Ganduje Ya Aika Muhimmin Sako ga Kwankwaso wajen Zaman Makokin Shekarau a Kano
- Tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyarar ta’aziyya ga Malam Ibrahim Shekarau bayan rasuwar yayansa
- Ganduje ya yi magana game da Rabiu Kwankwaso da ake kiransa makiyinsa, a nan ya ce yana daukarsa a matsayin dan uwa a addini
- Ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan ayyukan ci gaba a Kano tare da masa addu’ar samun nasara da ci gaba da yi wa al’umma aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Ana ci gaba da jimami bayan rasuwar yayan tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau wanda ya rasu bayan jinya.
Tsohon shugaban APC, Dr Abdullahi Umar Ganduje na daga cikin wadanda suka samu damar kai masa ziyara domn yin ta'aziyya.

Source: Twitter
Hakan na cikin wani bidiyo da shafin Mikiya ya wallafa a Facebook a jiya Juma'a 13 ga watan Faburairun shekarar 2026 da muke ciki.
Ganduje ya yi wa Kwankwaso shagube a Kano
A cikin bidiyon, Ganduje ya tabo Rabiu Kwankwaso da ya ce yana kiransa da makiyi duba da yadda siyasa ta raba su bayan zama tare na shekaru.
Ganduje ya bayyana cewa shi ba makiyinsa ba ne, kuma yana daukarsa kamar dan uwa kamar yadda hadisi ya ce Musulmi dan uwan Musulmi ne.
Ya ce:
"Ni ma an ce da ni makiyi, ni ma sakon da zan ba Ali Baba wanda ya ce da mu makiya, ka jawo masa hadisin nan da ya ce Musulmi dan uwan Musulmi ne.
"Saboda haka ni ba makiyi na ba ne, ni dan uwana ne, kuma da ya ce an miko mani akushi, sai ka kara tambayarsa, akushin nan da ya saba ci ne aka kwace aka kawo nan, to wannan akushi, akushi ne dai na yi wa al'umma aiki."

Source: Facebook
Ganduje ya yi wa Gwamna Abba Kabir addu'a
Har ila yau, Ganduje ya yabawa Gwamna Abba Kabir kan ayyukan ci gaba da yake yi a jihar Kano domin bunkasa jihar baki daya.
Tsohon gwamnan ya yi masa addu'o'i tare da yi masa fatan alheri inda ya yi ta'aziyya ga Ibrahim Shekarau bisa rashin da aka yi masa.
"Allah ya taimaki gwamnan jihar Kano domin ya ci gaba da yi wa al'ummar jihar aiki, ka gaya wa Kwankwaso da ya ce wai ranar can, rana ce ta wadanda suka yi butulci.
"To wani aike da zan kara yi maka ka ce da shi muddin ya yi bikin ranar nan muma muna so a ranar za mu yi bikin ranar 'yancin gwamna."
Ganduje yana magana game da 23 ga Junairu da 'Yan Kwankwasiyya suka ce ita ce ranar butulci ta duniya saboda ranar Abba Kabir Yusuf ya rabu da NNPP.
Ganduje ya bude masallaci a jihar Kano
Mun ba ku labarin cewa tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da sabon masallacin da gidauniyarsa ta gina a jihar Kano.
An ce Abdullahi Ganduje ya gayyaci Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero buden masallacin da aka yi ranar Juma'a 13 ga watan Faburairun shekarar 2026.
Manyan 'yan siyasa, malamai daga ciki da wajen Kano da sun shaida bude masallacin da aka ba Sheikh Lawal Shuaibu Abubakar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

