Atiku Ya Lura da Kuskuren INEC, Ya Bukaci a Sauya Lokacin Zaben 2027

Atiku Ya Lura da Kuskuren INEC, Ya Bukaci a Sauya Lokacin Zaben 2027

  • Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi martani kan lokacin da hukumar INEC ta tsara don gudanar da zaben 2027
  • Atiku Abubakar ya bukaci hukumar INEC da ta gaggauta sake nazari kan lokacin da ta shirya gudanar da babban zaben shekarar badi
  • Babban jagoran hamayya a kasar ya bayyana cewa akwai bukatar yin tsari na tafiya da kowa wajen sanya lokacin gudanar da zabe

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kira da babbar murya ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Atiku ya bukaci INEC da ta hanzarta sake nazari kan ranar 20 ga Fabrairu, 2027 da ta ayyana don gudanar da zaben shugaban kasa mai zuwa, inda ya bayar da dalilin cewa ranar ta fado ne a cikin watan azumin Ramadan.

Kara karanta wannan

An gano matsalar da za a iya samu a zaben shugaban kasar 2027 saboda azumin Ramadan

Atiku ya ba hukumar INEC shawara
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan da Atiku Abubakar Hoto: @inecnigeria, @atiku
Source: Twitter

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya sanya a shafinsa na X a daren ranar Juma’a, 13 ga watan Fabrairun 2026.

Me Atiku ya gaya wa hukumar INEC?

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa ranar zaben ta fado ne a cikin lokacin azumi, wanda ake tsammanin zai fara daga 7 ga Fabrairu zuwa 8 ga Maris, 2027.

“Dole ne hukumar zabe (INEC) ta hanzarta sake duba ranar 20 ga Fabrairu, 2027 da ta sanar domin gudanar da babban zabe."
“Wannan rana ta fado ne a cikin lokacin Ramadan (7 ga Fabrairu zuwa 8 ga Maris, 2027), wani lokaci ne mai tsarki na azumi, tunani, da sadaukar da kai ga ibada ga miliyoyin Musulmin Najeriya."

- Atiku Abubakar

Atiku ya yi magana kan zabe

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya lura cewa zabubbuka suna bukatar halartar jama’a da dama da kuma jajircewa na zahiri, wanda a cewarsa, ibadar addini na iya shafa.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: INEC ta sanar da ranar zaben shugaban kasa da na gwamnoni a 2027

“Zabubbuka ba wasu abubuwa ba ne kawai na gudanarwa ba; ayyuka ne na kasa wadanda ke bukatar halartar jama'a sosai, kuzari, da kuma hada hankali wuri guda."
“Sanya irin wannan muhimmin aikin na kasa a tsakiyar lokacin gudanar da babbar ibadar addini yana nuna rashin kyakkyawan tunani da kuma rashin kula da yanayin zamantakewa da addini na kasar nan."

- Atiku Abubakar

INEC: Atiku ya nuna shakku kan hukumar zabe

Ya jaddada bukatar yin tsari na tafiya da kowa a kasa mai addinai da kabilu daban-daban kamar Najeriya.

Atiku ya ba hukumar INEC shawara kan zabe 2027
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar Hoto: Mustapha Sule Lamido
Source: Facebook
“A kasa mai mabambantan al’adu kamar Najeriya, yin tsari na tafiya da kowa ba zabi ba ne, wajibi ne."
"Abu mai sauki kamar zabar ranar da kowa zai yarda da ita bai kamata a bar shi ya sukurkuce ba. Hakan yana nuna kwarewa, hangen nesa, da kuma girmama ’yan kasa."
“Idan INEC tana fuskantar kalubale wajen daidaita abu mai sauki kamar lokaci, ’yan Najeriya suna da gaskiyar tambayar cewa: Wane tabbaci muke da shi na cewa za ta iya gudanar da zabe mai gaskiya da adalci a 2027?”

- Atiku Abubakar

Kara karanta wannan

'Abin da Tinubu zai yi kan tura sakamakon zabe kai tsaye ta yanar gizo'

APC ta sha zargi daga wajen Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi zarge-zarge kan jam'iyyar APC.

Atiku Abubakar ya yi zargin cewa jam’iyya mai mulki ta APC tana kulla shirin yin amfani da bangaren shari’a domin raunana jam’iyyar ADC.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci kusoshin jam’iyyun adawa da su kasance cikin shiri domin dakile wannan shiri.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng