara da cewa, "Allah Ya sa mu cika da Imani idan ajalin mu ya yazo.

Kara karanta wannan

Lamari ya juya: Ƴan bindiga sun yi saɗaf saɗaf sun hallaka 'DPO' bayan sace shanu

Sheikh Bala Lau ya mika sakon ta'aziyya

Shugaban Kungiyar JIBWIS na kasa, Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi, ‘yan uwa da daukacin al’ummar Musulmi bisa rasuwar Alhaji Sani Abubakar Daura.

"Marigayin kafin rasuwarsa ya shafe shekaru masu yawa yana bayar da gudumawa, hidima da jajircewa wajen tallafawa harkokin da’awa da ayyukan alheri karkashin Kungiyar JIBWIS," in ji Bala Lau.
Sheikh Bala Lau.
Shugaban kungiyar JIBWIS na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

Shugaban Izala ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kurakuransa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, sannan Ya ba iyalansa da ‘yan uwansa hakurin jure wannan babban rashi.

Sheikh Habibu Yahaya Kaura ya kwanta dama

A wani rahoton, kun ji cewa babban malamin Izala, Sheikh Habibu Yahaya Kaura, ya rasu bayan doguwar jinya da ya yi a wani asibiti a birnin tarayya Abuja.

Rasuwar Sheikh Habibu Yahaya Kaura ta janyo alhini mai yawa, musamman ganin irin gudunmawar da ya bayar tsawon shekaru wajen wa’azi da karantar da al’umma.

Manyan malaman musulunci a Najeriya sun yi alhini tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, suna mai bayyana kyawawan halayensa da irin gudummuwar da ya bayar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262