'Yan Ta'adda Sun Kai Wasikar kai Hari Kauyuka, Mutane Sun Fara Gudu
- Kwanaki bayan kai mummunan hari a jihar Kwara, 'yan ta'adda sun rubuta wasika a wani kauye suna gargadin cewa za su kai hare-hare
- Biyo bayan lamarin, rahotanni sun bayyana cewa mutane sun fara gudu daga kauyen saboda tsoron abin da ka iya biyo bayan wasikar
- Rundunar 'yan sandan jihar da wasu jami'an tsaro sun tabbatar da samun wasikar, kuma an rahoto cewa an kara yawan sojoji a yankin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kwara - Ana fargabar hare-haren da ‘yan ta’adda ke kaiwa na iya cigaba bayan wasu mahara sun fara yaɗa wasikun gargadi zuwa ga al’ummomi da dama a Jihar Kwara.
Majiyoyi sun bayyana cewa an jefar da wata wasiƙa a yankin Ira, wani gari da ya haɗa garuruwan Inaja da Aho a karamar hukumar Oyun.

Source: Original
Jaridar Punch ta gano cewa cikin kwanaki shida da suka gabata an aika da wasiku zuwa wurare huɗu daban-daban, inda aka yi barazanar kai hari.
Mutane sun tsere bayan wasiƙar barazana
An tattaro cewa mazauna Ira, Inaja da Aho sun fara barin gidajensu sakamakon wasikun barazanar da ake zargin ‘yan ta’addan ne suka aika.
Abin da ke cikin daya daga cikin wasikun:
“Wannan saƙo daga kungiyar 'yan ta'adda ne. Takenmu: muna kashewa, muna satar mutane. Babu wani gari ko wuri da muke tsoro mu lalata…
"Muna bincike da tattara bayanai kafin mu kai hari. Mun ji labarin wannan gari Ira, ku mutane masu ƙarfi ne, kuna da manyan mutane masu ƙarfi da za su iya fuskantar ƙungiyarmu.
"Ku kasance a shirye da mu a kowane lokaci da kowace rana, ba mu damu da bokanku ko ƙarfinku ba. Mun bar Kaiama, mun koma Ira, Inaja, Aho da sauran garuruwa da ke kewaye.”
Yadda aka aika da wasikar
Wani basarake a Ira, wanda ya nemi a ɓoye sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce an jefar da wasiƙar ne a tashar babura kusa da babban masallacin garin.
“An ga wasiƙar da misalin ƙarfe 2:30 zuwa 3:00 na rana. Wasu mutane biyu a kan babur ne suka jefar da ita a wurin masu acaba a kusa da Babban Masallacin Ira.
"Da farko masu babur sun yi zaton kuskure ne, suka ajiye wa mutanen, amma bayan sun karanta sai suka garzaya da ita fadar sarki.
“Da wasiƙar ta isa hannun mai martaba, sai ya sanar da jami’an tsaro. Da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, jami’an DSS da ‘yan sanda suka ziyarci Inaja, Ira da Aho. Yanzu haka sojoji, ‘yan sanda da jami’an NSCDC na sintiri a yankin,”
- Inji shi
The Cable ta rahoto cewa basaraken ya ƙara da cewa duk da kasancewar jami’an tsaro, tsoro ya mamaye al’ummomin, lamarin da ya sa wasu mazauna suka koma wasu garuruwa na ɗan lokaci.

Source: Twitter
‘Martanin 'yan sanda da DSS
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Ejire Adetoun-Adeyemi, ta tabbatar da karɓar wasiƙar, inda ya ce suna cigaba da bincike.
Haka kuma, wani babban jami’in DSS ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa:
“Mun karɓi wasiƙar, kuma muna aiki a kai.”
A halin da ake ciki, shugaban karamar hukumar Oyun, Akanbi Olarewaju, ya kira taron gaggawa kan tsaro a sakatariyar majalisa da ke Ilemona.
An kai hari wajen biki a Kano
A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan ta'adda da ba a gano su waye ba sun kai hari wani waje da ake biki a karamar hukumar Shanono a Kano.
Wata majiya ta tabbatar da cewa maharan sun sace mata akalla 10, sun shiga daji da su a niyyar yin garkuwa da su kafin sojoji su bi su.
Bayan dakarun Najeriya sun bi sawun 'yan ta'addan, sun gwabza kazamin fada inda aka ceto wasu daga cikin matan da aka sace aka dawo da su.
Asali: Legit.ng


