Bayan EFCC, Wata Hukumar Binciken Rashawa Ta Gayyaci El Rufai, Zai Sha Tambayoyi

Bayan EFCC, Wata Hukumar Binciken Rashawa Ta Gayyaci El Rufai, Zai Sha Tambayoyi

  • Malam Nasir El-Rufai ya tabbatar da cewa zai kai kansa ofishin hukumar ICPC domin amsa gayyatar da ta yi masa
  • Lauyan El-Rufai ya bayyana cewa tsohon gwamnan zai fara kai kansa ofishin EFCC ranar Litinin kafin ya je ofishin ICPC
  • Wannan na zuwa ne 'yan awanni bayan jami'an tsaro sun yi yunkurin kama tsohon gwamnan a filin jirgin Abuja

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya tabbatar da cewa zai amsa gayyatar da hukumar ICPC ta yi masa a ranar Laraba, 18 ga Fabrairu.

Wannan na zuwa ne 'yan awanni bayan wasu jami'an tsaro sun yi yunkurin kama El-Rufai a filin jirgin sama na Abuja.

El-Rufai ya karbi takardar gayyata daga hukumar ICPC
Malam Nasir El-Rufai, da ginin ofishin hukumar ICPC da ke Abuja. Hoto: @elrufai, @icpcnigeria
Source: Twitter

Nasir El-Rufai zai mika kansa ga ICPC

El-Rufai ya bayyana cewa ya karbi takardar gayyata da ICPC ta aika masa a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Bayan sha da kyar, El Rufai ya fadi adadin jami'an tsaron da suka so cafke shi

Tsohon Ministan Abuja ya bayyana cewa zai gabatar da kansa a ofishin hukumar kamar yadda aka tsara domin amsa dukkan tambayoyin da ake masa.

Nasir El-Rufai ya ce:

"Jiya, bayan yunƙurin da aka yi na sace ni wanda ba ayi nasara ba, hukumar ICPC ta kawo mani takardar gayyatar su."

Ya ƙara da cewa:

"Lauyana ya riga ya rubuta takarda domin tabbatar da cewa zan bayyana a ofishin ICPC ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026."

El-Rufai ya ce jami'an tsaro sun matsa masa

Mai magana da yawunsa, Muyiwa Adekeye, ya yi zargin cewa jami'an sun yi ƙoƙarin kama El-Rufai ba tare da nuna takardar gayyata ta hukuma ba.

Tsohon gwamnan na Kaduna ya ce:

"Sun kwace fasfo ɗina na fita ƙasashen waje a lokacin dambarwar, wanda hakan ya sa magoya baya suka nuna fushinsu."

Haka zalika, lauyansa Ubong Akpan ya yi Allah-wadai da yunƙurin kama shi, inda ya bayyana lamarin a matsayin wani mataki da ya saɓa wa doka.

El-Rufai ya ce zai mika kansa ga ICPC awanni 48 bayan ya gana da EFCC.
Mallam Nasir El-Rufai, zaune a kan kujerar Gwamnan Kaduna a ranar 15 ga Yuni, 2019. Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Matsayar lauyoyi kan bin dokar kasa

Lauyan ya bayyana cewa wanda yake karewa a shirye yake ya ba da haɗin kai, amma dole ne a bi dukkan ƙa'idojin shari'a yadda ya kamata, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Shekaru 7 da ɗauke Dadiyata, El Rufai ya faɗi gaskiyar abin da ya sani

Akpan ya bayyana abin da ya faru a filin jirgin a matsayin keta haƙƙin ɗan adam da kuma saba wa tsarin aikin hukumomin tsaro a Najeriya.

Ya kuma bayyana cewa hukumar EFCC ta riga ta aika wa El-Rufai gayyata tun yana ƙasar waje, kuma ya amince zai kai kansa.

A halin yanzu, wasu na kusa da El-Rufai, Amadu Sule da Jimi Lawal, suna fuskantar tuhume-tuhume na zamba da halatta kuɗaɗen haram daga ICPC.

El-Rufai zai kai kansa ofishin EFCC

Tun da fari, mun rahoto cewa, Nasir El-Rufai ya ce zai kai kansa ofishin hukumar EFCC a ranar Litinin, domin amsa gayyatar da ta yi masa

EFCC ta aika da takardar gayyata zuwa gidansa a watan Disambar shekarar 2025, wanda hakan ya jawo raɗe-raɗin cewa za a iya kama shi.

Jama'a na dakon ganin yadda wannan ziyara ta El-Rufai zuwa ofishin EFCC za ta kasance a ranar Litinin mai zuwa, 16 ga Fabrairu, 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com